Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Obasanjo ne babban mai raba kan 'yan Najeriya – Buhari

Wannan shafi na kawo muku bayanai kai-tsaye dangane da irin wainar da ake toyawa a fadin duniya musamman batutuwan da suka shafi Najeriya da Nijar da makwabtansu.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Mustapha Musa Kaita

  1. Mutum 160 ne suka kamu da korona ranar Asabar a Najeriya

    Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa a Najeriya NCDC ta ce adadin mutanen da annobar korona ta harba a ƙasar sun kai 56,177 bayan da aka gano ƙarin mutum 160 da suka kamu da cutar ranar Asabar.

    A cewar NCDC, an samu mutum 2 da cutar ta kashe a ranar Asabar abin da ya kai adadin mamatan zuwa 1,078.

    Kazalika an samu karin waɗanda suka warke daga cutar su a ranar ta Asabar abin da ya sa a jumullar yawan mutanen da suka warke kuma aka sallame su daga asibiti ya kai 44,088.

    A ranar Asabar Abuja da Plateau ne ke kan gaba a yawan wadanda suka kamu da cutar inda aka samu mutum 39-39 a ko ina , sai Legas mai mutum 30.

    Kaduna na da mutum 23, yayin da Katsina ke binta da mutum 7.

    Jihohin Rivers da Oyo na da mutum 6-6 da suka kamu a kowacce jiha, sai kuma Yobe da Benue na da mutum 3-3.

    Jihohin Bayelsa da Abia da Edo da kuma Ekiti su kuma an samu mutum dai-dai a kowacce jiha da suka kamu a ranar Asabar.

  2. Maraba da shigowa shafin labarai kai-tsaye

    Masu bibiyarmu barkanku da hantsin Lahadi, da fatan ana yin hutun ƙarshen mako lafiya.

    Umar Mikail ke muku maraba da shigowa shafin labarai kai-tsaye - na abubuwan da ke faruwa a sassan duniya musamman Najeriya da maƙwabtanta.