Sai da safenku
Mun kawo ƙarshen rahotanni kai-tsaye a wannan shafi. Sai kuma gobe da yardar Allah.
Kafin goben, ku duba ƙasa domin karanta dukkanin labaran da muka wallafa a yau Talata.
Umar Mikail ke cewa na yi nan.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye na abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya a yau Talata 27 ga watan Oktoban 2020.
Buhari Muhammad Fagge and Umar Mikail
Mun kawo ƙarshen rahotanni kai-tsaye a wannan shafi. Sai kuma gobe da yardar Allah.
Kafin goben, ku duba ƙasa domin karanta dukkanin labaran da muka wallafa a yau Talata.
Umar Mikail ke cewa na yi nan.

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Barcelona, Josep Maria Bartomeu ya sauka daga mukaminsa, bayan matsin lamba daga magoya baya kan sabani tsakaninsa da Lionel Messi.
Bartomeu, wanda ya zama shugaban Barcelona a 2014, ya ajiye aikin bayan da magoya baya ke kokarin hambarar da shi.
Shugaban ya samu sabani tsakaninsa da kyaftin din Argentina, Lionel Messi, wanda ya bukaci barin Barcelona kafin fara kakar bana.
Ya ajiye aikin ne kwana uku bayan Barcelona ta sha kashi a hannun Real Madrid da ci 3-1a Gasar La Liga karawar hamayya ta El Clasico a Camp Nou.
Cikin watan Maris ya kamata Bartomeu ya sauka daga shugabancin Barcelona bayan wa'adin zango biyu.

Asalin hoton, @shehusanusi8
Gwamnan Jihar Adamawa ya bai wa waɗanda suka sace kayayyakin abinci a jihar wa'adin awa 12 da su mayar da abin da suka sata ko kuma a rushe inda suka ɓoye su.
Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ya bayyana haka ne a yau Talata cikin wani jawabi da ya yi wa al'ummar jihar.
"Na ba da wa'adin awa 12 daga 6:00 na yamma zuwa 6:00 na safe ga 'yan dabar da su dawo da dukkanin abin da suka sata daga ma'adanin gwamnati da na mutane ga ofishin 'yan sanda mafi kusa da su," in ji gwamnan.
"Wannan wa'adin zai ƙare da 6:00 na safiyar Laraba, 28 ga Oktoba, wanda bayan haka zan bayar da umarnin shiga gida-gida domin bincike da ƙarfe 7:00 na safiyar.
"Ɗaya daga cikin umarnin shi ne ƙwace shaidar mallaka ko kuma rushe gidan da aka ɓoye kowane irin kayan da aka sata. Ya kamata 'yan ƙasa na gari su bai wa jami'an tsaro haɗin kai don ganin an tabbatar da dokar."
Haka nan Gwamna Fintiri ya ce dokar hana fita ta awa 24 da aka saka a jihar "ta zama dole ne" bayan tuntuɓar hukumomin tsaro domin "daƙile ayyukan 'yan daba".

Asalin hoton, Lamaran Azare
Kungiyar tallafa wa manoma ta Arewa maso gabashin Najeriya, NECAS, ta ce an gano aƙalla tarakatoci 48 daga cikin 110 da aka sace ranar Litinin.
An sace motocin noman ne a ma’adanar kayayyakin noma a sheikwatar ƙungiyar da ke birnin Yola na Jihar Adamawa.

Asalin hoton, Lamaran Azare
Shugaban ƙungiyar ta NECAS na ƙasa, Sadeeq Daware ya ce da ma ƙungiyar ta karɓo tarakatocin ne bashi domin taimaka wa manoma farfado da ayyukansu a yankin na arewa maso gabashin Najeriya da ya sha fama da rikicin Boko Haram.

Asalin hoton, Lamaran Azare
A farkon makonnan ne dai bidiyon yadda matasa ke tura taraktoci ɗauke da sunan kungiyar ta NECAS ya yaɗu a shafukan zumunta bayan wawason kayan abinci da na noma suka yi a rumbunan kayan abinci a jihohi da dama na Najeriya.
Gwamnatin jihar ta Adamawa ta saka dokar hana fita a Yola sakamakon ayyukan masu satar kayan abincin ta tsawon awa 24.

