Saudiyya ta gano wata maɓuyar ƴan ta’adda

Wannan shafi na kawo muku bayanai kai-tsaye dangane da irin wainar da ake toyawa a fadin duniya musamman batutuwan da suka shafi Najeriya da makwabtanta.

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba and Awwal Ahmad Janyau

  1. Rufewa

    Nan za mu rufe wannan shafin da muka shafe yinin Litinin muna kawo labarai da rahotanni kai tsaye, sai kuma gobe Talata idan Allah ya kai mu inda za mu ci gaba da kawo rahotanni daga Najeriya da sassan duniya.

    Muna godiya. Za ku iya zuwa har ƙasan wannan shafin domin karanta abubuwan da suka faru a Najeriya da sassan duniya.

    Yadda ministan ma'aikatar cikin gida ta Najeriya Rauf Aregbesola ya kai wa Mai martaba sarkin Kano Aminu Ado Bayero ziyara.

    Asalin hoton, @raufaregbesola

    Bayanan hoto, Yadda ministan ma'aikatar cikin gida ta Najeriya Rauf Aregbesola ya kai wa Mai martaba sarkin Kano Aminu Ado Bayero ziyara.
  2. Za a riga buɗe gidajen barasa kafin makarantu a Kenya

    Za a sake bude gidajen sayar da barasa a Kenya a ranar Talata, watanni shida bayan an rufe su don dakile yaɗuwar kwayar cutar Korona.

    Sai dai an iyakance lokacin hada-hada zuwa karfe 10 na dare.

    Shugaban kasar Uhuru Kenyatta ne ya sanar da hakan yayin da yake yi wa al'ummar kasar jawabi game da sabbin dubarun da gwamnati ta ɓullo da su don magance cutar.

    Amma abin da ya bada mamaki shi ne yadda bai yi wani ƙarin bayani ba game da buɗe makarantu ba, abin da ke nufin cewa za su ci gaba da kasancewa a rufe.

    Sannan shugaban ya tsawaita dokar hana fita ta dare zuwa ƙarin kwanaki 60, wadda za ta riƙa aiki daga karfe 11 na dare zuwa 4 na asuba.

    Wakilin BBC ya ruwaito cewa an samu raguwar yaduwa cutar a makonnin da suka gabata.

    Ana ganin sauƙaƙa matakan kullen da hukumomin Kenyan suka yi a yanzu na da alaka da sauyin da aka samu.

    Sai dai shugaba Kenyatta ya yi gargadi da kakkausar murya, yana cewa har yanzu kasar ba ta tsira ba, don haka jama'a su kiyaye.

    ''Mun samu nasarar rage yaduwar cutar korona, amma hakan ba wai yana nufin mun kawo karshenta ba ne," in ji shi.

  3. Saudiyya ta gano wata maɓuyar ƴan ta’adda

    Yarima Salman na Saudiyya

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin Saudiyya ta ce tarwatsa wata maɓuyar wasu da ta kira ƴan ta’adda da ta gano a wannan watan inda ta kama mutum 10 tare da kuma kwace makamai da abubuwan fashewa.

    Kafofin yaɗa labaran ƙasar sun ambato wata sanarwa daga gwamnatin na cewa mutum uku da aka kama sun samu hoto ne daga dagakarun juyin juya halin Iran, sauran kuma suna da alaƙa da gidan gona inda aka gano.

    Babu dai wani cikakken bayani game da yankin da aka gano maɓuyar ƴan ta'addan

  4. An yi bikin ranar yaki da cutar karen zangai ta duniya

    Karen zangai

    Asalin hoton, @BvmLaurien

    An yi bikin ranar yaki da cutar zangai wato cizon mahaukacin kare ta duniya. A kan yi wannan bikin ne a ko wace ranar 28 ga watan Satumba domin kara fadakar da jama'a yadda za a kare kai daga cutar da kuma bayani kan ci gaban da aka samu wajen yaki da ita.

    A Najeriya, kungiyar likitocin dabbobi ta kasar NVMA ta yi bikin wannan ranar ne garin Birnin-kebbi, babban birnin jihar Kebbi.

