Mutum 160 ne suka kamu da korona ranar Asabar a Najeriya

Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa a Najeriya NCDC ta ce adadin mutanen da annobar korona ta harba a ƙasar sun kai 56,177 bayan da aka gano ƙarin mutum 160 da suka kamu da cutar ranar Asabar.
A cewar NCDC, an samu mutum 2 da cutar ta kashe a ranar Asabar abin da ya kai adadin mamatan zuwa 1,078.
Kazalika an samu karin waɗanda suka warke daga cutar su a ranar ta Asabar abin da ya sa a jumullar yawan mutanen da suka warke kuma aka sallame su daga asibiti ya kai 44,088.
A ranar Asabar Abuja da Plateau ne ke kan gaba a yawan wadanda suka kamu da cutar inda aka samu mutum 39-39 a ko ina , sai Legas mai mutum 30.
Kaduna na da mutum 23, yayin da Katsina ke binta da mutum 7.
Jihohin Rivers da Oyo na da mutum 6-6 da suka kamu a kowacce jiha, sai kuma Yobe da Benue na da mutum 3-3.
Jihohin Bayelsa da Abia da Edo da kuma Ekiti su kuma an samu mutum dai-dai a kowacce jiha da suka kamu a ranar Asabar.
