An kammala shirya ɗakin da INEC za ta sanar da sakamakon zaɓe a Ondo

Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Mustapha Musa Kaita

  1. Ba gaskiya ba ne cewa an harbe ni - Matar Gwamnan Ondo

    Betty Akeredolu

    Uwar Gidan Gwamnan Ondo Betty Akeredolu ta musanta cewa an harbe ta a filin zaɓe.

    A safiyar yau wani bidiyo ya ɓulla a shafukan sada zumunta, inda yake nuna mutane na gudu kuma ana jin ƙarar harbin bindiga. Mutane sun alaƙanta bidiyon da mai ɗakin gwamnan.

    Sai dai Betty ta musanta labarin jim kaɗan bayan ta kaɗa ƙuri'arta.

    Cikin wani bidiyo da aka wallafa a Facebook, ta ce: "Abokan hamayya ne suke yaɗa shi domin yin ƙafar ungulu game da sakamakon zaɓen."

  2. Sojojin Najeriya sun kashe 'yan fashi a Katsina

    Sojojin Najeriya sun kashe 'yan fashi da dama a garin Wagini na Jihar Katsina, a cewar hedikwatar tsaro da ke Abuja.

    Wani bidiyo da ta wallafa a shafinta na Twitter ya nuna yadda jiragen yaƙi suka kai wa sansanin 'yan fashin hari ranar Alhamis da ta gabata.

    "Jiragen yaƙi da na helikwafta sun hangi ɓarayin shanu a sansanin tare da shanun da suka sata," in ji rundunar. Nan take jiragen suka fara kai hari, inda suka tarwatsa wani ɓangare na sansanin."

    Ta ce rundunar musamman ta Operation Hadarin Daji ce ta kai harin.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  3. El-Rufai na karɓar baƙuncin Shugaba Buhari

    El-Rufai da Buhari

    Asalin hoton, @GovKaduna

    A wani labarin kuma, Gwamna Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna na karɓar baƙuncin Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.

    El-Rufai da Buhari

    Asalin hoton, @GovKaduna

    Buhari ya je Kaduna ne domin halartar bikin yaye ɗalibai a makarantar horon sojoji ta Nigerian Defence Academy.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  4. Bidiyo: Kawai sai ga ruwan sama ana tsaka da kaɗa ƙuri'a

    Bayanan bidiyo, Ruwa ya tarwatsa layin kaɗa ƙuri'a

    Me kuwa za ku yi idan ruwan sama ya tsuge ban da neman mafaka!

    Hakan ce ta faru a mazaɓar Akinremi da ke Akure babban birnin Jihar Ondo - inda ake kaɗa ƙuri'a a zaɓen gwamna yanzu haka.

  5. Ana zargin APC da sayen ƙuri'u a filin zaɓe

    Cibiyar Dimokuradiyya da Cigaba ta Yammacin Afirka mai suna Centre for Democracy and Development (CDD-West Africa) ta bankaɗo yadda wasu 'yan siyasa ke sayen ƙuri'u a zaɓen gwamnan Jihar Ondo.

    Cibiyar ta ce ana zargin wani jami'in jam'iyyar APC mai mulkin jihar da aikata hakan a cikin wani hoto da ta wallafa a shafinta na Harshen Hausa a Twitter.

    "Lamarin na faruwa ne a rumfar zaɓe mai lamba 2 a gunduma mai lamba 8 da ke Ugbo ta Ƙaramar Hukumar Ilaje," a cewar CDD.

    'Yan takara 17 ne ke fafatawa a zaɓen ciki har da gwamna mai-ci Rotimi Akeredolu na jam'iyyar APC.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  6. Labarai da dumi-dumi, Ɗan takarar ZLP ya kaɗa ƙuri'arsa

    Ondo

    Ɗan takarar jam'iyyar ZLP, Agbola Ajayi ya kaɗa ƙuri'arsa.

    Ondo

    Ya kaɗa ƙuri'ar tasa ne a mazaɓar Ikiribo.

  7. Allah ne zai ba ni nasara - Gwamna Akeredolu

    Akeredolu

    Asalin hoton, @ptcij

    Ɗan takarar jam'iyyar APC kuma gwamna mai-ci Rotimi Akeredolu ya ce "nasararsa tana hannun Allah".

    Gwamnan ya bayyana haka ne jim kaɗan bayan ya kaɗa ƙur'arsa a mazaɓar Ijebu.

    Kazalika, ya ce yana da ƙwarin gwiwar lashe zaɓen.

  8. Manyan hanyoyi sun kasance fayau a Ondo

    Ondo

    Ana ganin hanyar na ɗaya daga waɗanda suka fi saura hada-hadar ababen hawa a Najeriya amma al'umma sun ƙaurace mata a yau.

    Hakan ba ya rasa nasaba da dokar hana fita da 'yan sanda suka sanar a jiya Juma'a, wadda ta fara aiki daga 12:00 na dare.

    Ondo

    Babbar hanyar Benin-Ore-Shagamu - wadda aka sani da zirga-zirgar ababen hawa - ta kasance fayau a yau Asabar.

    Ana ganin hanyar na ɗaya daga waɗanda suka fi saura hada-hadar ababen hawa a Najeriya amma al'umma sun ƙaurace mata a yau.

    Hakan ba ya rasa nasaba da dokar hana fita da 'yan sanda suka sanar a jiya Juma'a, wadda ta fara aiki daga 12:00 na dare.

    Ondo
  9. Kwale-kwale ya kife da ma'aikatan INEC a Ondo

    INEC ya tabbatar da cewa wani kwale-kwale mai ɗauke da jami’anta da kayan aikinsu ya kife a jiya Juma'a da yamma a wani kogi.