    Dr. Nuhu Husaini Shehu, Shugaban Kungiya likitocin dabbobi a jihar Kebbi ya yi wa BBC ƙarin bayani game da ranar da kuma girman cutar ta zangai.

    Bayanan sautiAn yi bikin ranar yaki da cutar karen zangai ta duniya
  5. Yadda Liverpool da Arsenal ke shirin haduwa da juna

    Liverpool za ta karɓi bakuncin Arsenal a Anfield a gasar Premier League a daren Litinin wasan da zai ja hankalin masoya kwallon kafa.

    Ga Yadda Liverpool ke atisaye

    Liverpool

    Asalin hoton, @LFC

    Liverpool

    Asalin hoton, @LFC

    Liverpool

    Asalin hoton, @LFC

    Yadda tawagar Arsenal ke atisaye

    Arsenal

    Asalin hoton, @Arsenal

    Arsenal

    Asalin hoton, @Arsenal

    Arsenal

    Asalin hoton, @Arsenal

    Arsenal

    Asalin hoton, @Arsenal

  6. WHO za ta faɗaɗa gwajin korona a ƙananan ƙasashe

    Jami'an WHO a Najeriya

    Asalin hoton, @WHO

    Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta sanar da cimma wata yarjejeniya ta faɗaɗa gwajin korona a ƙasashe masu ƙaramin ƙarfi.

    Gwajin cutar na miliyan ɗari da ashirin cikin gaggawa da aka yi ya taimaka wajen rage yaɗuwarta wacce yanzu ta kashe kusan mutum miliyan ɗaya a duniya.

    Gwajin na bayar da sakamako cikin minti 15 kan dala biyar kawai.

    Shugaban Hukumar ya yi kira ga ƙasashe masu arziki su taimaka da tallafi kuɗi, saboda ana buƙatar kuɗaɗen domin aiwatar shirin.

  7. An naɗa mace Firaminista a Togo

    Victoire Tomegah Dogbé

    Asalin hoton, @LifeafricaTV

    Shugaban Togo ya naɗa mace matsayin Firaminista a karon farko a ƙasar.

    Victoire Tomegah Dogbé masaniya ce kan tattalin arziki kuma ta taɓa rike babban mukami a ofishin shugaban ƙasa.

    Kafin naɗin nata ta shafe shekaru fiye da 10 a matsayin ministar ci gaban matasa.

    Ta kuma taɓa aiki da hukumar Majalisar Ɗinkin Duniya UNDP

  8. Saudiyya ta ce ba za a yi taron G20 a Riyadh ba saboda annobar coronavirus

    Sarki Salman

    Asalin hoton, g

    Saudiyya – wadda a yanzu ke shugabantar kungiyar kasashe masu karfin tattalin arziki ta G20, ta ce za a yi taron kungiyar da zai gudana a watan Nuwamba ta Intanet saboda annobar korona.

    Masarautar ta ce ba za ta iya karbar bakuncin shugabannin kasashen duniya ba a Riyad – a wani taron da ake ganin zai kara daga kimar kasar a idon duniya.

    Kungiyoyin kare hakkin bil adama na duniya sun yi ta sukar Saudiyya a baya-bayan nan, kan kisan dan jaridar nan Jamal Khashoggi.

  9. 'Da jaki aka kai hari kan tawagar gwamnan Borno'

    Borno

    Asalin hoton, Getty Images

    Wani jami'i a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya ya bayyana cewa masu ta da ƙayar baya sun yi amfani da jaki wanda aka ratayawa abubuwan fashewa wajen kai wa tawagar gwamnan jihar hari.

    An kai harin ne na kwnaton bauna bayan gwamna Babagana Zulum ya tsallake rijiya da baya a harin da masu ta da kayar bayan suka kai a lokacin da yake ziyara wani yanki kusa da Tafkin Chadi ranar Juma'a.

    An kuma sake kai wa tawagar gwamnan hari a lokacin da suke komawa Maiduguri babban birnin jihar ranar Lahadi.

    Borno

    Asalin hoton, Getty Images

    Lokacin da sojoji suka ga jakin a kan titi, sun harbe shi inda abubuwan fashewar suka tashi daga nan kuma masu ta da ƙayar bayan nan take suka fito daga maboyarsu sannan suka budewa tawagar wuta, a cewar jami'in wanda yake cikin daya daga cikin motocin tawagar gwamnan.

