Wannan shafi na kawo muku bayanai kai-tsaye dangane da irin wainar da ake toyawa a fadin duniya musamman batutuwan da suka shafi Najeriya da makwabtanta.
Rahoto kai-tsaye
Umar Mikail
Rufewa
Nan ne zamu dakata da kawo muku labarai da rahotanni wanda muka shafe yinin yau na ranar Asabar muna kawo muku.
Ku kasance da mu domin kawo muku wasu sabbin labarai da rahotanni da suka shafi Najeriya da sauran kasashen Afrika harma da sauran nahiyoyin duniya.
Buhari Muhammad Fagge ke muku fatan mu kwana lafiya.
Da bukatar fahimtar juna tsakanin Burtaniya da EU
Asalin hoton, Getty Images
Firaministan Biritaniya Boris Johnson da Shugabar Hukumar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen sun amince da cewa dole ne sai an fahimci juna kafin su amince da yarjejeniyar cinikayya bayan ficewar Birtaniya.
Shugabannin biyu sun amince kan muhimmancin kulla yarjejeniyar, kuma sun umarci masu jagorantar tattaunawar su yi kokari cike gibin da aka samu.
MIsta Johnson da von der Leyen sun amince su ci gaba da ayyukansu cikin makonni masu zuwa.
Rahotanni na karo da juna game da rashin lafiyar Trump
Asalin hoton, Getty Images
Ana samun rahotanni masu karo da juna game da rashin lafiyar shugaba Trump bayan ya yi kwana ɗaya a asibiti inda yake jinyar cutar korona da ya kamu da ita.
Likitoci a asibitin Walter Reed da aka kwantar da Trump sun fada manema labarai cewa shugaban yana samun sauki kuma yana numfashi ba tare da wata matsala ba.
Haka kuma ba dadewa ba Trump ya rubuta sako a shafinsa na Twitter yana cewa yana samun sauki.
Sai dai kuma wani bayanin da aka aikawa maso aiko da rahotanni a fadar White House da aka ɓoye sunan wanda aiko da sakon ya bayar da wani rahoto na daban.
Inda sakon ya ce halin da Trump yake ciki abin damuwa ne, kuma nan da sa’o’i 48 abin zai iya tsananta.
Wani rahoton kamfanin dillacin labaru na AP da ba a tabbatar ba ya ce shugaban sai da ya bukaci iskar oxygen a fadar White House a ranar juma’a kafin tafiya asibiti.
Atiku ya buƙaci a dauki mataki kan rundunar SARS
Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya Atiku Abubakar ya bi sahun wadanda suke kira ga gwamnati ta dauki matakin da ya dace kan wannan runduna, "inda ya ce an kafa ta ne domin yaƙi da manyan laifuka irinsu fashi da makami da satar mutane.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Amma a yanzu sun koma farwa mutane masu neman na kansu."
Wannan ya biyo bayan rahotannin da wasu daga cikin jaridun kasar suka wallafa, da kuma wani hoton bidiyo da ya nuna wasu da ake zargin jami'an rundunar SARS ne sun kashe wani mutum tare da guduwa da motarsa.
Lamarin ya faru ne a ranar Asabar 3 ga watan Oktoba a kofar wani Otel da ke kira Wetland, a garin Ughelli da ke Jihar Delta.
Cikin bidiyon an nuna jami'an da ake zargi sun dauki motar mutumin da suka kashe kirar Lexus SUV.
Ba wannan ne karo na farko da ake samun takun saƙa tsakanin ƴan Najeriya da rundunar SARS kan irin ayyukan da rundunar ke yi, waɗanda mutane ke zargin cewa zalunci ne zalla.
A shekarar 2017 an yi ta kiraye-kirayen a soke rundunar inda har aka yi ta zanga-zangar a wasu biranen kasar, bayan gangamin da aka rika yi a shafukan zumunta na neman a rushe ta bisa zargin taka hakkin bil'adama.
Ammam a martanin da ta mayara a watan Disamban 2017 rundunar 'yansandan Najeriya ta ce babu wani abu da zai sa ta rusa rundunar nan ta musamman mai yaki da fashi da makami da ake kira SARS duk da kiraye-kirayen da wasu a kasar ke yi na soke ta.
