Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Agenda 2050: Buhari ya kafa kwamitin bunƙasa Najeriya nan da shekara 30

Wannan shafi yana kawo muku bayanai ka-tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Mustapha Musa Kaita

  1. Rufewa

      • Marubuci, Mustapha Musa Kaita
      • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multi-Media Broadcast Journalist

    Masu bibiyarmu a wannan shafin a nan muka zo ƙarshen kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye, sai kuma gobe Alhamis idan Allah ya kai mu za mu ci gaba da kawo muku wasu labaran.

    Ga wasu daga cikin labaran da muka wallafa a wannan shafin a yau:

    • An kori shugaban cibiyar kiwon lafiya na Liberia daga aiki
    • An sallami 'yan sanda 28 daga aiki a Ghana
    • Bam ya kashe mutum uku a wani gidan abinci
    • Agenda 2050: Buhari ya kafa kwamitin bunƙasa Najeriya nan da shekara 30
    • 'Da gangan Trump ya nuna korona ba ta da muhimmanci'
    • EFCC ta damƙe matasa 7 kan zargin aikata zamba ta intanet

    Za ku iya duba ƙasa domin karanta waɗannan labaran da ma wasu muhimmai.

  2. 'Dole ne likitocin da ke yajin aiki a Najeriya su ƙara haƙuri da gwamnati'

    Ministan Lafiya na Najeriya Osagie Ehanire, a ranar Laraba ya bayyana cewa dole ne likitocin da ke yajin aiki su ƙara haƙuri da gwamnatin Najeriya kafin a biya musu buƙatunsu.

    Ministan ya bayyana haka ne a wani shiri na musamman a kafar talabijin ta Channels a ƙasar.

    A ranar Litinin ne dai kungiyar ta likitoci masu neman sanin makamar aiki a ƙasar suka soma yajin aiki, inda suka ce gwamnatin ƙasar ta gaza biya musu buƙatunsu.

    Cikin buƙatun har da alawus-alawus na hatsarin aiki a lokacin korona.

    Ko a watan Yunin bana sai dai likitocin suka je irin wannan yajin aikin.

    Mista Ehanire, ya ce wannan ba lokaci bane na zuwa yajin aiki, a cewarsa gwamnati na ƙoƙarin ganin an biya likitocin kuɗinsu.

  3. Martanin Garba Shehu kan ƙarin farashin fetur

  4. EFCC ta damƙe matasa 7 kan zargin aikata zamba ta intanet

    Hukumar da ke yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya EFCC, ta kama wasu mutum bakwai a Ibadan, da zargin aikata zamba da almundahana ta intanet.

    A wani saƙo da hukumar ta wallafa a shafinta na Twitter, ta ce ta damƙe su ne a maɓoyarsu a yau Laraba a Unguwar Alaka da ke Elebu a garin Ibadan da ke jihar Oyo.

    An samu kama su ne sakamakon bayanan sirri da aka samu kansu cewa suna rayuwa ta ƙasaita amma ba a san hanyar samun kuɗinsu ba.

    Cikin kayayyakin da aka ƙwace a wurinsu akwai motoci huɗu, da kwamfutoci ƙirar Laptop, da manyan wayoyi na alfarma, da kuma wani hatimi da ke ɗauke da sunan ofishin kula da kuɗi na jami'ar koyon aikin likitanci ta Queensland da ke Australia.

    Cikin mutum bakwai da aka kama, Ayoola Timilehin da Olusola Timilehin 'yan gida ɗaya ne, hakazalika Oladayo Fayemi da kuma Tolulope Fayemi su ma 'yan gida ɗaya ne.

  5. Labaran Yamma Na BBC Cikin Minti Ɗaya - 09/09/2020

  6. 'Da gangan Trump ya nuna korona ba ta da muhimmanci'

    Wani sabon littafi ya yi zargin cewa Shugaban Amurka, Donald Trump, yana sane cewa cutar korona ta fi murar da ƙasar ta taɓa fama da ita illa, amma ya so shiriritar da hakan da gangan.