    Kimanin mutum 18 - ƴan sanda da sojoji 14 da farar hula hudu ne suka mutu a harin kwanton baunar na ranar Juma'a.

    Gwamnan dai ya kai ziyara garin na Baga a ƙoƙarin da ake na ganin an mayar da dubban mutanen da rikicin Boko Haram ya ɗaiɗaita gidajensu.

  10. An kori jami'ai 40 a Ethiopia saboda rikicin ƙabilanci

    Habasha

    Asalin hoton, Reuters

    An kori kimanin jami'an gwamnati 40 a jihar Benishangul-Gumuz da ke yammacin ƙasar Habasha sakamakon rikicin ƙabilanci kamar yadda jam'iyya mai mulki ta PP ta sanar.

    10 daga cikin jami'an na fuskantar bincike sai dai jam'iyyar ta PP ba ta yi ƙarin haske ba.

    An jibge jami'an tsaro a gunduma biyar domin dakile rikicin da ya yi sanadin mutuwar mutane da dama tare da ɗaiɗaita ɗaruruwa a makon da ya gabata.

    Hukumar kare haƙƙin bil adama ta Ethiopia ta ce ta damu matuƙa da tashin hankalin da ya shafi farar hula.

    A harin da daka kai ranar Juma'a kimanin mutane 15 ciki har da mata hudu aka kashe.

    Hare-haren da aka kai a farkon watan nan ya halaka mutane 30 sai dai masu fafutuka sun ce adadin na iya kai wa 80.

    Akasarin mutanen da rikicin ya shafa sun fito ne daga ƙabilar Amhara da Agew.

    A ranar Lahadi, hukumomi daga jihar Amhara sun zargi jami'ai a Benishangul-Gumuz da rashin yin abin da ya kamata don hana tashin hankalin.

    Akwai damuwa game da karuwar tashe-tashen hankula masu nasaba da kabilanci a Habasha.

    Ana kallon lamarin a matsayin daya daga cikin kalubalen da ke fuskantar Firaminista Abiy Ahmed wanda ya lashe kyautar Nobel ta Zaman Lafiya.

  11. Maudu'in ƙin jinin ƴan Najeriya a Tuwita na tashe a Afirka ta Kudu

    Afirka ta Kudu

    Asalin hoton, Getty Images

    Wani maudu'i da yake ƙin jinin zaman ƴan Najeriya a Afirka ta Kudu na #NigeriansMustGo shi ne maudu'in da yake tashe a shafin Tuwita musamman a Afirka ta Kudu - wata alama da ke nuna ruruwar matsalar nan ta ƙyamar baƙi a ƙasar.

    Wannan ya zo ne ƴan kwanaki bayan wata ƙwarya-ƙwaryar zanga-zanga da aka gudanar a wajen ofishin jakadancin Najeriya da ke Pretoria babban birnin ƙasar ta Afirka ta Kudu ƙarƙashin maudu'in #PutSouthAfricansFirst wato a sanya buƙatun ƴan Afirka ta Kudu kan gaba.

    Maudu'in na #NigeriansMustGo ya samo asali ne daga wani rahoto da wata kafar yaɗa labarai a ƙasar ta yi cewa ƴan sanda sun kai wani samame lamarin da ya yi sanadiyyar kama wasu ƴan Najeriya biyar tare da zarginsu da safarar mutane bayan gano wasu mata 11 na karuwanci.

    Wasu dai ƴan Afirka ta Kudu na zargin baƙi da karɓe musu ayyukan yi da kuma aikata laifuka.

    Wasu kuma sun ce yawancin baƙin suna bin doka da oda a don haka bai kamata a zarge su ba kan taɓarɓarewar tattalin arziki da kuma matsalolin rayuwa a ƙasar.

    A zanga-zangar da aka yi a makon da ya gabata, Jakadan Najeriya a Afirka ta Kudu Bala Kabiru ya ce ba za su amince da yadda ake bayyana ƴan Najeriya ba ƙasar.