Asalin hoton, @MinOfInteriorNG
Gwamnatin Najeriya ta sanar da ranar Alhamis 29 ga watan Oktoba a matsayin ranar hutu ga ma'aikata domin yin bikin Maulidin Annabi Muhammadu S.A.W.
An bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai na Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida Mohammed Manga ya fitar a yau Talata.
Sanarwar ta ce Ministan Ma'aikatar, Ogbeni Rauf Aregbesola, ya taya al'ummar Musulmin Najeriya murnar zagayowar ranar na gida da kuma na ƙasashen waje.
Sannan ministan ya umarci Musulmi da "su ɗabbaƙa ɗabi'ar Annabi ta haƙuri da juriya" yayin bikin, yana mai cewa "yin hakan zai samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a ƙasa baki ɗaya".
Al'ummar Musulmi a faɗin duniya kan yi bikin tunawa da ranar haihuwar Annabi Muhammadu - amincin Allah ya tabbata a gare shi - a kowace ranar 12 ga watan uku na kowace shekarar Musulunci wato Rabi’ul Awwal.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X

Wata kotu ta yi watsi da ƙarar da aka shigar da wasu matasa 47 a gabanta bisa zargin auren jinsi.
An kama mazajen ne yayin wani samamen 'yan sanda a wani otel a Jihar Legas cikin shekarar 2018 bayan da 'yan sandan suka yi zargin cewa wani gidan cashiya ne na 'yan luwaɗi.
Sai dai waɗanda ake zargin sun ce suna halartar wani bikin ranar haihuwa ne lokacin da aka kama su.
Bayan an sha ɗage zaman ƙarar, Mai Shari'a Rilwan Aikawa na Babbar Kotun Jihar Legas ya yi watsi da ita yana mai cewa ya yi hakan ne "saboda ƙarancin nuna kulawa a shari'ar".
Ana kallon ƙarar a matsayin wani gwaji na dokar da aka kafa a 2014, wadda ta haramta auren jinsi gami da nuna wata ɗabi'ar luwaɗi ko maɗigo a bainar jama'a.
Duk wanda aka kama da laifi, zai iya fuskantar ɗaurin shekara 14 a gidan yari. An haramta luwaɗi da maɗigo a ƙasashe da dama na Afirka.

Asalin hoton, Getty Images
'Yan sanda a Najeriya sun ce sun kama mutum fiye da 800 da ake zargi da sace-sacen kayan abinci a rumbunan ajiye kayayyaki da ke jihohin ƙasar.
Aƙalla mutum 520 aka kama a Jihar Legas kaɗai.
Kamen ya biyo bayan wawaso da wasu matasa suka saka wa wuraren ajiyar kayan abinci a jihohin Kaduna da Filato da Adamawa da Oyo da Kwara da kuma Abuja.
Kazalika an wawashe gidajen wasu manyan 'yan siyasa a ƙasar jim kaɗan bayan lafawar zanga-zangar da aka shafe mako biyu ana yi ta nuna ɓacin rai kan ayyukan rundunar 'yan sandan ƙasar, wadda ta rikiɗe zuwa tashin hankali.
A yau Talata ma wasu 'yan daba sun kutsa sansanin horar da masu yi wa ƙasa hidima na NYSC da ke Abuja riƙe da wuƙaƙe, inda suka yi awon gaba da katifu da sauran kayayyaki.
'Yan sanda a Legas sun ce an kama mutanen ne da zargin laifuka daban-daban da suka haɗa da fashi da kisan kai da tayar da hankali da lalata dukiya da kuma mallakar makamai ba bisa ƙa'ida ba.
A Jihar Filato ma an kama fiye da mutum 300 bayan sun saci kayayyaki da kuma lalata gine-gine a Jos, babban birnin jihar.
"Yan sanda a Abuja sun ce sun kama mutum 51 da irin waɗannan laifuka bayan an wawashe wuraren ajiyar abinci daban-daban.
Kusan mako guda kenan matasan na fasawa tare da wawasahe rumbunan abinci a jihohi, inda suka ce an jibge kayan tallafin annobar korona da Gwamnatin Tarayya ta bai wa jihohi.

Asalin hoton, @Zazzau_Emirate
Wata babbar kotun Jihar Kaduna da ke zamanta a Zariya da ke arewacin Najeriya ta ɗage shari'ar da aka ake alubalantar nain sabon Sarkin Zazza Alhaji Ahmad Nuhu Bamalli.
Kotun ta saka ranar 2 ga watan Nuwamba don ci gaba da sauraren ƙarar da Iyan Zazzau, Alhaji Bashir Aminu ya shigar.
Kotun, wadda mai shari’a Kabir Dabo ke jagoranta, ta ɗage cigaba da shari'ar ne domin bayar da dama a miƙa takardun ƙarar ga dukkan ɓangarorin da ake ƙalubalanta a shari'ar.
Ustaz Usman Yunus babban lauyan Najeriya, shi ne ya jagoranci sauran lauyoyin mai shigar da ƙara, ya kuma yi wa manema labarai karin bayani bayan zaman kotun na yau.
Ku latsa hoton da ke ƙasa ku saurari bayanin nasa:

