Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Rahoto kai-tsaye
Mustapha Musa Kaita and Fauziyya Kabir Tukur
Rufewa
A nan za mu yi bankwana da ku. Sai kuma gobe Alhamis inda za mu ci gaba da kawo maku labarai daga Najeriya da sauran sassan duniya a wannan shafin.
Kuna iya kewaya shafin don karanta labaran da muka kawo maku tun daga safiyar yau.
Mu kwana lafiya!
An sa sabuwar ranar gudanar da taron Commonwealth
Asalin hoton, AFP
Taron shugabannin kasashen Commonwealth (Chogm) wanda aka daga a watan Afrilu saboda annobar cutar korona, zai gudana yanzu a watan Yunin shekara mai zuwa a Kigali, babban birnin Rwanda.
Taron da ake gudanarwa sau daya a shekaru biyu, shi ne taro mafi shahara na Commonwealth.
Za a gudanar da taron ne a makon 21 ga watan Yunin 2021.
Sakatariyar Commonwealth din ta ce kasashe mambobin ne suka amince da sabuwar ranar yin taron.
Buhari zai tafi Guinea Bissau
Asalin hoton, BAYO OMOBARIYOWO
Shugaba Muhammadu Buhari zai tafi Bissau ranar Alhamis don halartar bikin zagayowar ranar samun 'yancin Jamhuriyar Guinea Bissau ran 24 ga Satumba.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa manyan ma'aikatan gwamnati za su raka Shugaba Buharin cikinsu har da Ministan Harkokin Kasashen Waje, Geoffrey Onyeama da Ministan Tsaro Manjo-Janar Bashir Salihi Magashi mai Ritaya da Babban mai bai wa Shugaban Kasa shawara kan lamurran tsaro da Shugaba Hukamar Leken Asiri ta kasa Ahmed Rufa'i Abubakar.
Haka kuma, jaridar ta ruwaito Shugaban zai hadu da shugabannin Sanegal da Cote d'Ivoire da Rwanda da Mauritania da Togo da Liberia don bikin shekara 47 da samun 'yancin Guinea Bissau din.
Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Femi Adesina ya fitar ta ce Buhari zai ci abincin rana da sauran shugabannin kasashe da Shugaba Umaro Sissoco Embalo na Guinea Bissau.
Ku saurari Labaran Duniya cikin Minti Ɗaya Na BBC Hausa
Bayanan sautiMinti Ɗaya Da BBC Hausa Na Yamma 23/09/2020
Burtaniya da Faransa da Jamus na so a sako 'yan kasarsu daga Iran
Asalin hoton, Reuters
Kasashen
Burtaniya da Faransa da Jamus sun nemi Iran ta saki wasu mutanensu masu shaidar
zama ‘yan kasa biyu da suka ce ana tsare da su ba bisa ka’ida ba.
Cikin
wata wasikar hadin gwiwa, kasashen uku sun yi kiran a saki ‘yan kasarsu, ciki
har da wani mai takardar zama dan Burtaniya da Iran domin su sake haduwa da
iyalansu.
Sun
kuma nuna damuwa kan yadda ake ci gaba da gurfanar da mutane a Iran, wadanda ke
fafutukar kare hakkin dan adam.
Wakilin BBC na fannin Diflomasiyya ya ce, wannan sako na
da muhimmanci ganin cewa kasashen uku na kare Iran kan yarjejeniyar nukiliya
ta 2015, tare da kin amsa kiran Amurka na neman Majalisar Dinkin Duniya ta kara
sanya mata takunkumi
Ana zargin sama da naira biliyan talatin sun bace a Zamfara
Gwamnatin jihar Zamfara da ke Najeriya ta zargi tsohuwar gwamnatin jihar da batan wasu kudaden ayyukan gwamnatin tarayya da ta gudanar, kimanin sama da naira biliyan talatin da bakwai wanda ta ce an mayar wa da gwamnatin jihar.
