Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Jirgin ƙasa ya tunkuyi motoci a Lagos

Wannan shafi na kawo muku bayanai kai-tsaye dangane da irin wainar da ake toyawa a fadin duniya musamman batutuwan da suka shafi Najeriya da Nijar da makwabtansu.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Nasidi Adamu Yahaya

  1. Mu kwana lafiya

    A nan muke kawo karshen labarai da rahotannin da muke kawo muku a wannan shafi. Ku kasance tare da mu gobe domin samun sabbin labarai. Sai dai za ku iya lekawa kasa domin karanta bayanai da muka kawo muku tun daga safiyar yau.

    Mun gode

  2. Hadaddiyar Daular Larabawa ta amince a yi wa ma'aikatan lafiya riga-kafi

    Gwamnatin Hadaddiyar Daular Larabawa ta amince a yi amfani da riga-kafin Covid-19 kan ma'aikatan lafiyar da ke yaki da cutar korona baan da aka yi nasarar gwada maganin.

    Ministan lafiyar kasar ya ce za a yi amfani da riga-kafin a yanayi irin na "gaggawa" idan ya safi ma'aikatan lafiyar.

    Ya kara da cewa an yanke shawarar ce bayan an yi gwajin riga-kafin sau uku kuma ya nuna cewa ba shi da wata matsala.

    A cewarsa, tuni mutu 31,000 suka amince a yi gwajin riga-kafin a kansu, wadanda suka fito daga kasase 125.

  3. Ma'aikatan lafiya sun yi zanga-zanga a Morocco

    Ma'aikatan lafiya a Morocco sun kwashe makonni suna gudanar da jerin zanga-zanga domin neman a inganta yanayin da suke aiki sanadin barkewar annobar korona.

    Kimanin mutum 2,430 suka kamu da cutar a kasar ranar juma'ar da ta wuce, kuma ana samun karin fiye da mutum 1,000 da ke kamuwa da ita kullum tun daga watan Yuli.

    Kungiyar ma'aikatan lafiya ta ce wuraren kula da mutane na gaggawa sun cka makil da marasa lafya.

    Ma'aikatar lafiya ta Morocco ta yi yunkurin samar da karin wuraren kula da lafiya inda ta kafa tantuna ta sanya gadaje da iskar da ake sanyawa marasa lafiya.

    Sai dai ma'aikatan lafiyar sun ce babbar matsalar ita ce ta rashin isassun ma'aikata musamman a yankunan karkara.

  4. An kama mutum ɗauke da ƙoƙon kan yaro a majalisar dokoki

    'Yan sanda a Uganda sun kama wani mutum a kofar shiga majalisar dokokin kasar rike da jakar da ke dauke da kan wani yaro da aka yanke.

    Ba a san sakon da mutumun yake son isarwa ba.

    Kazalika ba a san inda ya samo kan yaron ba.

    Tuni dai 'yan sandan da ke bincike suka soma yi masa tambayoyi.

    Wata majiya a rundunar 'yan sandan ta ce an sanar da batan yaron a yankin Masaka da ke kudancin Kampala, babban birnin kasar ranar Lahadi.

    Kazalika an gano gawar da babu kai a jikinta a yankin a ranar ta Lahadi.

    'Yan sanda na gudanar da bincike don ganin ko akwai alaka tsakanin mutumin da aka kama da gawar da aka gano ba tare da kai a jikinta ba.

    A shekarun 1990 zuwa 2000, Uganda ta sha fama da satar kananan yara inda ake kashe su domin yin tsafe-tsafe.

    A shekarun baya bayan nan, an samu rahotannin ajiye kananan aladu a kofofin majalisar dokokin, domin yin tur da cin hanci da rashin ayyukan yi a kasar.

  5. Karin mutum 2,621 sun kamu da cutar korona a Birtaniya

    An samu karin mutum 2,621 da suka harbu da cutar korona a fadin Birtaniya.

    Hakan raguwa ce da fiye da mutum 600 da suka kamu da cutar ranar Lahadi, inda mutum 3,330 suka kamu da cutar.

