Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Obasanjo ne babban mai raba kan 'yan Najeriya – Buhari

Wannan shafi na kawo muku bayanai kai-tsaye dangane da irin wainar da ake toyawa a fadin duniya musamman batutuwan da suka shafi Najeriya da Nijar da makwabtansu.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Mustapha Musa Kaita

  1. Rufewa

      • Marubuci, Mustapha Musa Kaita
      • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multi-Media Broadcast Journalist

    Masu bibiyarmu a wannan shafin a nan muka zo ƙarshen kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye, sai kuma gobe Litinin idan Allah ya kai mu za mu ci gaba da kawo muku wasu labaran.

    Za ku iya ziyartar shafinmu na Facebook ko Twitter ko kuma Instagram domin bayyana ra'ayoyinku kan labaran da muka wallafa ko kuma tafka muhawara a kansu.

  2. Lafiya Zinariya: 'Yadda cutar PCOS ta sauya min rayuwa'

  3. 'Yan sanda sun kama masu zanga-zanga kusan 400 a Belarus

    Ƴan sanda a Belarus sun kama kusan mutum 400 daga cikin masu ci gaba da zanga-zangar ƙin jinin gwamnatin Shugaba Alexander Lukashenko.

    Ɗaruruwan mutane ne suka fito zanga-zangar a yau Lahadi kamar yadda suka saba, domin ci gaba da yin kira ga shugaba Lukashenko ya yi murabus bayan shafe shekaru 26 yana mulki a kasar.

    An samu rikici a wasu wuraren tsakanin masu zanga-zangar da jami’an ƴan sanda yayin da ƴan sandan ke ƙoƙarin kama masu zanga-zangar.

    Masu zanga-zangar sun yi kiran kawo ƙarshen cin zarafin mutane da ƴan sanda ke yi, da kuma neman a saki shugabannin adawar da ake tsare da su.

  4. A FADA A CIKA tare da Gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal

  5. An kama mutum 13 a Uganda bayan kisan da aka yi wa 'yan gudun hijira

    'Yan sanda a Uganda sun bayyana ce akalla mutum 13 ne aka kama bayan kisan da aka yi wa 'yan gudun hijira akalla shida 'yan asalin Sudan Ta Kudu.

    'Yan sandan sun bayyana cewa an kashe 'yan gudun hijiran ne a sansaninsu da ke a arewa maso yammacin ƙasar ta Uganda.

    An kai hari ne ga sansanin Rhino mai ɗaukar akalla 'yan gudun hijira dubu 100 bayan wasu 'yan Sudan Ta Kudun sun ci zarafin wani makiyayi.

    An tura sojoji yankin dai domin dawo da zaman lafiya. Uganda na kula da sama da 'yan gudun hijira miliyan 14.

    A wani lokacin ana samun rashin jituwa tsakanin 'yan gudun hijiran da kuma 'yan ƙasar wanda hakan a ƙarshe ke zama rikici.

  6. Shirin Taɓa Kiɗi Taɓa Karatu na wannan makon

  7. Saudiyya za ta buɗe iyakokinta ga 'yan ƙasar masu son shiga da fita

    Ƙasar Saudiyya ta bayyana cewa za ta cire duka takunkumin da ta saka wa 'yan ƙasar kan fita da shiga ƙasar daga ranar 1 ga watan Janairun 2021

    Za a bar mutanen da suka samu takardar shiga ƙasar su fara shiga daga ranar 15 ga watan Satumbar 2020.

    Sai an tabbatar da mutum ya yi gwajin korona sa'o'i 48 kafin a bar mutum ya shiga ƙasar.

    Saudiyya ta ɗauki matakin na buɗe iyakokinta na ƙasa da sama da na ruwa ne ga 'yan ƙasarta masu son shige da fice bayan ta samu gamsassun bayanai daga hukumomi dangane da ci gaban da ake samu a yaƙi da cutar korona a ƙasar.

  8. Obasanjo ne babban mai raba kan 'yan Najeriya – Buhari

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewa Tsohon Shugaban ƙasar Olusegun Obasanjo na ƙoƙarin raba kan 'yan Najeriya ne sakamakon irin kalaman da yake yi a 'yan kwanakin nan.

    A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban, Malam Garba Shehu ya fitar a ranar Lahadi, ya bayyana cewa Shugaba Buhari a kullum yana ƙoƙarin haɗa kan 'yan Najeriya ne da kuma gina ƙasar.

    Wannan sanarwar da Garba Shehu ya fitar, tamkar martani ce ga kalaman da Obasanjo ya yi a ƙarshen makon da ya gabata inda Obasanjon ya ce Najeriya na "lalacewa cikin sauri da kuma rabewa" ƙarƙashin mulkin Buhari.