    A littafi wanda Bob Woodward, dan jaridar da ya bankaɗo abin fallasar nan na Watergate, ya yi hira da Mista Trump sau 18 daga watan Disamba zuwa Yulin da ya wuce.

    Mista Trump ya shaida masa cewa cutar na da "matuƙar haɗari" tun kafin a samu mutum na farko da ta kashe a Amurka, inda daga baya kuma ya ce ya so ya nuna cewa ba ta da muhimmanci ne don kada mutane su shiga ruɗu.

    A baya dai shugaban ya kira littafin na Woodward a matsayin na bogi, ya kuma soki ɗan jaridar da cewa yana fakewa ne kawai bai da abin faɗa.

    Sai dai Fadar White House ta fitar da sanarwa inda ta musanta yaudarar da ake zargin shugaban ya yi wa 'yan ƙasar kan cutar.

  7. Agenda 2050: Buhari ya kafa kwamitin bunƙasa Najeriya nan da shekara 30

    Shugaban Najeriya Muhammadu ya kafa kwamitin bunƙasa ƙasar nan da shekara 30 mai suna Agenda 2050, ƙarƙashin jagorancin ɗan kasuwar nan Atedo Peterside da kuma ministar kuɗi da kasafi da tsare-tsare, Zainab Ahmed.

    Ana sa ran wannan muradin na Najeriya na 2050 zai cire 'yan ƙasar mutum miliyan 100 daga talauci sakamakon hasashen da Bankin Duniya ya yi na cewa nan da 2040 adadin 'yan Najeriya zai kai miliyan 400.

    Kwamitin zai gaji shirin Najeriya na Vision 2020 wanda gwamnatin marigayi Umar Yar'adua ta ƙaddamar a 2009, da kuma shirin ERGP na 2017 da aka kafa domin farfaɗo da tattalin arziƙin Najeriya.

    Kwamitin da gwamnatin ta kafa zai ƙunshi gwamnoni shida, ɗaya daga cikin kowane yanki na ƙasar, da kuma 'yan majalisa da sanatoci da ministoci da wakilan hukumomi da na manyan jam'iyyu, da 'yan kasuwa da 'yan jarida da dai sauransu.

  8. Bam ya kashe mutum uku a wani gidan abinci

    Akalla mutum uku suka mutu, bakwai kuma suka samu raunuka sakamakon harin da wani ɗan ƙunar baƙin wake ya kai a wani gidan abinci a Mogadishu babban birnin Somalia.

    Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewa ɗan ƙunar baƙin waken ya hari farar hula ne, inda ya shiga gidan abincin, ya kuma je a daidai inda suke ya tayar da bam ɗin.

    Waɗanda suka shaida lamarin sun bayyana cewa tuni jami'an tsaro sun killace wurin da lamarin ya faru.

    Har yanzu babu wata ƙungiya da ta ɗauki nauyin kai harin, sai dai ƙungiyar al-Shabab wadda ke da alaka da ƙungiyar al-Qaeda na yawan kai hare-hare a birnin na Mogadishu.

  9. An sallami 'yan sanda 28 daga aiki a Ghana

    Gwamnatin ƙasar Ghana ta sallami 'yan sanda 28 sakamakon samunsu da laifin rashin ɗa'a.

    Korar 'yan sandan na zuwa ne bayan 'yan ƙasar sun matsa ƙaimi da kai koke-koke tun daga Janairun bana zuwa Agusta.

    An tattara laifukan da 'yan sanda suka aikata da ke da alaƙa da rashin ɗa'a har 181, sai dai bayan bincike mai tsanani da aka gudanar, an samu 'yan sanda 28 da laifi.

    Amfani da makami ba yadda ya dace ba, shan barasa a lokacin aiki da kuma rashin zuwa aiki na daga cikin laifukan da suka aikata.

    An rage wa wasu 'yan sandan girma, amma duk da korar da gwamnatin ƙasar ta yi, ta waiwayi waɗanda suyka gudanar da abin kirki a aikinsu domin yaba musu.

