Rundiunar 'yan sandan Jihar Ribas da ke kudancin Najeriya ta ce ta kama wani gawaurtaccen mai garkuwa da mutane Honest Digbara, wanda aka fi sani da Boboski.
Rahotanni sun bayyana cewa an kama Boboski ne ɗan asalin yankin Nwidera na Ƙaramar Hukumar Gokana a garin Korokoro na Ƙaramar Hukumar Khana, inda yake ɓoye da gungun tawagarsa.
Sai dai kafar talabijin ta Channels TV ta ce wanda ake zargin ya mutu 'yan awanni bayan kama shi sakamakon raunukan da aka yi masa da gatari bayan harsashin bindiga ya kasa shiga jikinsa.
Kwamishinann 'yan sandan jihar Joseph Mukan ne ya bayyana hakan ranar Asabar a Fatakwal, babban birnin jihar, inda ya "Boboski ne ke da alhakin aikata mafi yawan laifuka a jihar".
Kwamishinan ya ce sun samu nasarar kama shi ne bayan wasu bayanan sirri da suka samu daga mazauna yankin.
A cewar Mukan, Boboski ne ya yi sanadiyyar kisan wani lauya mai suna Emelogu bayan sun karɓi kuɗin fansar garkuwa da shi.
Kazalika, 'yan sanda sun zargi Boboski da kisan wani shugaban ofishin 'yan sanda a jihar.