    Babu wanda ya mutu a hatsarin.

    wani bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumunta ya nuna yadda lamarin ya kasance.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  10. Bidiyo: Yadda aka fara jefa ƙuri'a

    Bayanan bidiyo, Yadda aka fara kaɗa ƙuri'a

    Tun misalin ƙarfe 8:50 aka fara kaɗa ƙuri'a a wasu mazaɓu.

    Tuni 'yan takarar APC (Gwamna Rotimi Akeredolu) da na PDP (Eyitayo Jegede) suka kaɗa ƙuri'unsu.

  11. Labarai da dumi-dumi, Gwamna Akeredolu ya kaɗa ƙuri'arsa

    Gwamnan Jihar Ondo kuma ɗan takarar jam'iyyar APC, Rotimi Akeredolu ya kaɗa tasa ƙuri'ar.

    Ɗan takarar APC ɗin da matarsa sun kaɗa ƙuri'ar ne da misalin ƙarfe 9:40.

  12. Bidiyo: 'Ku bi doka, ku zama masu tsari'

    Bayanan bidiyo, Zaɓen gwamnan Ondo

    Wani ɗan sanda kenan yake roƙon masu kaɗa ƙuri'a da su zama "masu bin doka da tsari" yayin jefa ƙuri'un nasu a zaɓen gwamnan Jihar Ondo.

  13. Labarai da dumi-dumi, Ɗan takarar PDP da matarsa sun jefa ƙuri'a

    Ondo

    Ɗan takarar jam'iyyar PDP mai adawa Eyitayo Jegede ya jefa ƙuri'arsa a zaɓen gwamnan Jihar Ondo.

    Ya jefa ƙuri'ar ne tare da matarsa bayan sun bi layi, kamar yadda aka tsara.

  14. Lokacin janyewa daga takara a zaɓen Ondo ya wuce

    Agboola Ajay

    Asalin hoton, Agboola Ajay

    Kakakin hukumar zaɓe ta INEC, Festus Okoye, ya shaida wa BBC cewa lokaci ya ƙure ga duk wani ɗan takara da yake son janyewa daga zaɓen gwamnan Ondo.

    Wannan na zuwa ne yayin da ake raɗe-raɗin cewa mataimakin gwamna kuma ɗan takarar jam'iyyar ZLP, Agboola Ajayi ya fice daga takarar.

    "Ya zuwa yanzu da muke magana da ku, sunan ɗan takarar na jikin takardar sunayen 'yan takara kuma duk adadin ƙuri'ar da ya samu za a ƙirga masa ita. Lokacin da ya kamata a janye daga takara ya wuce," in ji Festus Okoye.

    A gefe guda kuma, mai magana da yawun ɗan takarar ya musanta cewa mai gidan nasa ya janye daga takarar.

    Tuni aka fara kaɗa ƙuri'a a wasu mazaɓu a zaɓen gwamnan na Jihar Ondo.

  15. An fara kaɗa ƙuri'a

    Ondo

    Masu zaɓe sun fara kaɗa ƙuri'a a mazaɓar Gbogi/isikan 1 unit 9 ward 2.

    Ondo
  16. An fara tantance masu kaɗa ƙuri'a

    Ondo
    Bayanan hoto, Tuni aka fara tantance masu kaɗa ƙuri'a domin tabbatar da cewa sun cancanci yin zaɓen.
    Ondo
    Bayanan hoto, Masu zaɓe za su darje tsakanin 'yan takara 17 ne da ke fafatawa a zaɓen na yau.
  17. Manyan 'yan takara a zaɓen gwamnan Ondo

    Ondo

    Asalin hoton, Facebook

    A yau Asabar masu katin kaɗa ƙuri'a ke zaɓar gwamna a Jihar Ondo da ke Kudu Maso Yammacin Najeriya domin zaɓar gwamnan jiharsu.

    Al'ummar Ondo ba su yi zaɓen gwamna ba lokacin da sauran jihohi suka kaɗa ƙuri'u a 2019 sakamakon wani hukuncin kotu a 2017.

    A cewar hukumar zaɓe ta INEC, mutum 1,822,346 ne suka yi rijistar kaɗa ƙuri'a a zaɓen na ranar 10 ga watan Oktoba.

    Jam'iyyu 17 ne za su fafata ciki har da APC da PDP, jam'iyyu mafi girma a Najeriya.

    Sai dai babu mace ko ɗaya a cikin 'yan takarar.

    Gwamna mai-ci Arakurin Oluwarotimi Akeredolu wanda na jam'iyyar APC mai mulki, da Eyitayo Jegede na jam'iyyar PDP, da kuma Agboola Ajayi na jam'iyyar ZLP wanda tsohon kwamishinan shari'a ne, su ne suka fi shahara.

    Waɗannan 'yan takarar uku ne mafiya shahara ganin yadda jam'iyyunsu ke da ƙarfi a ƙananan hukumomi 18 na jihar.

    Jegede na ZLP na yin takarar ne a karo na biyu bayan ya nema a 2016.

    Dukkanin 'yan takarar uku lauyoyi ne kuma sun fito daga mazaɓun sanata uku daban-daban - Akeredolu daga Ondo ta Arewa; Jegede daga Ondo ta Tsakiya da kuma Ajayi daga Ondo ta Kudu.

  18. Maraba

    Assalamu Alikum Barkanku da safiyar ranar zaɓen gwamna a Jihar Ondo da ke Kudu maso Gabashin Najeriya.

    Za mu kawo muku yadda al’ummar jihar ke kaɗa ƙuri’unsu kai-taye a zaɓen da sauran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Umar Mikail ke muku maraba.