Sudan ta ƙulla yarjejeniyar zaman lafiya da 'yan tawayen Darfur
Asalin hoton, Reuters
Bayan kwashe watanni ana tattaunawa, a
karshe dai an sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin gwamnatin
Sudan da gamayyar ‘yan tawaye, wadda ake fatan ta kawo karshen rikicin da aka
kwashe shekaru ana yi.
Shugabannin kasar da dama ne suka halarci
wannan biki da ya gudana a Juba – babban birnin kasar Sudan ta Kudu mai
makwabtaka.
Cikin kungiyoyin ‘yan tawayen da suka sanya
hannu a yarjejeniyar har da wadanda suka fito daga yankin Darfur inda aka kashe
dubban mutane a 2003.
Ana kallon wannan yarjejeniya a matsayin wani gagarumin ci gaba, sai dai kuma ana nuna damuwa kan wasu kungiyoyi biyu da ba su shiga yarjejeniyar ba.
Cikin yarjejeniyar za a mayar da wasu ‘yan tawayen sojojin kasar.
Za kuma ta kawo karshen yakin kogin Nilu da na kudancin Kordofa.
Wata tsawa ta tarwatsa birane a Turai
Asalin hoton, AFP
Kimanin mutum 24 ne
suka ɓata bayan wata mummunar tsawa da aka yi a Faransa da Italiya.
Wani mai aikin
kwana-kwana ya mutu bayan wata bishiya ta fado masa a arewacin Italiya.
Asalin hoton, AFP
Ana neman wasu mutum 16 a yankin Piedmont, gwamnan yakin Alberto Cirio ya ce wannan ce mummunar tsawar da ta haifar da barna mafi muni tun 1994, lokacin da mutum 70 suka mutu.
A kudancin Faransa mutum takwas ne suka ɓata, ciki har da ‘yan kwana-kwana biyu da tsawar ta yi gaba da abin hawansu.
Asalin hoton, AFP
Masar ta gano akwatinan gawa da aka binne shekara 2,500
Asalin hoton, AFP
Masana tarihi a Masar sun ce sun gano akwatunan gawa 59 da aka
binne cikin yanayi mai kyau, a makonnin baya-bayan nan.
Kamfanin dillacin labarai na AFPya ruwaito cewa daya daga
cikin akwatunan da aka bude wanda ya kwashen sama da shekara 2,500 a kasa,
masana tarihin sun ce an naɗe wanda ke ciki ne da farin tufafi.
Tun bayan gano wasu
akwatina 13 da aka yi sati uku baya, ake ci gaba da gano wasu masu yawa a haƙar da ake yi wadda ba ta wuce mita 12 be, kwatankwacin taku 40.
Asalin hoton, AFP
Za a iya gano wasu akwatunan a binne a ƙasa, in ji
ministan kula da harkokin yawon buɗe ido Khaled al-Anani, wanda ya bayyana
hakan a kusa da pyramid of Djoser da ya kusa shekara 4,700.
Haƙar da ake yi a Saqqara a yan
shekarun nan, takai ga samo wasu abubuwa da mutanen baya suka kera da kuma
gawawwakin dabbobi irin su maciji tsintsaye da kwari da dai wasu sauran
dabbobi.
Asalin hoton, AFP
Wani harin bam ya kashe mutum sama da 10 a Afghanistan
A kalla mutum 15 ne suka mutu sama da 30 suka jikkata a wani harin bam din mota da aka kai a lardin Nangarhar in ji jami'an kasar.
Mai magana da yawun gwamnan yankin ya ce bam din ya fashe ne a daidai kofar shiga shalikwatar yankin, kuma masu dauke da makamai sun yi ta kokarin kutsa kai cikin ginin bayan tashin bam din.
Har yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin.
Amma kungiyoyin Taliban da IS suna yawan kai hare-hare yankin gabashin Afghanistan.
Tashin haknali na ƙara ƙamari a Afghanistan duk da tattaunawar zaman lafiya tsakanin gwamnatin kasar da kungiyar taliban da ake yi a Doha babban birnin Qatar.
Arsene Wenger na fatan komawa Arsenal
Asalin hoton, Getty Images
Tsohon kocin Arsenal Arsene Wenger ya ce a shirye yake ya koma kulob ɗin 'wata rana' bayan ɗauke ƙafarsa tun da ya bar Emirates shekara biyu da suka gabata.