    Sai dai a nasa ɓangaren, Shugaba Buhari ya ce Obasanjo ya zama babban mai raba kan ƙasa, kamar yadda sanarwar Garba Shehu ta bayyana.

    An daɗe ana caccaka da kuma mayar da martani tsakanin Shugaba Buhari da kuma Obasanjo.

    Obasanjon ya sha rubuta wa Buhari wasiƙa inda yake masa hannunka mai sanda, a wani lokacin kuma ya caccaki gwamnatin ta Buhari inda yake zarginta da gazawa.

  9. Minista a Isra'ila ya yi murabus kan adawa da dokar kulle

    Wani daga cikin ministocin Isra'ila ya yi murabus daga muƙaminsa sakamakon adawa da yake yi kan ƙoƙarin saka dokar kulle a faɗin ƙasar a karo na biyu.

    Mista Yaakov Litzman, wanda shi ne ministan gidaje a ƙasar, ya bayyana cewa dokar kullen da za a saka a ƙasar za ta hana Yahudawa yin bikin shagulgulansu da suka saba yi a wannan watan.

    Ana sa ran dokar kullen za ta fara ne a ranar Juma'a mai zuwa, wanda dokar za ta taɓa bikin sabuwar shekarar Yahudawa da kuma ranar Yom Kippur, wadda ita ce rana mafi girma a kalandar Yahudawa, kuma za ta kasance a ranar 27 ga watan Satumba.

    Mista Litzman ya kuma yi barazanar janye jam'iyyarsa daga gamayya mai mulki a ƙasar.

  10. Ƙarin mutum 10,000 sun kamu da korona a Faransa

    Faransa ta bayar da rahoton samun adadi mafi yawa na mutanen da suka kamu da cutar korona a rana guda, yayin da take faman yaƙi da yaɗuwar cutar.

    A ranar Asabar, mahukuntan ƙasar sun ce ƙarin mutum 10,561 ne suka kamu da cutar, inda aka samu ƙarin 1,000 a kan na ranar Juma'a.

    Adadin waɗanda ake kwantarwa a asibiti na ƙaruwa har ma da waɗanda ake kai wa sashen kulawar gaggawa.

    Wani rukunin likitoci ya buƙaci mutane su ƙaurace wa taruwa wuri guda domin gudun yaɗuwar cutar.

    Mutum fiye da 30,000 ne suka mutu sakamakon cutar a Faransa - adadi na bakwai mafi yawa kenan a duniya.

  11. Covid-19: An kama masu zanga-zanga 17 a Australia

    An kama sama da mutum 17 da ke zanga-zanga a birnin Melbourne na Australia, gabannin sassauta dokar kulle a birnin.

    Masu zanga-zangar sun fito ne domin nuna rashin jin daɗinsu kan dokokin kulle - waɗanda suka haɗa da haramta taruwar jama'a.

    Har yanzu akwai doka mai tsauri a birnin ta zaman gida kuma babu batun zuwa makaranta ga yara, sai dai a yanzu an yi sassauci kan cewa mutanen birnin za su iya fitowa na sa'o'i biyu domin su ɗan motsa jiki.

    Kusan mutum 800 da suka mutu a Australia sakamakon korona a ƙasar sun fito ne daga birnin Melbourne da kuma garuruwan da ke makwaftaka da birnin.

  12. Ɗaliban JSS3 da SSS2 ne za su fara komawa makarantu a Legas

    Gwamnatin Jihar Legas ta sanar da cewa ɗaliban aji uku na ƙaramar sakandare (JSS3) da na aji biyu a babbar sakandare (SS2) ne kaɗai za su koma makaranta ranar Litinin 21 ga watan Satumba, 2020.

    Kwamishinar Ilimi ta jihar Folashade Adefisayo ce ta bayyana hakan a yau Lahadi cikin wata sanarwa da kakakin ma'aikatar ya fitar yayin bayyana tsare-tsaren da gwamnatin ta tanada na sake buɗe makarantu.

    Ta ce Legas za ta bi sannu a hankali wurin buɗe makarantun gwamnati sannan ta taya ɗaliban ƙarshe na sakandare murnar kammala jarrabawar ƙarshe ta WASSCE da suka yi.

    "Ɗaliban makarantun gwamnati da ke JSS3 da SSS2 ne kaɗai za su koma azuzuwa daga ranar Litinin 21 ga watan Satumba, 2020," in ji ta.

    Kwamishinar ta ƙara da cewa azuzuwan da ba a buɗe ba tukunna za su ci gaba da karatunsu ta intanet da talabijin da rediyo "yayin da za a sanar da buɗe su nan gaba".

    Kazalika, an bai wa su ma makarantu masu zaman kansu damar buɗewa daga ranar 21 ga watan Satumba.