  12. Annobar korona ta janyo tsaiko kan ƙaddamar da kuɗin Eco

    Eco

    Asalin hoton, Getty Images

    Da alama shirin ƙaddamar da sabon kuɗin da zai maye gurbin CFA da mafi yawan ƙasashen yammacin Afirka ke amfani da shi ba zai tabbatu ba kusan aƙalla shekara biyar.

    Shugaban Ivory Coast Alassane Ouattara ya ce annobar korona ta janyo koma baya ga ƙoƙarin samar da kuɗin bai ɗaya na Euro a wannan shekarar.

    A watan Disambar bara, ƙasashen yammacin Afirka takwas sun yanke shawarar daina amfani da kuɗin CFA domin fara amfani da sabon kuɗin na eco.

    Asusun ba da lamuni IMF ya yi hasashen tattalin arzikin ƙasashen Afirka da ke kudu da hamadar Sahara zai ragu da kashi uku cikin ɗari a wannan shekarar.

    Ƙasashen da Faransa ta mulka kamar Benin da Mali da Nijar da Senegal sun amince su yi aiki tare domin rage giɓin da ke kasafin kuɗinsu zuwa ƙasa da kashi uku na arzikin da aka samar a kasar.

    Amma a cewar Shugaban Ivory Coast, hakan ba zai faru ba nan da shekara uku zuwa huɗu.

    Sauran ƙasashe da ba sa amfani da kuɗin CFA kamar Najeriya da Ghana suma sun nuna sha'awar shiga sabon tsarin amfani da kuɗin na eco.

    Amma Ghana ba ta son a alaƙanta kuɗin da euro yayin da ita kuma Najeriya take son sauran ƙasashen da Faransa ta mulka su yanke duk wata alaƙarsu da Paris.

  13. An sake buɗe makarantu a Zimbabwe duk da yajin aikin malamai

    Dalibai na rubuta jarabawa

    Asalin hoton, Getty Images

    Ɗalibai a Zimbabwe na komawa makaranta a karon farko cikin wata shida amma malamai daga wasu ƙungiyoyi biyu na gudanar da yajin aiki bayan bayyana fargaba kan lafiya saboda annobar korona.

    Tun da farko an rufe makarantun a farkon shekarar nan saboda annobar.

    Gwamnati ta ce ɗaliban ba za su kasance cikin wata barazana ba amma wakilin ƙungiyar Obert Masaraure ya faɗa wa BBC cewa ba za a koyar ba a akasarin makarantun.

  14. Saudiyya za ta yanke shawara kan ƴan ƙasashen da su iya zuwa Umrah

    korona

    Asalin hoton, Reuters

    Ministan kula da aikin Hajj da Umrah a Saudiyya Muhammad Saleh Benten ya bayyana cewa ma'aikatar lafiyar ƙasar za ta yanke shawara kan ƙasashen da za su baiwa damar tura al'umarsu zuwa Umrah.

    Sanarwar ministan ta biyo bayan wata sanarwa da ministan cikin gida ya fitar da ke cewa Saudiyya za ta bai wa al'umomin wasu ƙasashen damar zuwa ƙasar bayan da aka janye dakatarwar da aka yi game da gudanar da umrah daga ɗaya ga watan Nuwamba.

    Benten ya ce cikin sa'a 24 na kashin farko, za a bar tawagar mutane 12 ne su gudanar da Umrah sannan kuma maniyyata da ke tsakanin shekara 18 da 65 ne kawai za a bari su yi umrah.

    Shafin Saudi Gazette ya rawaito ministan cewa ba za a bar kowane maniyyaci a aikin umrah ba ya shiga masallacin Makkah ba tare da cika ƙa'idojin shiga wajen ba ta intanet.

    Ya ce za a yi haka ne domin kare lafiyar maniyyatan.

  15. MDD na son a yafe wa wanda ya yi ɓatanci ga addini a Najeriya

    Kano

    Asalin hoton, IDRIS IBRAHIM

    Wasu ƙwararru kan kare haƙƙin bil adama a Majalisar Dinkin Duniya sun buƙaci a saki ɗan Najeriyar nan da aka yankewa hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda yin ɓatanci ga addini.

    An yanke wa matashin Yahaya Sharif-Aminu mai shekara 22 hukuncin ne ranar 10 ga watan Agusta bayan samunsa da yin ɓatanci cikin wata waƙa da ya yi.