Wenger mai shekara 70, ya ajiye aikinsa a Mayun 2018 bayan taimaka wa Gunners lashe kofin Premier uku da kofin FA bakwai a shekara 22 da ya shafe a ƙungiyar.
An sha gayyatarsa amma ya ce ya fi kyau ya ɗauke ƙafarsa gaba ɗaya daga kulob ɗin bayan ya tafi.
Bayan Shugaban Amurka Donald Trump da matarsa sun kamu da cutar korona, dandalin Twitter ya gargaɗi masu amfani da shi cewa duk wanda ya yi wa shugaban fatan mutuwa za a goge saƙon nasa.
Kamfanin ya ce yin hakan ya saɓa wa ƙa'idojinsa na ɗabi'un cin zarafi amma ya ce hakan ba ya nufin za a dakatar da mutum daga amfani da dandalin.
Wasu daga cikin masu amfani da dandalin sun zargi Twitter da ƙin ɗaukar mataki a kan irin wannan ɗabi'a da ta faru da su a baya.
Wannan cewa ta ke: "Wani ya taɓa faɗa mani cewa za a yi mani ƙanshin mutuwa amma da na kawo muku ƙara, Twitter ya ce hakan bai saɓa ƙa'ida ba."
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Malaman makaranta za su kai gwamnatin Jihar Abia kotu
Asalin hoton, @Abiastategov
Wasu malaman makaranta 5,664 da gwamnatin Jihar Abia ta sallama daga aiki sun yi barazanar gurfanar da ita gaban kotu idan ba a dawo da su bakin aiki ba.
A ranar Laraba lauyoyin malaman suka rubuta wa hukumar ilimin sakandare ta jihar wasiƙa suna bayyana aniyarsu ta shigar da ƙara idan ba a dawo da malaman aikin ba tare da biyan haƙƙoƙinsu.
Lauyoyin nasu suka ce ba a taɓa biyan su albashi ba tun bayan ɗaukarsu aiki a 2019 tare da rarraba musu wuraren aiki.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito lauyoyin na cewa "an sanar da korar tasu ne ta kafar yaɗa labarai kawai wadda kuma ta saɓa wa Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999.
Sojojin Najeriya sun tarwatsa sansanin Boko Haram
Rundunar musamman ta Operation Lafiya Dole ta sake yin nasarar lalata sansanin 'yan Boko Haram tare da kashe mayaƙan ƙungiyar da dama a Maima ta Jihar Borno.
Hedikwatar tsaro ta sojojin Najeriya da ke Abuja ce ta bayyana hakan cikin wata sanarwa a yau Asabar.
Wani bidiyo da ta wallafa a shafinta na Twitter ya nuna yadda ta kai hare-hare ta sama kan sansanin. Sai dai ba ta bayyana yawan waɗanda suka rasa rayukansu ba.
Kazalika ba ta bayyana ko an samu asarar rai ko rauni ba daga ɓangaren dakarunta.
A jiya Juma'a, mai magana da yawun rundunar Manjo Janar John Enenche ya ce sun kashe 'yan ta'adda 869 tare da ceto mutum 321 da aka yi garkuwa da su cikin wata uku da suka wuce.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Duba da shekaru da nauyinsa, korona na barazana ga rayuwar Trump
Asalin hoton, Getty Images
Donald Trump na fuskantar haɗurra daban-daban da suka haɗa da
nauyi da shekarunsa - waɗanda ka iya ta'azzara jinyar cutar korona da yake yi
yanzu haka.
Shekarun haihuwarsa 74 sannan yana da girman jiki fiye da 30 a
ma'aunin Body Mass Index (BMI).
Ya zuwa yanzu Trump na fuskantar ƙananan alamun cutar ne, yayin
da ake kula da shi da ƙwayoyin da ke rage raɗaɗin cutar a jikin ɗan Adam.
Sai dai yawan shekaru babbar barazana ce da ka iya
ta'azzara cutar har a je asibiti, a wasu lokutan ma har da mutuwa.
"Sai dai mafi yawan waɗanda ke kamuwa da cutar na warkewa," in ji Dr Bharat Pankhania na Jami'ar Exeter a hirarsa da BBC.