  13. Ma'aikatan lafiya sun sake tsunduma yajin aiki a Najeriya

    Gamayyar ƙungiyar ma'aikatan lafiya a Najeriya ta Joint Health Workers Union (JOHESU) ta nemi 'ya'yanta su fara yajin aiki a ƙasa baki ɗaya tun daga yau Lahadi, 13 ga watan Satumban 2020.

    Ƙungiyar ta ɗauki matakin ne bayan kwamitin gudanarwarta na ƙasa ya yi wata ganawa ranar Asabar, kamar yadda wata sanarwa da shugaban ƙungiyar Biobelemoye Joy Josiah ya sanya wa hannu a jiya Asabar ta bayyana.

    Wannan yajin aikin na zuwa ne kwana uku bayan wata ƙungiyar likitocin ta National Association of Resident Doctors of Nigeria (NARD) ta janye nata yajin aikin da ta shafe kusan mako ɗaya tana yi.

    JOHESU ta ce ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa'adin kwana 15 domin a biya mata buƙatunta amma "babu abin da aka yi".

    Likitocin na neman Gwamnatin Tarayyar ta magance matsalar rashin kayan aiki a ɓangaren lafiya sannan ta biya bashin alawus-alawus da ma'aikatan yaƙi da annobar korona ke bin ta.

    Babu tabbacin irin girman tasirin da wannan yajin aiki zai yi ga yaƙin da Najeriya ke yi da annobar cutar korona, wadda ya zuwa yanzu mutum 56,177 suka kamu sannan 1,078 suka mutu.

  14. Makaɗin da ya ƙirƙiro salon reggae Toots Hibbert ya mutu

    Shahararren makaɗin salon kiɗan reggae Frederick Nathaniel Toots Hibbert ya rasu yana da shekara 77.

    Tauraron makaɗin, shi ne ya ƙirƙiri salon kiɗan reggae da kuma tawagar Toots & the Maytals a shekarun 1960.

    Hibbert ya mutu "salin-alin" a Kingston na Jamaica kewaye da iyalansa, a cewar tawagar tasa ranar Juma'a.

    Duk da cewa ba a san abin da ya yi sanadiyyar mutuwarsa ba, tauraron ya kamu da cutar korona mako biyu da suka wuce kuma ya yi jinya a ɓangaren kulawar gaggawa a asibiti.

    Ana kallon Hibbert a matsayin wanda ya ƙirƙiro kiɗan reggae tare da raɗa masa suna - waƙarsa ta "Do the Reggay" a 1968, ita ce waƙar da ta fara yin amfani da sunan salon.

  15. Sojoji sun kashe mutum uku a arewacin Kamaru

    Rahotanni daga Kamaru na cewa sojojin ƙasar sun harbe mutum uku a Bamenda, babban birnin Lardin Arewa-Maso Yamma.

    Shafin kafar labarai na Mimi Mefo Info ya ruwaito ranar Juma'a cewa biyu daga cikin waɗanda aka kashe ɗin su ne Konfor Gilbert Ngalla da kuma Akum Shallot kuma sun rasu ne bayan sojojin sun buɗe wa motarsu wuta.

    Jami'an tsaro ba su ce komai ba game da lamarin amma sun bayyana a baya cewa suna kan wani aikin zaƙulo masu neman ɓallewa mai laƙabin Operation Bamenda Clean.

    An shafe kusan mako biyu a jere ana tashin hankali a yankin bayan kisan wani ɗan sanda da ake zargin 'yan tawayen da yi.

    Lamarin ya ƙara ƙamari sakamakon taƙaita zirga-zirgar ababen hawa da aka yi, abin da ya jawo wahalhalu ga mazauna yankin.

  16. Austria na fuskantar ɓarkewar annobar korona a karo na biyu

    Austria na fuskantar zagaye na biyu na ɓarkewar annobar korona, a cewar shugaban ƙasar a yau Lahadi, yayin da mutanen da ke harbuwa da cutar ke ƙaruwa kamar sauran ƙasashen ƙungiyar Tarayyar Turai.

    Daga Juma'a zuwa Asabar, ƙasar mai mutum kusan miliyan tara ta samu mutum 869 da suka kamu da cutar - fiye da rabinsu a Vienna babban birnin ƙasar.

    "Abin da muke gani yanzu shi ne karo na biyu na annobar," in ji Shugaba Sebastian Kurz cikin wata sanarwa, inda yake shawartar mutane da su bi dokokin daƙile yaɗuwar cutar.

    Ya kuma yi gargaɗin cewa nan gaba kaɗan za a fara samun mutum 1,000 da ke kamuwa a kullum.

