'Yan sanda sun yi wa gidan shugaban 'yan adawa a Kamaru ƙawanya
'Yan sanda a Kamaru sun yi wa gidan shugaban 'yan adawa a ƙasar ƙawanya.
Sun yi wa gidan na Mista Maurice Kamto ƙawanya ne sakamakon zanga-zangar da ya haɗa a ranar Talata ta ƙin jinin gwamnati.
Ana ta yaɗa wani bidiyo da ke nuni da motocin 'yan sanda jibge a ƙofar gidan shugaban.
Shugaban ƙungiyar ta CRM ya shaida wa kafar yaɗa labarai ta Muryar Amurka cewa babu wanda ya buge shi ko kuma kama shi, amma yana tsoron za a kama shi da ya fita daga cikin gidansa.
Mista Kamto, ya kira zanga-zangar ne don a kawo ƙarshen rikicin da ke faruwa a yankin renon Ingila da kuma kawo sauyi kan tsarin zaɓen ƙasar.