Wasu bincike da aka yi fiye da 100 a faɗin duniya sun nuna cewa haɗarin da ke kan matasa da ƙananan yara na cutar ba shi da yawa.
Sai dai daga cikin 'yan shekara 75, duk mutum ɗaya cikin 25 na waɗanda suka kamu da cutar na mutuwa.
Cutar korona ta kashe mutum fiye da 100,000 a Indiya
Asalin hoton, Getty Images
Indiya ta tabbatar da mutuwar mutum fiye da 100,000 sakamakon annonbar korona - abin da ya sa ta zama ƙasa ta uku a duniya bayan Amurka da Brazil.
Watan Satumba ne mafi muni ga ƙasar a tarihi: aƙalla mutum 1,100 ne ke mutuwa kullum saboda korona.
Wasu jihohin na bayar da rahoton adadin da ya fi na saura wasu. Hakan ya sa masana ke cewa har yanzu annobar na ci gaba da ratsa sassan ƙasar.
Jihar Maharashtra wadda ke ɗaya daga ciki mafiya arziki da yawan al'umma, ita ce kan gaba a yawan masu cutar da mutum miliyan 1.3 sannan fiye da 36,000 suka mutu.
Gane Mani Hanya: Asalin Hausawan birnin Benin na Edo
Shirin Gane Mani Hanya na wannan makon ya tattauna da Sarkin Hausawan birnin Benin na Jihar Edo da ke Kudu Maso Kudancin Najeriya, Alhaji Adamu Isa.
Sarki ya yi magana kan batutuwa da dama ciki har da yadda Hausawa suka samu kansu a Benin da kuma yadda alaƙarsu take da 'yan asalin yankin.
Bayanan sautiLatsa hoton sama domin sauraron shirin
Zaɓen Ondo: Manyan jami'an 'yan sanda 14 ne za su kula da tsaro
Asalin hoton, Nigerian Police
Babban Sufeton 'Yan Sandan Najeriya Mohammed Adamu ya aika manyan jami'an rundunar guda 14 zuwa Jihar Ondo domin tabbatar da tsaro yayin zaɓen gwamna.
Daga cikin waɗanda aka tura, DIG Adeleye Olusola Oyabade zai jagoranci aikin kula da harkar tsaro, yayin da AIG Karma Hosea Hassan zai taimaka masa.
Kazalika, mataimaka kwamishinan 'yan sanda guda 11 na cikin waɗanda aka aika domin gudanar da ayyukan tsaron.
Hukumar zaɓe ta INEC za ta gudanar da zaɓen gwamna a Jihar ta Ondo da ke Kudu Maso Yammacin Najeriya ranar 10 ga watan Oktoba.
Wata sanarwa da Kakakin 'Yansan Najeriya Frank Mba ya aike wa manema labarai ta bayyana cewa Mohammed Adamu ya buƙaci mazauna jihar su haɗa kai da jami'an tsaro domin kaɗa ƙuri'a cikin kwanciyar hankali.
Sarki Salman da ɗansa na yi wa Trump addu'ar samun sauƙi
Asalin hoton, Getty Images
Sarki Salman na Saudiyya da kuma Yarima Mai Jiran Gado Muhammad Bin Salman sun miƙa saƙon addu'ar samun sauƙi ga Shugaban Amurka Donald Trump bayan shi da matarsa sun kamu da cutar korona.
Kamfanin dillancin labaran Saudiyya SPA ya ruwaito shugabannin biyu na yin addu'ar nemamn afuwa ga Trump.
Cikin saƙonsa, Sarki Salman ya ce: "Na samu labarin cewa shugaban da matarsa sun kamu da cutar korona. Ina yi muku fatan samun sauƙi cikin gaggawa da cikakkiyar lafiya da jin daɗi."
Shi ma Yarima Muhammad ya bayyana kyakkyawan fatansa ga shugaban na Amurka.
Donald Trump ya bayyana ranar Juma'a cewa shi da matarsa Melania sun kamu da cutar cikin wani saƙon Twitter.
Sannan ya ce za su killace kansu, amma an garzaya da shi asibiti tare da ba shi wani magani da ake yin gwajinsa na yaƙi da cutar bayan ya fara nuna alamu.