  17. 'Gawurtaccen' ɗan fashi a Ribas ya mutu bayan 'yan sanda sun kama shi

    Rundiunar 'yan sandan Jihar Ribas da ke kudancin Najeriya ta ce ta kama wani gawaurtaccen mai garkuwa da mutane Honest Digbara, wanda aka fi sani da Boboski.

    Rahotanni sun bayyana cewa an kama Boboski ne ɗan asalin yankin Nwidera na Ƙaramar Hukumar Gokana a garin Korokoro na Ƙaramar Hukumar Khana, inda yake ɓoye da gungun tawagarsa.

    Sai dai kafar talabijin ta Channels TV ta ce wanda ake zargin ya mutu 'yan awanni bayan kama shi sakamakon raunukan da aka yi masa da gatari bayan harsashin bindiga ya kasa shiga jikinsa.

    Kwamishinann 'yan sandan jihar Joseph Mukan ne ya bayyana hakan ranar Asabar a Fatakwal, babban birnin jihar, inda ya "Boboski ne ke da alhakin aikata mafi yawan laifuka a jihar".

    Kwamishinan ya ce sun samu nasarar kama shi ne bayan wasu bayanan sirri da suka samu daga mazauna yankin.

    A cewar Mukan, Boboski ne ya yi sanadiyyar kisan wani lauya mai suna Emelogu bayan sun karɓi kuɗin fansar garkuwa da shi.

    Kazalika, 'yan sanda sun zargi Boboski da kisan wani shugaban ofishin 'yan sanda a jihar.

  18. Gwamna Zulum ya ziyarci 'yan gudun hijirar Najeriya a Nijar

    A ci gaba da yunƙurin mayar da 'yan gudun hijirar Najeriya gida daga Jamhuriyar Nijar, wakilan Najeriya sun kai wa 'yan gudun hijirar ziyara a jiya Asabar.

    Tawagar ƙarƙshin jagorancin Gwamnan Borno Babagana Umara Zulum, ta ƙunshi shugaban hukumar 'yan gudun hijira ta Najeriya Basheer Garba Mohammed da Alhaji Ali Grema, waɗanda suka fara zuwa garin Diffa.

    Tawagar ta gana da 'yan Najeriyar mafi yawansu mata da ƙananan yara sannan ta yi musu alƙawarin mayar da su gida Najeriya, a cewar wata sanarwa da ma'aikatar bayar da agaji ta Najeriya ta wallafa a Twitter.

    Sanarwar ta ƙara da cewa tawagar ta gana da Gwamnan Jihar Diffa Isa Lameen.

    Daga baya kuma ta nufi garin Damasak da ke kan iyakar Najeriya da Nijar, inda ta duba wasu ayyukan gina matsuganan 'yan gudun hijirar, inda ake gina tanti 1,000 da kuma gida 280.

  19. Trump zai kai ziyara wurin gobarar daji

    Yau Lahadi ake sa ran shugaba Trump zai kama hanyar zuwa yammacin Amurka, inda wutar daji ta lalata kusan kadada miliyan biyar gami da garuruwa masu yawa.

    Bayan ya halarci wani taron gangamin zabe a Nevada, zai isa California a ranar Litinin, wurin da lamarin ya fi ƙamari.

    A Oregon, kimanin mutum 40,000 ne suka tsere daga gidajensu, yayin da kusan 5,000 ke karkashin kulawar hukumomi.

    Babu alkalumman wadanda suka rasa rayukansu har kawo yanzu amma hukumomin jihar sun ce akalla mutum 25 ake san sun mutu.

  20. Ana fafata zaɓe a ƙasar Rasha

    Al'ummar Rasha na tururwa zuwa rumfunan zaɓe a yau Lahadi domin jefa kuri'a a zaɓen ƙananan hukumomi da ake kallo a matsayin muhimmin gwaji ga jam'iyyar haɗin kan ƙasar ta shugaba Vladmir Putin.

    Masharhanta na ganin cewa jam'iyyar na rasa karfinta sannu a hankali saboda durkushewar ɓangaren haraji da dokar biyan fansho mai cike da sarƙaƙiya da ƙaruwar cin hanci da rashawa.

    Babban mai hamayya da shugaba Putin Alexei Navalny wanda yanzu haka ke farfadowa a asibiti, ya jima yana goyon bayan wadanda ke kalubalantar jam'iyyar shugaban a zaɓukan gwamnoni.

    Sai dai duk da yana ci gaba da farfadowar, jam'iyyarsa na ƙoƙarin rage tasirin jam'iyya mai mulki a kasar.

    Yayin da ake zaɓen a lardunan kasar da dama, 'yan siyasa na kokarin bin salon yakin neman zaɓen Mista Navalny domin mara baya ga 'yan takarar da ke da farin jinin kayar da jam'iyyar shugaba Putin.