Amma kuma tsohuwar gwamnatin ta musanta wannan zargin ne da cewa kudaden suna nan a asusun gwamnati babu ko kwabo da ya bace.
Ku latsa lasifikar da ke ƙasa don sauraron rahoton da Bilkisu Babangida ta hada mana.
Bayanan sautiRahoton da Bilkisu Babangida kan ɓatan kudin Zamfara
Hezbollah ce ta janyo fashewar sinadarai a Lebanon- Sarki Salman
Asalin hoton, EPA
Sarki
Salman na Saudiyya ya yi kira ga ‘yan kungiyar Hezboullah da ke Lebanon da su
ajiye makamansu.
Ya ce karfin ikon da kungiyar ta ke da shi a kasar ne ya
janyo wannan mummunar fashewar sinadaren da aka samu a Beirut a watan jiya.
A
wani bayani da ya yi wa taron Majalisar Dinkin Duniya, Sarki Salman ya nemi
hadin kan kasashen kan abin da ya kira mafita game da Iran.
Ya ce yana goyon bayan mutanen na Lebanon wadanda ke fuskantar
wannan tashin hankali na fashewar sinadarai a tashar ruwa ta Beirut, wadda ta
faru saboda ikon da Hezbollah ke da shi, kungiyar ‘yan ta’adda da ke samun
goyon bayan Iran.
Ya
kuma kara da cewa Iran ta yi amfani da yarjejeniyar makamai ta 2015 da aka
cimma da manyan kasashen duniya, domin ta kara fadada abin da ya kira rikici da
ra’ayin rikau da kuma nuna bangarancin addini.
An samu dan sanda da laifin kisan Breonna Taylor
Asalin hoton, FACEBOOK
An samu wani dan sanda, Brett Hankinson da laifin kashe wata mata bakar fata Breonna Taylor a cikin gidanta da ke jihar Kentucky a Amurka.
Ranar 13 ga watan Maris ne aka harbi Breonna a kalla sau biyar a wani samame na kuskure da aka kai a birnin Louisville.
Kisan nata ya janyo zanga-zangar nuna kin jinin wariyar launin fata, inda masu zang-zangar suka rika kira da a kama 'yan sanda ukun da ke da hannu a kisan.
A watan Yunin ne aka kori Mista Hankinson daga rundunar 'yan sanda bayan da masu bincike suka gano cewa ya saki harsasai 10 da gangan kuma ba da wani dalili ba a cikin gidan Breonna Taylor.
Coronavirus: An yabi Afrika kan yaki da cutar korona
Asalin hoton, ANADOLU AGENCY
Shugaban hukumomin da ke yaki da cutuka masu yaduwa na Afrika, John Nkengasong ya yabi kasashen nahiyar kan yadda suka dauki matakan hana yaduwar cutar korona.
Mutum kusan miliyan daya da dubu dari hudu ne suka kamu da cutar a nahiyar yayin da mutum 34,000 suka mutu tun daga watan Maris.
Wadannan alkaluman ba su kai na Turai da Asiya da Amurka ba.
Daukar matakan kariya daga farko-farkon bullar cutar ta taimaka wajen yadda aka yake ta a cewar shugaban hukumomin John Nkengasong.
Kashi 5 cikin 100 na mutanen da suka kamu da cutar da kashi 3.6 cikin 100 na wadanda suka mutu a fadin duniya ne kawai suka fito daga nahiyar da ke da sama da mutum biliyan daya.
Gwamnatin Najeriya ta ce ta bayar da umarnin raba kudin tallafin
da suka kai kimanin Naira biliyan 10 da miliyan 900. Haka kuma shugaban kasar Muhammadu Buhari ya fuskanci annobar
koronan na mayar da hannun agogo baya a kokarin da ake na cimma ci gaba mai
dorewa na 2030.
Tawagar hukumar lafiya ta duniya a Mauritania ta binciko kusan
masu korona 5,000 a yankuna shida na kasar cikin kwanaki 12. Tawagar da ke aiki
da wasu kungiyoyi masu zaman kansu, na bibiyar wadanda suka yi mu’amala da masu
cutar domin dakatar da cutar.
