'Duk ɗalibin sakandare a Jihar Zamfara sai ya yi noma a aikace'
Gwamnatin Jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya ta umarci dukkanin makarantun sakandare a jihar da su saka maudu'in kimiyyar noma wato Agricultural Science a cikin manhajarsu.
Kwamishinan Ilimi na Jihar Dr Ibrahim Abdullahi ne ya bayyana hakan a Gusau, babban birnin jihar, ranar Juma'a yayin da yake ƙaddamar da wani shirin horon aikin gona ga malamai mai laƙabin School Farm Programme and E-Quality Assurance Training.
Za a gudanar da shirin ne a ƙarƙashin jagorancin hukumar ilimin bai-ɗaya ta jihar mai suna State Universal Basic Education Board (ZSUBEB).
"Gwamna Matawalle ya umarce ni da na tabbatar cewa kowacce makaranta ta saka ilimin aikin gona a manhajarta," in ji Ibrahim Abdullahi a cikin rahoton kamfanin dillancin labarai na NAN.
Ya ci gaba da cewa: "Mun ɗauki wannan mataki ne domin bai wa ɗalibai horo kan harkokin noma domin su samu damar zama ƙwararru kan noman a nan gaba.
"Za mu tabbatar da cewa an bi umarnin gwamna, za mu tabbatar cewa kowacce makaranta na aiwatar nazarin noma a aikace. Wajibi ne a bai wa kowanne ɗalibi iri ya shuka na aƙalla mita biyu."