    Kodayake galibi ana samun raguwar masu kamuwa da cutar a ranakun karshen mako, saboda jinkirin bayar da rahoto.

    An samu karin mutum tara da cutar ta kashe tun karfe 9 na saifiyar Lahadi, inda jumulla mutum 41,628 suka mutu sanadin cutar a Birtaniya.

  6. Jirgin ƙasa ya tunkuyi motoci a Lagos

    Mutum guda ya mutu sannan mutum biyu suka ji munanan raunuka sakamakon karon da motoci uku suka yi da wani jirgin kasa a Lagos, cibiyar kasuwancin Najeriya, a cewar hukumomi.

    Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Lagos ta ce mutumin da ya mutu na cikin fasinjoji biyu da ke cikin mota kirar SUV da ta yi karo da jirgin kasa lokacin yana kan hanyarsa a yankin Oshodi ranar Litinin.

    Har yanzu babu cikakken bayani kan yadda lamarin ya faru, sai dai ana zargin motocin uku sun yi kokarin haurawa ta layin dogo amma suka kasa kafin isowar jirgin.

    An janye motocin biyu - SUV da wata motar bas mai dauke da fasinja shida - zuwa wasu 'yan mitoci daga kan layin dogo kafin jirgin ya tsaya.

    Mutane da dama sun samu kananan raunuka kuma an ba su magani a wurin da lamarin ya faru kodayake an kai wadanda suka ji rauni sosai asibit, a cewar Lasema.

    Wakilin BBC a Lagos Andre Gift ya ce lamarin ya kawo tsaikon zirga-zirga a yankin ta kusan awa biyu.

    Oshodi ne yankin da aka fi zirga-zirgar motoci a Lagos.

  7. Masu daukar gawa sun soma yajin aiki a Afirka ta Kudu

    Ma'aikatan da ke daukar gawa kusan 3,000 sun tsunduma yajin aiki a Afirka ta Kudu inda suke bukatar a inganta yanayin aikinsu da kuma kara musu albashi.

    Sun ki daukar gawarwaki daga gidaje da asibitoci - da kuma yi musu jana'iza.

    Kungiyar ma'aikatan daukar gawa ta yi kira ga gwamnati ta kafa gidauniyar tallafa musu saboda cutar korona.

    Kudaden binne gawa da na kona ta sun karu da kashi 25 cikin dari tun da annobar korona ta barke, saboda bukatar tufafin bayar da kariya, da man goge hannu da wasu kayayyakin.

    Hukumomi sun ce suna fargabar cewa yajin aikin yana iya haifar da matsala kan harkokin lafiya.

  8. Minti Daya da BBC Na Rana 14/09/2020

    Ku saurari Minti Daya da BBC Na Rana 14/09/2020.

  9. 'Yan sanda sun kama wani mai shirya fim ɗin batsa a Najeriya

    'Yan sandan Jihar Osun da ke kudancin Najeriya sun kama wani mutum da ya ɗauki fim ɗin batsa a wani wurin bauta da ke Dajin Osun Osogbo mai tsarki.

    Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Yeisi Opalola ya ce sun kama Tobi Jolaosho wanda aka fi sani da King Tblak ne bayan wani mamban ƙungiyar addinin gargajiya ya kai musu koke.

    Rahotanni sun ce Jolaosho ya yi shiga irinta masu bauta tare da wata mace tsirara sannan ya shiga dajin kuma ya ɗauki fim ɗin a watan Yuli da ya gabata tare da yaɗa shi a shafukansa na sada zumunta.

    Amoo Awosunwon, wani mai bauta a Idinleke, ya ce ya ga Jolaosho da idanunsa yana ɗaukar fim ɗin batsar a dajin kuma ya faɗa masa cewa aikin nasa zai iya jawo rashin jituwa a tsakanin al'umma.