    Cikin wata sanarwa, ƙwararrun su 10 sun nemi a soke hukuncin inda suka ce tun farkon shari'ar matashin bai samu lauyan da zai kare shi ba.

    A cewarsu, yin waƙa ba laifi bane.

    Dakta Piotr Cywinski, ya ce shi da wasu ƴan sa-kai 119 daga sassan duniya za su yi wa yaron zaman gidan yari na wata ɗaya ko wannensu.

  16. Ƴan sandan Afirka ta Kudu sun kama mutumin da ya yi wa jami'in gwamnati sojan gona

    Ƴan sanda a Afirka ta Kudu sun kama wani mutum mai shekara 28 bisa zarginsa da yi wa wani magajin gari sojan gona.

    Ya kuma yi yunƙurin damfarar wata mata har da yi mata alƙawarin ba ta kwangila.

    An miƙa mutumin ofishin ƴan sanda da ke Durban inda ake zarginsa da karɓar kuɗi ba bisa ƙa'ida ba.

    A yau ne kuma zai bayyana a gaban kotu.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  17. Kasuwar ‘yan kwallo: Makomar Kante da Jorginho da Mata da King da Garcia

    Wasanni

    Manchester United ta tuntubi wakilan dan wasan Faransa N'Golo Kante domin dauko shi daga Chelsea, sai dai idan dan wasan zai tafi za a rage albashinsa na mako-mako inda ake biyansa £300,000. (Mirror)

    Paris St-Germain tana tattaunawa da Chelsea domin karbo aron dan wasan Italiya Jorginho, mai shekara 28. (Telefoot, via Mail)

    Lazio za ta iya soma zawarcin 'yan wasan Manchester United guda biyu - dan wasan Sufaniya mai shekara 32 Juan Mata da dan wasan Brazil Andreas Pereira, mai shekara 24. (Sun)

    Tottenham na sanya ido kan dan wasan Bournemouth dan kasar Norway Joshua King, mai shekara 28 a yayin da take son dauko dan wasan gana kafin a rufe kasuwar 'yan kwallon kafa. (Telegraph - subscription required).

    Kuna iya shiga nan domin karanta ƙarin bayani.

  18. Yadda ake tallafa wa makiyayan Kamaru don bunƙasa kiwo

    Wata ƙungiya mai suna ACEFA ta ƙasar Faransa ta bayyana ƙudirinta na tallafa wa ƙungiyoyin makiyaya da kudi da horo don bunƙasa sana’ar kiwo.

    Ƙungiyar ta ƙudiri wannan aniya ne a wani mataki na yaƙi da fatara a tsakanin al’umma da taimaka wa juna,

    Ɗaya daga cikin ƙungiyoyin da suka ci moriyar wannan tallafi mai suna “Kiwo a Sawwaƙe” da ke unguwar Fadama a birnin Garoua da ke Kamaru kuma mamba a cikin ƙungiyar Aminatu Dadaji ta ce sun fara kiwo ne da dabbobi ƙadan kamar 15.

    A cewarta, suna samun biyan buƙata idan suka sayar da dabbobin.

    Bayanan sautiLatsa alamar lasifikar domin sauraron rahoton Mohamman Babalala
  19. Hotuna: Yadda aka yi jana'izar sojojin da suka mutu a harin Borno

    Borno

    Asalin hoton, Getty Images

    Borno

    Asalin hoton, Getty Images

    Borno

    Asalin hoton, Getty Images

  20. Yawan masu korona a duniya sun zarce miliyan 30

    Korona

    Asalin hoton, EPA

    Adadin masu fama da annobar korona a duniya yanzu ya zarce miliyan 33 a cewar Jami'ar Johns Hopkins.

    Amurka ce ke da kashi mafi tsoka na mutanen da suka kamu inda take da mutum miliyan 7.1 sannan India mai mutum kusan miliyan 6.1 sannan Brazil da take da mutane miliyan 4.7.

    Binciken da aka gudanar a Jami'ar Johns Hopkins ya nuna cewa akwai kusan mutum miliyan ɗaya da aka tabbatar korona ta halaka a duniya. wata 10 bayan da ɓullar cutar a birnin Wuhan na ƙasar China.