Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya Atiku Abubakar ya bi sahun wadanda suke kira ga gwamnati ta dauki matakin da ya dace kan wannan runduna, "inda ya ce an kafa ta ne domin yaƙi da manyan laifuka irinsu fashi da makami da satar mutane.
Amma a yanzu sun koma farwa mutane masu neman na kansu."
Wannan ya biyo bayan rahotannin da wasu daga cikin jaridun kasar suka wallafa, da kuma wani hoton bidiyo da ya nuna wasu da ake zargin jami'an rundunar SARS ne sun kashe wani mutum tare da guduwa da motarsa.
Lamarin ya faru ne a ranar Asabar 3 ga watan Oktoba a kofar wani Otel da ke kira Wetland, a garin Ughelli da ke Jihar Delta.
Cikin bidiyon an nuna jami'an da ake zargi sun dauki motar mutumin da suka kashe kirar Lexus SUV.
Ba wannan ne karo na farko da ake samun takun saƙa tsakanin ƴan Najeriya da rundunar SARS kan irin ayyukan da rundunar ke yi, waɗanda mutane ke zargin cewa zalunci ne zalla.
A shekarar 2017 an yi ta kiraye-kirayen a soke rundunar inda har aka yi ta zanga-zangar a wasu biranen kasar, bayan gangamin da aka rika yi a shafukan zumunta na neman a rushe ta bisa zargin taka hakkin bil'adama.
Ammam a martanin da ta mayara a watan Disamban 2017 rundunar 'yansandan Najeriya ta ce babu wani abu da zai sa ta rusa rundunar nan ta musamman mai yaki da fashi da makami da ake kira SARS duk da kiraye-kirayen da wasu a kasar ke yi na soke ta.