Masar ta shiga
cikin jerin kasashen da suke habbaka a watan Yunin 2020, bayan ta samu
sahhalewar majalisar hukumar shirya tafiye-tafiye da yawon bude ido ta duniya. Sauran kasashen da ke cikin jerin sun hada da Philippines da Maldives da Uganda da Bermuda da Montenegro.
Abin da ya sa ba za mu janye yajin aikin da muka shirya ba - NLC
Ƙungiyoyin ƙwadago na Najeriya sun yanke shawarar tsunduma cikin yajin aiki na gama-gari daga ranar Litanin mai zuwa.
Daukar matakin ya biyo bayan wani taro ne da shugabanin ƙwadagon suka yi,
mako guda bayan wa'adin makonni biyu da suka baiwa gwamnati na ta janye karin
kudin man petur da na wutar lantarki.
Tun dai a baya kungoyoyin sun bai wa gwamnatin tarraya wa’adin mako biyu
domin janye ƙarin kuɗin man fetur da na lantarki da ta yi.
Kabiru Nasir shi ne mataimakin sakataren haɗaɗɗiyar ƙungiyar ƙwadago ta NLC
a Najeriya, ga kuma karin bayanin da ya wa Abdou Halilou a cikin tattaunawarsu.
Bayanan sautiHirar Abdou Halilou da Kabiru Nasir na NLC
An kama tsoho mai shekara 60 da 'ya yi wa ƴar shekara biyar fyaɗe a Bauchi'
Rundunar ƴan sandan jihar Bauchi ta sake cafke wani tsoho
mai shekara 60 mai suna Mohammed Dahiru kan zargin fyaɗe ga wata yarinya ƴar shekara biyar da haihuwa, a ƙauyen
Nahuta da ke ƙaramar hukumar Toro.
Ko a makon jiya ma sai da rundunar ƴan sandan ta bayar da sanarwar cafke
mutum 20 a bisa aikata laifin fyaɗen a wurare da kuma lokuta daban-daban a
jihar.
DSP Ahmed Mohammed Wakili shi ne kakakin rundunar ƴan sandan jihar Bauchi
kuma a hirarsu da Bilkisu Babangida ya yi mata ƙarin bayani.
Ku latsa lasifikar da ƙasa don sauraron hirar.
Bayanan sautiHirar Bilkisu Babangida da DSP Ahmed Mohammed Wakili na Bauchi
Wakilan Isra'ila sun isa Bahrain don tattauna yadda alaƙarsu za ta kasance
Asalin hoton, Getty Images
Rahotanni na cewa wakilan Isra’ila sun sauka a Bahrain, domin tattaunawa daki-daki kan yadda yarjejeniyar alaƙar da kasashen biyu suka sanyawa hannu a makon jiya za ta yi aiki.
Bahrain ba ta bayyana za ta karɓi baƙuncin ganawar ba, amma wani babban jami’in Isra’ila ya tabbatar da hakan a shafin sada zumuntar Isra’ilan.
Tafiyar na zuwa ne bayan Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da yarima mai jiran gado na Bahrain Salman bin Hamad Al Khalifa sun yi wata tattauna ta waya a ranar Talata.
Wannan ne karon farko da jirgin Isra’ila ya bi ta sararin samaniyar Saudiyya cikin lokuta masu tsawo.
Tun ranar da Sarkin Zazzau ya rasu, ba na iya bacci sai na sha magani – El Rufai
Asalin hoton, @GovKaduna
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El Rufai, ya bayyana cewa tun ranar Lahadi da aka sanar masa da rasuwar Sarkin Zazzau, bai sake bacci ba sai ya sha magani saboda baƙin ciki.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a wurin taron addu'ar uku na Marigayi Mai martaba Sarkin Zazzau, Dakta Shehu Idris wanda ya rasu a ranar Lahadi.
