Saudiyya ta gano wata maɓuyar ƴan ta’adda

Wannan shafi na kawo muku bayanai kai-tsaye dangane da irin wainar da ake toyawa a fadin duniya musamman batutuwan da suka shafi Najeriya da makwabtanta.

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba and Awwal Ahmad Janyau

  1. Mu muka kai wa tawagar gwamna Zulum hari – IS

    Zulum

    Asalin hoton, Getty Images

    Wasu da ake zargi masu iƙirarin jihadi ne sun sake kai wa tawagar gwamnan Borno Babagana Zulum hari dai-dai lokacin da suke komawa Maiduguri, babban birnin jihar.

    Gwamnan ya tsira da ga hari na ranar Lahadi sannan ba a samu asarar rai ba.

    Babu tabbaci kan ko gwamnan yana cikin tawagar.

    Harin dai ya faru ne kusan sa'a 48 bayan da masu ta da ƙayar bayan suka afkawa tawagar gwamnan a yankin Baga inda kimanin mutum 30 suka mutu a harin - har da sojoji da ƴan sanda.

    Ƙungiyar IS ta ɗauki alhakin kai harin.

    Gwamna Zulum ya kai ziyara yankin Baga a ƙoƙarin da ake na maido da dubban mutanen da rikicin Boko Haram ya ɗaiɗaita matsugunansu.

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari dai cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan kafafen yaɗa labarai, Malam Garba Shehu ya fitar ya yi Allah wadai da harin da aka kai kan tawagar gwamnan.

    Ya bayyana harin a matsayin maƙarƙashiya ga shirin da ake yi na ganin mutanen da rikici ya ɗaiɗaita sun koma gidajensu.

  2. Za a gudanar da taron G20 ta intanet saboda korona

    G20

    Asalin hoton, EPA

    Saudiyya ta ce za a gudanar da taron ƙungiyar ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziki G20 cikin watan Nuwamba ta intanet saboda annobar cutar korona.

    Saudiyya ce ƙasar da take shugabantar ƙungiyar ta G20.

    Hakan na nufin ba za a gudanar da taron yadda aka saba ba inda shugabannin ƙasashe ke taruwa a birnin Riyadh domin gudanar da taron da Saudiyyan ke fata zai bunƙasa martabarta.

    Martabar ta Saudiyya a ƴan shekarun nan na fuskantar matsaloli na cin zarafin bil adama da kuma kisan ɗan jaridar nan Jamal Khashoggi.

  3. Najeriya na fargabar makomarta kan yaki da cutar AIDS

    Gwamnatin Nijeriya ta ce tana daukar matakai don cike gibin da za a iya samu idan masu ba da gudummawa a shirin yaki da cuta mai karya garkuwar jiki na kasar suka janye nan da 'yan shekaru.

    Babban daraktan hukumar yaki da cuta mai karya garkuwar jiki a Nijeriya, Dr. Gambo Aliyu ya ce matakan sun hadar da tsame dillalai daga harkar sayen magungunan da ake bai wa masu cutar.

    Ya ce Nijeriya na fatan kara yawan masu cuta mai karya garkuwar jiki da take samarwa magunguna da mutum dubu 50 duk shekara.

    Ga abin da ya shaida a hirar da BBC ta yi da shi.

    Bayanan sautiHirar Mukhtar Bawa da Dr. Gambo Aliyu
  4. Barka da Safiya

    Masu bibiyarmu a wannan shafin barkanmu da wannan safiya ta Litinin kuma kamar kullum a yau ma za mu ci gaba da kawo muku bayanai da rahotanni kai tsaye a wannan shafin.

    Za ku iya ziyartar shafinmu na Facebook ko Twitter ko Instagram domin bayyana ra'ayoyinku ko kuma tafka muhawara dangane da labaran da muke wallafawa.