    Babbar jami'ar hulɗa da jama'a ta rundunar 'yan sandan ƙasar Sheila Abayie Buckman, ta bayyana cewa rundunar ba za ta taɓa yarda da rashin ɗa'a ba.

    Ta kuma buƙaci jama'ar ƙasar da su rinƙa kai ƙarar duk wani ɗan sandan da suka ga ya saɓa doka yayin da yake gudanar da aikinsa.

  10. An kori shugaban cibiyar kiwon lafiya na Liberia daga aiki

    Shugaban Liberia, George Weah, ya kori shugaban cibiyar kiwon lafiya na ƙasar, Mosoka Fallah, wanda aka dakatar tun a baya sakamakon bincikensa da ake yi kan yadda ya jagoranci yaƙi da korona a ƙasar.

    Wani kwamiti ne a ƙasar ya bayar da shawarar korarsa. Dakta Fallah ya kasance shugaban cibiyar lafiya na ƙasar na watanni hudu ne kacal.

    Har yanzu dai Dakta Fallah bai ce komai ba kan korarsa da aka yi.

    An dakatar da shi daga muƙaminsa ne tun a watan Agusta sakamakon sakamakon wasu laifuka da ya aikata ciki har da wata ƙunbiya-ƙunbiya da ake zargin ya yi a wurin fitar da sakamakon masu ɗauke da cutar korona a ƙasar.

  11. Ana sukar shugaban Lebanon saboda karkatar da kayan agaji

    Ana sukar Shugaban Ƙasar Lebanon Michel Aoun bayan da aka raba ganyen shayin da aka aiko daga Sri Lanka ga dogarawansa maimaimakon waɗanda fashewar sinadarai ta shafa a birnin Beirut.

    Mutane na ta tambayar yadda aka yi da kayan agajin.

    Hakan ya biyo bayan martanin da ofishin shugaban kasar ya mayar ne kan cewa an raba wa iyalan dogarawan fadar shugaban ƙasa fiye da kilo 1,600 na ganyen shayin, lamarin da ya fusata ma’abota shafukan sada zumunta a kasar.

    Masu suka sun bayyana cewa wannan wani misali ne na yadda jami’an gwamnati ke cin hanci da rashawa, abin da kuma ke ƙara kassara kasar kenan.

  12. Ambaliyar ruwa ta rusa gadoji a Jihar Sokoto

    Rahotanni daga jihar Sokoto na cewa ambaliyar ruwa ta yi sanadiyyar yankewar wata muhimmiyar gada abin da ya yanke al’ummomi da yawa daga sauran sassan jihar.

    Ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da ake yi a kwanan nan ya yi sanadin karyewar gadar Margai wadda ta haɗa Ƙaramar Hukumar Kebbe da sauran sassan jihar a jiya Talata.

    Alhaji Auwali Marafa Fakku, shi ne Shugaban Karamar Hukumar ta Kebbe kuma ya shaida wa BBC cewa ba iya Kebbe lamarin ya shafa ba.

    "Ita ma gadar ta Kebbe an yanke gabanta da bayanta sannan wani ƙauye da ake kira Faku, shi ma gadarsa ta yanke babu shiga ba fita."

    Ya ƙara da cewa gadar ita kaɗai ce ke bai wa mazauna ƙauyuka maƙwabta damar kai kayayyaki na kasuwanci.

    Karyewar gadar dai ita ce ta’adi na baya-bayan nan da ambaliyar ta yi a jihar a bana baya ga haddasa asarar rayukan mutane da dabbobi da gidaje da kuma gonaki a yankunan ƙananan hukumomi biyar na jihar.

  13. Amsar da Buhari ya bai wa Trump game da zargin kashe Kiristoci a Najeriya

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana yadda ta kasance tsakaninsa da Shugaban Amurka Donald Trump yayin da suka gana a Fadar White House game da zargin kashe Kiristoci a Najeriya.

    Shugaban ya bayyana haka ranar Talata a Abuja lokacin da yake magana a wurin taron duba ayyukan ministoci na shekara ɗaya bayan fara wa'adin mulkinsa na biyu.