Shari'ar Cin Hanci: Ban san inda Abdulrasheed Maina yake ba – Ali Ndume
Asalin hoton, Nigerian Senate
Sanata Ali Ndume wanda ya karɓi belin Abdulrasheed Maina, tsohon shugaban kwamiitin fansho na Pension Reform Task Team, ya faɗa wa kotu a Abuja cewa bai san inda wanda ya karɓa belin yake ba.
Ndume ya bayyana hakan ranar Juma'a a gaban Babbar Kotun Tarayya yayin da yake amsa tambayar kotun game da rashin bayyanar Abdulrasheed Maina a gabanta karo na uku a jere cikin mako ɗaya.
Hukumar EFCC na tuhumar Maina da laifuka 12 da suka shafi almundahanar kuɗi kusan naira biliyan biyu.
Alƙalin kotun Mai Shari'a Okon Abang ya umarci Maina ya gabatar da sanata mai-ci a matsayin wanda zai tsaya masa don karɓar belinsa.
Sanata Ali Ndume mai wakiltar Mazaɓar Kudancin Borno - inda Abdulrasheed Maina ya fito - ya amince ya zama wakilin Maina.
Sau biyu alƙalin yana sassauta sharuɗan belin, inda ya rage kuɗin daga naira biliyan ɗaya zuwa miliyan 500 da kuma sanata ɗaya maimakon biyu, bayan Maina ya yi ta miƙa buƙatar neman hakan.
Mai Shari'a Abang ya ɗage zaman sauraron ƙarar zuwa 5 ga watan Oktoba tare da umartar a zo masa da wanda ake ƙara a ranar.
An bayar da belin Maina a ranar 28 ga watan Yuli bayan ya shafe watanni a Gidan Yarin Kuje da ke Abuja.
Trump ya taɓa cewa ba ya tsoron kamuwa da korona
Asalin hoton, EPA
Kafar talabijin ta CNN ta yaɗa wani sautin hirar da ɗan jarida Bob Woodward ya yi da Donald Trump a watan Afrilu, inda shugaban ya bayyana cewa ba ya tsoron kamuwa da cutar korona.
Duk da cewa Trump ya yarda cewa cutar annoba ce "da ka iya kashe mutum", an sha ganinsa yana yawo ba tare da takunkumi ba tare da karya dokar nesa-nesa da juna.
"Akwai yiwuwar ka kamu da ita fa," Woodward ya tambaye shi yayin tattaunawar. "Yadda kake yawo a bainar jama'a kana cakuɗuwa da su, ba ka wata fargaba?"
"A'a, ba na fargaba. Ban san me ya sa ba. Ba fargaba," a cewar Trump.
"Me ya sa," Woodward ya sake tambaya.
"Ban san me ya sa ba. Kawai dai ni ba na wata fargaba."
A ranar Alhamis Shugaban na Amurka ya sanar da cewa shi da matarsa Melania sun killace kansu cikin daren Laraba sakamakon kamuwa da cutar ta korona.
Kamfanin man fetur na Chevron zai kori ma'aikata a Najeriya
Asalin hoton, NNPC
Kamfanin haƙar man fetur na Chevron Nigeria Limited (CNL) ya sanar cewa zai rage ma'aikatansa a Najeriya da kashi 25 cikin 100.
Sai dai ƙungiyar ma'aikatan man fetur ta ƙasa Petroleum and Natural Gas Senior Staff Association of Nigeria (PENGASSAN) ta nuna matuƙar takaicinta kan matakin.
Rahotanni sun ambato ƙungiyar ta PENGASSAN na zanga-zanga ranar Juma'a a Legas domin yin Allah-wadai da korar ma'aikata 600.
Shugaban kamfanin kuma mai kula da hulɗa da jama'a, Esimaje Brikinn, ya faɗa ranar Juma'a cikin wata sanarwa cewa za su rage ma'aikatan ne "domin daidaita kamfanin da gudanar da sahihin aiki tare da gogayya da sauran kamfanoni".
Ya ce: "CNL da sauran abokan hulɗarsa na duba yawan ma'aikatansa sakamakon sauyawar yanayin kasuwanci, yayin da yake ci gaba da ƙoƙarin kyautata harkoki da kuma rage kashe kuɗin gudanarwa.
"Saboda haka, kamfanin zai yi kwaskwarima ga ma'aikatansa tare da bunƙasa gudanar da ayyuka a dukkanin matakai."