Hatsarin mota ya kashe mutum biyar a Adamawa

Asalin hoton, Kabiru Kelly
Hukumar Kiyaye Haɗura ta Najeriya (FRSC) ta tabbatar da mutuwar mutum biyar sakamakon wani hatsarin mota da ya auku a Jilima da ke Ƙaramar Hukumar Mayo Belwa ta Jihar Adamawa.
Hatsarin na manyan tirelolin da ke dakon shanu biyu ya auku ne ranar Asabar a kan babban titin Mayo Belwa zuwa Ganye, yayin da motocin suka bar garin Ngurore zuwa cin kasuwar dabbobi a garin Ganye.
Kazalika, wasu mutum 32 sun ji munanan raunuka daga cikin 53 da lamarin ya rutsa da su, a cewar jami'in rundunar FRSC reshen Jihar Adamawa Aminu Ibrahim.
Wani da ya tsallake rijiya da baya ya alaƙanta aukuwar hatsaarin da tuƙin ganganci, inda ya ce direbobin biyu na “tsere ne domin nuna bajintarsu ta tuki”.
“Gudu da tuƙin ganganci ne suka haddasa hatsarin saboda fasinjojin motocin sun yi ta ziga direbobin tare da yi musu kirari don su yi gudu," in ji Aminu Ibrahim.
A watan Maris na shekarar 2017 ma sai da hatsarin motar shanu ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 35 a garin Ngurore na jihar Adamawa.
Asarar rayuka sakamakon hatsarin manyan motoci da ke ɗaukar shanu na aukuwa lokaci zuwa lokaci a manyan titunan Najeriya, inda sau da dama hukumomi ke alaƙanta hakan da tuƙin ganganci ko kuma lodin da ya wuce kima.
Sai dai su kuma direbobin motocin sun fi ɗaura alhakin hakan kan lalacewar hanyoyi.