    Jolaosho wanda kuma ake yi wa laƙabi da King Tblak HOC, yana kiran kansa a matsayin tauraron fim ɗin batsa a Najeriya kuma yana da mabiya fiye da 20,000 a dandalin Twitter - inda yake wallafa bidiyon fina-finan batsar.

    Kazalika, an kalli fim ɗin batsa a shafinsa na intanet sau fiye da miliyan 109.

    Al'ummar Yarabawa na kallon Dajin Osun Osogbo a matsayin wani wurin bauta mai tsarki, inda suka yi imanin cewa Osun Osogbo ɗaya ce ɗaga cikin matan abin bautar addinin gargajiyarsu mai suna Sango.

    Hukumar adana wuraren tarihi ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNESCO) ta ayyana wurin a matsayin wurin tarihi na duniya.

  10. Jihohi su shirya nema wa 'yan gudun hijirar ambaliya mafaka - Sadiya Umar

    Ministar Ma'aikatar Agaji, Cigaban Al'umma da Kare Afkuwar Bala'i, Sadiya Umar Farouq ta ce ƙaramar hukuma 377 na jiha 36 ne aka yi hasashen za su fuskanci ruwan sama mai yawa da ambaliyar ruwa a wannan shekara.

    Ministar ta bayyana haka cikin wata yekuwa da ta yi, inda ta shawarci jihohin da suke cikin jerin da su nemi kan tudu domin gina mafaka ga mutanen da ruwan zai raba da mahallansu.

    "Ambaliyar ruwa ta baya-bayan nan a wasu yankuna ta tabbatar da buƙatar da ake da ita ta ɗaukar matakan gaggawa domin kare rayuka da dukiyoyin al'umma a wuraren da ake tsammanin ambaliyar," in ji ta.

    "Hasashen 2020 na ruwan sama da kuma ambaliya ya nuna za a samu ruwa mai yawa a ƙaramar hukuma 102 na jiha 28, yayin da ƙaramar hukuma 275 a jiha 36 - har da Abuja - za su fuskanci matsakaiciyar ambaliyar ruwa.

    "Sauran ƙaramar hukuma 397 na cikin waɗanda ba sa fuskantar hasashen ambaliya mai girma. Abin baƙin ciki, tuni ambaliyar ta fara faruwa a yankunan jihohin Bauchi da Kebbi da Jigawa. Saboda haka yana da kyau a ɗauki duk matakin da ya dace don kauce wa faruwar hakan."

  11. Ana fargabar harin Boko Haram a sansanin 'yan gudun hijirar Najeriya a Kamaru

    Sansanin 'yan gudun hijirar Boko Haram na ci gaba da fuskantar kutsen 'yan kungiyar Boko Haram a garin Zeleved da ke Lardin Arewacin Ƙasar.

    Sau uku kenan a jere ana zargin ƙungiyar da kai hari sansanin na Zeleved kuma a duk lokacin da hakan ya faru yana barin baya da ƙura.

    Jama’ar da rikicin ya raba da muhallinsu na cikin wani hali na fargaba da rashin sanin madogara tun ƙarshen makon jiya lokacin da basaraken gargajiya na Zeleved da uwargidansa da wasu mutum huɗu suka rasa rayukansu.

    Mutanen sun mutu ne sakamakon wani hari da ake zargin Boko Haram da kaiwa.

  12. Gobara ta halaka ɗaliban firamare 10 a ɗakin kwanansu a Tanzania

    Ɗaliban firamare 10 sun rasa rayukansu sakamakon gobarar da ta tashi a ɗakunan kwanan ɗalibai a wata makaranta da ke arewacin yankin Kagera na ƙasar Tanzania.

    An kwantar da wasu ɗaliban guda bakwai da suka ji munanan raunuka a asibiti.

    Yara 'yan shekara shida zuwa 10 ne ke kwana a ɗakunan. 'Yan sanda sun fara bincike amma zuwa yanzu ba a san abin da ya haddasa gobarar ba.

    Wutar ta fara tashi ne a ɗaya daga cikin ɗakunan kwanan makarantar firamare ta Byamungu English Medium da ke unguwar Kyerwa da misalin ƙarfe 04:30 na dare.

