Ana ci gaba da ce-ce ku-ce kan kalaman tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo game da mulkin Shugaba Buhari da kuma martanin da fadar shugaban ƙasar ta mayar.
Martani na baya-bayannan shi ne wanda Kungiyar Dattawan Arewa ta Northern Elders Forum (NEF) ta yi na kare kanta game da zargin fadar shugaban ƙasar cewa kungiyoyin da suka halarci taron da tsohon Obasanjo ya yi na mutane ne masu kalaman ƙabilanci da nuna ɓangaranci.
Mai magana da yawun ƙungiyar ta NEF wadda ke ɗaya daga kungiyoyin da suka halarci ganawar da Obasanjo, Dr Hakeem Baba-Ahmed ya ce a ganinsa taron na ciyar da ƙasa gaba ne kuma abin a yaba.
A yayin taron dai tshohon shugaban na Najeriya Obasanjo ya bayyana cewa Najeriya na taɓarɓarewa a ƙarƙashin mulkin Buhari, yayin da kalaman ƙiyayya ke ƙara zama ruwan dare.
Ya ce tattaunawa ta haƙiƙa da 'yan Najeriya ce kaɗai za ta magance matsalar ta kalaman ƙiyayya da kuma matsalolin da kasar ke fuskanta.
A martaninsa, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewa tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo na ƙoƙarin raba kan 'yan Najeriya ne sakamakon irin kalaman da yake yi a 'yan kwanakin nan.
A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban, Malam Garba Shehu ya fitar a ranar Lahadi, ya bayyana cewa Shugaba Buhari a kullum yana ƙoƙarin haɗa kan 'yan Najeriya ne da kuma gina ƙasar.
Shugaba Buhari ya ce Obasanjo ya zama "babban mai raba kan ƙasa," kamar yadda sanarwar Garba Shehu ta bayyana.
Ko a ƙarshen makon jiya sai da Ministan Yaɗa labarai Lai Mohammed ya yi wasu kalamai da suke nuna tamkar martani ne ga Obasanjo, inda ya ce "ba don Buhari ba da yanzu Najeriya ta ruguje".
Sai dai 'yan Najeriya da dama na ci gaba da matani kan kalaman na Lai Mohammed a kafofin sada zumunta musamman Twitter.