Asalin hoton, Getty Images
Masu amfani da kafafen sada zumunta a Tanzaniya na fama da matsalar shiga Twitter da Whatsapp, kwana daya gabanin babban zaben kasar.
Tun a safiyar yau ne masu amfani da wannan shafuka ke fama wajen sauke hoto ko kuma bidiyo, ba sa iya komi sai dai baika rubutaccen sako. shima shafin Twitter ba ya aiki sai ta hanyar amfani da manhajar VPN.
BBC ta yi kokarin jin ta bakin hukumar sadarwa ta kasar kan wannan batu amma kokarin ya ci tura.
Da yawa sun yi imanin wannan matsalar na da alaka da zaben Zanzibar.
Babbar jam'iyyar adawa a Zanzibar ta yi ikirarin cewa an kashe mutane takwas a wata tarzomar zabe da ta tashi.
'Yan sanda sun musanta wannan ikirari amma sun tabbatar da kama mutane sama da 40.
Ana ta yada hotuna da bidiyo na rikicin zaben Zanzibar a kafafen sada zumunta.
Shugaba John Magafuli na neman shugabancin kasar ne a karo na biyu. tare da babban abokin hamayyarsa Tundu Lissu.

An fara fuskantar wahalar man fetur a Abuja babban birnin Najeriya.
Layukan motoci da sauran abubuwan hawa sun cika kusan kowanne gidan sayar da mai a Abuja, babban birnin kasar.
Tun a ranar Litinin mazauna Abuja suka fara fuskantar dogayen layukan a gidajen sayar da man fetur.
Amma kamfanin mai na NNPC ya ce matsalar ba wan abin fargaba ba ne domin akwai man yana nan wadace.
Kamfanin ya fadi a Twitter cewa "NNPC yana da litar fetir sama da biliyan biyu a ajiye da za a fitar domin samun wadatuwarsa."
Wasu na ganin an fara shiga wahalar fetur din ne saboda dokar hana fita da aka kafa a wasu jihohi.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Yadda ake wahalar fetur a Abuja








Asalin hoton, AFP
An tsaurara jami'an tsaro a Bamako babban birnin kasar Mali, inda ake shari'ar wasu masu ikirarin jihadi uku da ake zargi da kitsa wani harin otal da aka kai kan 'yan kasar waje a 2015.
Biyu ne kawai da ake zargi suka gurfana gaban kotun, daya da ake kira Fawaz Ould wani dan kasar Maurtaniya wanda ake ganin babba ne daga cikin masu jihadi a Sahel, ana tuhumarsa da harbe wasu mutum shida a gidan rawa, da kuma shirin ruguza wani otel da ake kira Radisson da ke Bamako.
Akwai wani ma'aikacin jirgi dan kasar Rasha da wani dan siyasar Belgium da wasu sauran mutane na cikin wadanda ya kashe.
Ba kasafai ake gabatar da irin wadannan shari'o'i ba a yankin, saboda mafi yawan kasashen Sahel gwamnatoci ba su da cikakken iko kan kasashensu.
Tsohon kakakin sojin Uganda Shaban Bantazira ya mutu bayan ya kamu da cutar korona.
An kwantar da tsohon sojan ne a wani asibiti a ranar Lahadi bayan koken fama da ciwon kirji da hawan jinni da ciwon siga da kuma tari.
Mai magana da yawun gwamnatin kasar Ofwono Opondo ya tabbatar da cewa tsohon sojan ya kamu da cutar.
Jam’iyyar NRM mai mulki ta bayyana Mista Bantazira a matsayin mai biyayya ga gwamnati da kuma jami’iyyarsa, wanda kuma ke mata aiki har lokacin mutuwarsa.
Wani sabon rahoto da aka fitar ya nuna cewa ana samun kimanin tan 250,000 na roba da ke kwarara a tekun Bahar Rum kowace shekara – kwatankwacin sama da kwantenonin jigilar kayayyaki sama da 500 kowace rana.
Rahoton na ƙungiyar da ke kula da yanayi ya ce lamarin na faruwa ne sakamakon rashin sarrafa shara yadda ya kamata abin da ke sa robobi shiga cikin teku.
A ƙarshe kuma robobin na lalata tsarin halittu sannan kuma suna barazana ga rayuwar dabbobin ruwa idan suka haɗiye su.