    Kwamishinan yankin mai suna Rashid Mwaimu ya faɗa wa BBC cewa yaran sun ƙone ta yadda ba za a iya gane su ba kuma sai an yi musu gwajin ƙwayar halitta kafin a iya gane su.

    Ana yawan samun gobara a makarantu a yankin yayin da ake ƙara matsa wa mahukunta su ɗauki matakan kare rayukan ɗaliban.

    Ɗalibai uku sun mutu a watan Yuli a wata sakandare ta Musulunci da ke birnin Dar es Salaam sakamakon gobara.

  13. Buhari da Obasanjo: Ana cacar baki kan kalaman shugabannin biyu

    Ana ci gaba da ce-ce ku-ce kan kalaman tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo game da mulkin Shugaba Buhari da kuma martanin da fadar shugaban ƙasar ta mayar.

    Martani na baya-bayannan shi ne wanda Kungiyar Dattawan Arewa ta Northern Elders Forum (NEF) ta yi na kare kanta game da zargin fadar shugaban ƙasar cewa kungiyoyin da suka halarci taron da tsohon Obasanjo ya yi na mutane ne masu kalaman ƙabilanci da nuna ɓangaranci.

    Mai magana da yawun ƙungiyar ta NEF wadda ke ɗaya daga kungiyoyin da suka halarci ganawar da Obasanjo, Dr Hakeem Baba-Ahmed ya ce a ganinsa taron na ciyar da ƙasa gaba ne kuma abin a yaba.

    A yayin taron dai tshohon shugaban na Najeriya Obasanjo ya bayyana cewa Najeriya na taɓarɓarewa a ƙarƙashin mulkin Buhari, yayin da kalaman ƙiyayya ke ƙara zama ruwan dare.

    Ya ce tattaunawa ta haƙiƙa da 'yan Najeriya ce kaɗai za ta magance matsalar ta kalaman ƙiyayya da kuma matsalolin da kasar ke fuskanta.

    A martaninsa, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewa tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo na ƙoƙarin raba kan 'yan Najeriya ne sakamakon irin kalaman da yake yi a 'yan kwanakin nan.

    A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban, Malam Garba Shehu ya fitar a ranar Lahadi, ya bayyana cewa Shugaba Buhari a kullum yana ƙoƙarin haɗa kan 'yan Najeriya ne da kuma gina ƙasar.

    Shugaba Buhari ya ce Obasanjo ya zama "babban mai raba kan ƙasa," kamar yadda sanarwar Garba Shehu ta bayyana.

    Ko a ƙarshen makon jiya sai da Ministan Yaɗa labarai Lai Mohammed ya yi wasu kalamai da suke nuna tamkar martani ne ga Obasanjo, inda ya ce "ba don Buhari ba da yanzu Najeriya ta ruguje".

    Sai dai 'yan Najeriya da dama na ci gaba da matani kan kalaman na Lai Mohammed a kafofin sada zumunta musamman Twitter.

  14. Ɗalibai sun koma makarantu a Sudan ta Kudu

    Jami'o'i da sauran makarantu a Sudan ta Kudu za su ci gaba da karatu a yau Litinin bayan kusan wata shida da rufe su sakamakon annobar cutar korona.

    An yanke matakin sake buɗe makarantun ne yayin zaman majalisar zartarwa na ranar Juma'a, wanda Shugaba Salva Kiir ya jagoranta.

    Ministar Lafiya Elizabeth Acuei Yol ta faɗa wa abokan aikinta cewa an samu "gagarumar raguwa a yawan adadin masu kamuwa da cutar kuma hakan ne ya sa za a buɗe makarantun a ƙasar".

    Gwamnati ta rufe dukkanin makarantu a ƙasar a watan Maris bayan ƙaruwar mutanen da ke kamuwa da ctar ta korona.

