'Yar Majalisar Tarayyar Amurka kuma 'yar asalin Somalia Ilhan Omar, ta caccaki Shugaban Amurka Donald Trump, inda ta ce yana mulkin ƙasar kamar wani yaro ɗan shekara takwas.
'Yar majalisar ta bayyana hakane yayin da take mayar da martani kan wasu jawabai da shugaban ya yi yayin wani yaƙin neman zaɓe da yaje a daren jiya inda ya ce:
"Za mu lashe zaɓe a jihar Minnesota saboda ita, in ji su. Har za ki gaya mana yadda za mu yi mulki a ƙasarmu, me kika yi a ƙasar da kika fito? Me ke faruwa a ƙasar ki? Wai tana gaya mana yadda za mu yi mulkin ƙasarmu."
Ita kuma a nata martanin da ta mayar, ta bayyana cewa:
"Da farko, wannan ƙasata ce, kuma ina daga cikin 'yan majalisar da muka tsige ka. Na baro ƙasarmu lokacin da nike 'yar shekara takwas. 'Yar shekara takwas ba za ta iya mulkin ƙasa ba duk da cewa kai kana mulkin ƙasar tamu kamar ɗan shekara takwas," in ji Ms Omar kamar yadda ta wallafa a shafinta na Twitter.
An haife ta ne a Somalia amma kuma iyayenta sun koma Amurka da zama bayan da yaƙin basasa ya ɓarke a cikin shekarun 1990.