Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Agenda 2050: Buhari ya kafa kwamitin bunƙasa Najeriya nan da shekara 30

Wannan shafi yana kawo muku bayanai ka-tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Mustapha Musa Kaita

  1. Mutum 296 ne suka kamu da korona ranar Talata a Najeriya

    Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa a Najeriya NCDC ta ce adadin mutanen da annobar korona ta harba a ƙasar sun kai 55,456 bayan da aka gano ƙarin mutum 296 da suka kamu da cutar ranar Talata.

    A cewar NCDC, an samu mutum 6 da cutar ta kashe a tsakanin ranakun Litinin da Talata, abin da ya kai adadin mamatan zuwa 1,067.

    Kazalika an samu karin waɗanda suka warke daga cutar su 103 a ranar ta Talata, abin da ya sa a jumullar yawan mutanen da suka warke kuma aka sallame su daga asibiti ya kai 43,334.

    A ranar Talata jihar Plateau ce ke kan gaba a yawan wadanda suka kamu da cutar inda aka samu mutum 183, sai Lagos mai mutum 33.

    FCT na da mutun 25, yayin da Ogun ke binta da 16.

    Jihar Oyo na bin Ogun da mutun 7, sai Ekiti da 6.

    Jihohin Kwara da Ondo na da 5-5, yayin da Anambra da Imo da kuma Nassarawa ke da 3-3 kowannnensu.

    Jahohin Gombe na da 2-2-, sai kuma Akwa Ibom mai 1 tal.

  2. Assalamu Alaikum

    Barkanku da hantsin Laraba - ta bawa ranar samu.

    Ku biyo mu domin sanin yadda duniya ke ciki musamman a Najeriya da maƙwabta da ma sassan duniya.