    "Labari ne mai daɗin ji amma sai an yi kyakkyawan shiri na buɗe makarantun. Sai an yi feshin magani kafin ci gaba da karatu," in ji Thuou Loi, kakakin ma'aikatar lafiya a hirarsa da manema labarai a babban birnin ƙasar Juba ranar Lahadi.

  15. Coronavirus: Ana yi wa shugabar fannin lafiyar Queensland barazana

    Shugabar fannin lafiya ta birnin Queensland na Australia, Jeannette Young ta ce 'yan sanda sun fara ba ta tsaro bayan an aike mata da barazana game da rayuwarta.

    Young ta ce ta fi samun natsuwa tare da masu gadi.

    An yi ta samun ɓacin rai game da matakin da hukumomin Queensland suka ɗauka na rufe iyakokin yankin da maƙwabtansa a yunƙurinsu na daƙile yaɗuwar annobar korona.

    A makon da ya gabata, an faɗa wa wasu yara da ke son zuwa Brisbane don ganin mahaifinsu da ba shi da lafiya daga Sydney cewa sai sun biya dalar Australia 16,000 na kuɗin killace kansu kafin a ba su damar yin hakan.

  16. Yajin aikin ma'aikatan lafiya ba ya kan ƙa'ida – Gwamnatin Najeriya

    Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta bayyana yajin aikin da gamayyar ƙungiyar ma'aikatan lafiya ta Joint Health Sector Unions (JOHESU) ta fara a yau Litinin a matsayin "karya doka".

    Kazalika, gwamnatin ta ce "bai dace ba kuma ma ba abu ne da ya zama dole ba".

    Ministan Ƙwadago da Samar da Aikin Yi Chris Ngige ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da mataimakin kakakin Ma'aikatar Ƙwadago ta Najeriya ya fitar ranar Lahadi.

    Mista Ngige ya ce Gwamnatin Tarayya ta umarci ƙungiyoyin da ke ƙarƙashin JOHESU da kar su ci gaba da yajin aikin.

    Har wa yau, ya shawarci ƙungiyoyin da su sake tunani game da yajin aikin "wanda ba ya kan ƙa'ida ta hanyar fifita mahimmancin lafiyar mutane fiye da komai".

    JOHESU ta ɗauki matakin ne bayan kwamitin gudanarwarta na ƙasa ya yi wata ganawa ranar Asabar, inda ta ce ta fara yajin aikin daga 12:00 na daren Lahadi bayan ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa'adin kwana 15 domin a biya mata buƙatunta amma "babu abin da aka yi".

  17. Ma'aikatan lafiya sun fara yajin aiki a Najeriya

    Gamayyar ƙungiyar ma'aikatan lafiya a Najeriya ta Joint Health Workers Union (JOHESU) ta fara yajin aikin gargaɗi a ƙasa baki ɗaya tun daga a yau Litinini, 14 ga watan Satumban 2020.

    Ƙungiyar ta ɗauki matakin ne bayan kwamitin gudanarwarta na ƙasa ya yi wata ganawa ranar Asabar, kamar yadda wata sanarwa da shugaban ƙungiyar Biobelemoye Joy Josiah ya sanya wa hannu a jiya Asabar ta bayyana.

    Wannan yajin aikin na zuwa ne kwana uku bayan ƙungiyar likitoci ta National Association of Resident Doctors of Nigeria (NARD) ta janye nata yajin aikin da ta shafe kusan mako ɗaya tana yi.

    JOHESU ta ce ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa'adin kwana 15 domin a biya mata buƙatunta amma "babu abin da aka yi".

    Likitocin na neman Gwamnatin Tarayyar ta magance matsalar rashin kayan aiki a ɓangaren lafiya sannan ta biya bashin alawus-alawus da ma'aikatan yaƙi da annobar korona ke bin ta.

    Babu tabbacin irin girman tasirin da wannan yajin aiki zai yi ga yaƙin da Najeriya ke yi da annobar cutar korona, wadda ya zuwa yanzu mutum 56,177 suka kamu sannan 1,078 suka mutu.