Asalin hoton, AFP
Rahotanni na nuna cewa ana gwabza ƙazamin yaƙi a arewacin Syria tsakanin dakarun da ke goyon bayan gwamnati da kuma mayaƙan IS.
Ƙungiyar kare hakkin bil adama ta Syrian Observatory for Human Rights ta ce mutum 16 aka kashe a ɓangaren gwamnati yayin da mutum 13 suka mutu daga bangaren IS.
Rikicin na faruwa ne a yankin hamada inda Lardunan Hama da Aleppo da Raqqa suka haɗu.
Mayakan IS ɗin sun koma yankin ne a shekarar da ta gabata bayan da aka fatattake su daga ƙauyuka da garuruwan da suke da iko da su.

Asalin hoton, Reuters
Indiya ta samu adadi mafi ƙaranci na masu kamuwa da korona a kwana guda cikin wata uku, inda aka samu mutum 36,000 kuma 488 suka mutu.
Idan aka kwatanta da adadin da ake samu a watan Satumba da ke kai wa 90,000, wanda hakan ya kusa da na watan Agusta da ke kai wa 70,000 a kullum.
Ana ci gaba da gwajin masu korona akai-akai a ƙasar – inda ake gwada kimanin mutum miliyan daya a rana.
Duk da cewa cutar kamar ba ta yin baya, har yanzu masana na shawartar a bi lamarin cutar a hankali.
Ana tuhumar wasu ɗaliban jami'a biyu a Kenya da yin kutse cikin asusun wani banki tare da sace miliyoyin kudi, kamar yadda jaridar Daily Nation ta kasar ta ruwaito.
Daliban na jami'ar Jomo Kenyatta na karantar harkar noma da fasaha, kuma suna zaune ne a wajen birnin Nairobi, ana zarginsu da satar kuɗi kimanin miliyan 24 na kudin Kenya, kwatankwacin dala 220,000, kuma suna kokarin kara kwashe wasu kudin da suka kai miliyan 190 daga CBN.
Wannan laifin da ake tuhumarsu da shi sun aikata shi ne a watan jiya.
Sai dai Antony Mwangi Ngige mai shekara 23, da Ann Wambui Nyoike mai shekara 21, sun musanta tuhume-tuhumen da aka yi musu.
Jaridar ta wallafa wannan sako ne a shafinta na Twitter kan wadanda ake zargin.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Ma’aikatar lafiya ta Sudan ta Kudu ta sanar da bullar cutar foliyo a yankuna biyar na ƙasar.
Samun ɓullar cutar a wannan karon na da alaƙa da karancin allurar rigakafi.
A watan Yuni ne Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayyana yankin Afrika a matsayin yankin da bashi da wannan cuta.
Ma’aikatar ta ce za a riƙa bibiyar mutane da kuma ci gaba da gangamin wayar da kai gme da rigakafin cutar.
“Wannan rigakafin da za a yi a wannan karon za ta mayar da hankali ne kan yara miliyan 1.4 da za a yi a ƙasashe 45 a kuma jihohi 10.
Za a yi shi ne karo biyu na farko za a fara shi ne a makon farko na watan Nuwamba, in ji Dakta John Rumunu na ma’aikatar lafiya da ke Juba.
Mataimakin shugaban Hukumar Turai Margaritis Schinas ya kamu da cutar korona.
Cikin wani sakon Twitter, ya ce sakamakon kamuwar tasa na zuwa ne bayan gwajin da ake masa akai-akai .
Yanzu dai ya killace kansa kamar yadda ake yi.
Hakan na zuwa ne bayan tattaunawar Tarayyar Turai da Gwamnatin Burtaniya kan yarjejeniyar kasuwanci bayan ficewar Burtaniyan daga kungiyar,
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X

Masu wasoso a Najeriya sun afkawa ofishin 'yan kwana-kwana da ke yankin Kuje a Abuja babban birnin ƙasar.
Sun kuma yi yunkurin kutsawa cikin sakatariyar yankin domin kai wa ga dakunan ajiye-ajiye, sai dai jami'an tsaro sun kai daukin gaggawa yankin.

Mutanen sun yayyaga takardun da ake ajiye mayanai tare da koma wasu masu yawa.


Da yawan masu sace-sacen sun yi carko-carko a bakin ofishin duk da cewa ba su samu abin da suke nema ba.

An fasa ofishin hukumar kiyaye haɗɗura na Abuja.
A gefe daya kuma, rahotanni na cewa masu wasoson sun kutsa kai sansanin 'yan bautar kasa da ke birnin tarayyar da ke yankin Kubwa.
Sun kwashi katifu da babura da wasu sauran kayayyakin ayyukan gida da ake ajiyewa saboda masu bautar ƙasa.
Duka wannan na zuwa ne daidai lokacin da masu wasoso a jihohin ƙasar ke ci gaba da fasa rumbunan ajiyar kayan abincin gwamnatocinsu na tallafin annobar korona da ya kamata a raba.