Manyan mutane da dama sun halarci addu'ar uku da aka yi a yau irin su Tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo da Gwamnan Jigawa Abubakar Badaru, da Gwamnan Ekiti Kayode Fayemi da na Filato Simon Lalong.
Wakilan Isra'ila sun isa Bahrain domin tattaunawa
Rahotanni na cewa wakilan Isra’ila sun sauka a Bahrain, domin tattaunawa kan yadda yarjejejniyar alaƙar da ƙasashen biyu suka sanyawa hannu a makon jiya za ta yi aiki.
Bahrain ba ta bayyana za ta karbi baƙuncin ganawar ba, amma wani babban jami’in Isra’ila ya tabbatar da hakan a shafin sada zumuntar Isra’ilan.
Tafiyar na zuwa ne bayan Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da yarima mai jiran gado na Bahrain Salman bin Hamad Al Khalifa sun yi wata tattaunawa ta waya a ranar Talata.
Wannan ne karon farko da jirgin Isra’ila ya bi ta sararin samaniyar Saudiyya.
Minti Ɗaya Da BBC Na Rana 23 09 2020
Bayanan sautiLatsa alamar lasifikar da ke sama domin sauraren labaran
Kamfanin Johnson & Johnson zai yi gwajin matakin ƙarshe na riga-kafin korona
Kamfanin samar da magani na Johnson & Johnson ya zama kamfani na huɗu da zai yi gwajin matakin ƙarshe na riga-kafin annobar korona.
Kamfanin na Johnson & Johnson ɗin ya bayyana cewa a gwajin farko, za a fara ne da mutum dubu 60 a faɗin nahiyar Amurka da kuma Afrika Ta Kudu.
Ana ganin cewa za a samu sakamakon gwajin zuwa ƙarshen 2020, ko kuma farkon shekara mai zuwa.
Waɗanda za a yi gwajin da su za a tsira musu allurai biyu, za bayar da tazarar makonni da dama tsakanin alluran,
Gobarar tankar mai ta yi sanadin mutuwar mutane da dama a Lokoja
Bindigar da wata tankar mai ta yi a Lokoja, babban birnin jihar Kogi da ke tsakiyar Najeriya ta yi sanadin mutuwar mutane da dama.
Lamarin ya faru ne a yankin Felele dazun nan kuma hotunan da aka watsa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda mutane da dama suka ƙone ƙurmus.
Wani ganau, Ahmed Sai'du Bilal, ya shaida wa BBC cewa lamarin ya faru ne a yayin da direban tankar motar ya yi ƙoƙarin yin ajiye mota amma ta ƙwace daga hannunsa.
'Yar Majalisar Tarayyar Amurka kuma 'yar asalin Somalia Ilhan Omar, ta caccaki Shugaban Amurka Donald Trump, inda ta ce yana mulkin ƙasar kamar wani yaro ɗan shekara takwas.
'Yar majalisar ta bayyana hakane yayin da take mayar da martani kan wasu jawabai da shugaban ya yi yayin wani yaƙin neman zaɓe da yaje a daren jiya inda ya ce:
"Za mu lashe zaɓe a jihar Minnesota saboda ita, in ji su. Har za ki gaya mana yadda za mu yi mulki a ƙasarmu, me kika yi a ƙasar da kika fito? Me ke faruwa a ƙasar ki? Wai tana gaya mana yadda za mu yi mulkin ƙasarmu."
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Ita kuma a nata martanin da ta mayar, ta bayyana cewa:
"Da farko, wannan ƙasata ce, kuma ina daga cikin 'yan majalisar da muka tsige ka. Na baro ƙasarmu lokacin da nike 'yar shekara takwas. 'Yar shekara takwas ba za ta iya mulkin ƙasa ba duk da cewa kai kana mulkin ƙasar tamu kamar ɗan shekara takwas," in ji Ms Omar kamar yadda ta wallafa a shafinta na Twitter.
An haife ta ne a Somalia amma kuma iyayenta sun koma Amurka da zama bayan da yaƙin basasa ya ɓarke a cikin shekarun 1990.