  18. Gwamna Aminu Tambuwal ya cika alƙawari sakamakon hirarsa da BBC

    Gwamnan Jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya cika alƙawarin da ya ɗauka bayan hirarsa da Sashen Hausa na BBC ta cikin Shirin A Faɗa A Cika.

    Shirin wanda ke bin bahasin alƙawuran da 'yan siyasa suka yi wa magoya bayansu kafin zaɓe, ya karɓi baƙuncin Aminu Tambuwal ranar Litinin da ta gabata, inda aka tambaye shi dalilin da ya sa bai cika alƙawarin naɗa mai ba shi shawara kan nakasassu ba.

    Gwamnan ya amsa da cewa zai cika alƙawarin. "Nan da kwana nawa?" Yusuf Ibrahim Yakasai ya tambaye shi. "Nan da kwana biyu," in ji Tambuwal.

    A ƙarshe dai gwamnan ya naɗa Abdulazeez Ibrahim Abdullahi - wani mai buƙata ta musamman - a matsayin mai ba shi shawara kan harkokin masu buƙata ta musamman, abin da ba a saba gani ba.

    Abdulazeez ya shaida wa BBC cewa tuni 'yan uwansa masu buƙata ta musamman suka haɗa masa walima tare da bayyana masa buƙatunsu.

    "Na je na tambayi mabarata dalilin da ya sa suke yin bara kuma sun shaida mani cewa in suka samu sana'o'in hannu ba za su sake yin barar ba sannan kashi 20 cikinsu karatu suke so," in ji shi.

    "Yadda aka saba shi ne, sai dai a ɗauko wani wanda lafiyarsa ƙalau a ba shi [wakilcin nakasassu]."

  19. An zargi Trump da ƙin yarda da sauyin yanayi yayin da wutar daji ke cinye gidaje a Amurka

    Jagororin siyasa a yankin arewacin Amurka sun zargi Shugaba Donald Trump da ƙin gasgata cewa sauyin yanayi na da illa ga muhalli.

    Wannan na zuwa a daidai lokacin da jihohin ƙasar guda uku ke faɗi-tashin kashe wutar daji da ke ci ba ji ba gani.

    Gwamnan Washington Jay Inslee ya ce abin takaici ne duk da irin halin da ake ciki, shugaban ƙasa bai fahimci illar ba har yanzu.

    Takwararsa ta Oregon Kate Brown ta ce dole ne gwamnati ta kawo musu mafita kan bala'in sauyin yanayi.

    Misis Brown ta ce: "Ba ƙaramin bala'i ba ne. Ba mu taɓa ganin irin wannan gobara ba a tarihin Oregon."

    A yau ne a ke dakon Shugaba Trump zuwa California don haɗuwa da 'yan kwanakwana.

  20. Korona a Najeriya: Mutum 79 sun kamu, huɗu sun mutu ranar Lahadi

    Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa a Najeriya NCDC ta ce adadin mutanen da annobar korona ta harba a ƙasar sun kai 56,256 bayan da aka gano ƙarin mutum 79 da suka kamu da cutar ranar Lahadi.

    A cewar NCDC, an samu mutum 4 da cutar ta kashe a ranar Lahadi abin da ya kai adadin mamatan zuwa 1,082.

    Kazalika an samu karin mutum 62 da suka warke daga cutar a ranar ta Lahadi, abin da ya sa a jumullar yawan mutanen da suka warke kuma aka sallame su daga asibiti ya kai 44,152.

    A ranar Lahadin jihar Legas ne ke kan gaba a yawan wadanda suka kamu da cutar inda aka samu mutum 30.

    Sai Kaduna mai mutum 17, yayin da Ogun ke bin ta da mutum bakwai.

    Jihar Anambra na da mutum biyar, sai kuma Kano mai guda huɗu.

    Katsina da Abuja da Akwa Ibom na da an samu mutum 3-3 a kowace jiha da suka kamu a ranar Lahadi.

    Jihohin Oyo da Rivers na da 2-2, inda jihohin Delta da Filato da Ondo ke da 1-1 kowacensu.