    Ya ce: "Ina ganin ni kaɗai ne shugaba daga Afirka da shugaban Amurka ya gayyata fadarsa. Kuma lokacin da nake ofishinsa, ni da shi kaɗai, ya kalli tsabar idanuna ya ce me ya sa kuke kashe Kiristoci?

    "Zan yi mamakin martanin da za ku mayar idan ku ne a wurin. Ina fatan abin da zuciyata ta riƙa raya mani a lokacin ba ta yaudare ni ba. Saboda haka na fahimce shi.

    "Matsalar da ke tsakanin Fulani makiyaya da kafaffun manoma - wadda ta girme ni ba ma shi ba [Donald Trump] don na san na girme shi - ta sha faruwa.

    "Matsalar sauyin yanayi ce da kuma ƙaruwar yawan al'umma da rashin fahimtar al'adun Fulani [ita ce matsalar].

    "Idan kana da saniya 50 kuma suna cin ciyawa ko wani abu to fa duk hanyar da za ta kai su wurin shan ruwa za su bi ta, ba ruwansu da ko gonar wacece.

    "Saboda haka na yi ƙoƙarin yi masa bayani cewa matsalar ba ta da alaƙa da ƙabilanci ko addini. Matsalar al'adu ce wadda shugabanni ke ƙara ta'azzarawa a ƙasar.

    "Na umarci ministan noma ya tattatara bayanai na shekarun 1960, waɗanda suka zayyana hanyoyin da ake bi na kiwo, ta yaya suka yi amfani da kuɗi kaɗan suka ƙirƙiri madatsun ruwa da na'urorin samar da wutar lantarki har ma da na tsafta."

  14. Minti Ɗaya da BBC na rana

  15. Amurka za ta janye sojoji 2,200 daga Iraƙi a watan Satumba

    Amurka za ta janye fiye da kashi ɗaya cikin uku na sojojinta daga Iraƙi a makonnin da ke tafe, a cewar babban kawamandanta na Gabas Ta Tsakiya.

    Janar Kenneth McKenzie ya faɗa wa manema labarai cewa za a rage sojoji daga 5,200 zuwa 3000 nan da ƙarshen watan satumba.

    Waɗanda za su rage za su ci gaba da bayar da shawara da taimakon hukumomin tsaron Iraƙi a wurin “zaƙulo sauran ɓurɓushin” ƙungiyar IS mai iƙirarin jihadi.

    A watan da ya wuce, Shugaban Amurka Donald Trump ya tabbatar da cewa ya shirya janye duka sojojinsa daga Iraƙi nan da nan.

  16. Matashi ya yi wa 'yar shekara 86 fyade a Indiya

    Ana samun dubban rahotannin fyaɗe a Indiya a kowacce shekara, amma akwai waɗanda suka fi damun al'umma.

    'Yan sanda a babban birnin ƙasar, Delhi, sun kama wani matashi mai shekara 30 da 'yan kai bisa zargin cin zarafi tare da yi wa wata tsohuwa mai shekara 86 fyaɗe.

    "Matar na tsaye ne a ƙofar gidanta tana jiran mai sayar da madara lokacin da maharin ya tunkaro ta," in ji Swati Maliwal, shugabar hukumar mata ta birnin Delhi a hirarta da BBC.

    "Ya faɗa mata cewa mai kawo mata madarar ba zai zo ba sannan ya nemi ta bi shi domin ya nuna mata inda za ta samu madarar.

    Dattijuwar ta bi shi, in ji Ms Maliwal, sannan ya kai ta wata gona, inda ya yi mata fyaɗe.

    "Ta yi ta kuka tana roƙon ya ƙyale ta. Ta faɗa masa cewa ita tamkar kakarsa ce. Amma ya yi watsi da maganganun nata kuma ya ci zarafinta a lokacin da ta yi ƙoƙarin kare kanta," in ji Ms Maliwal.

  17. Sojoji sun ƙaddamar da shirin 'dawo da zaman lafiya' a arewacin Kamaru

    Sojoji da jami'an tsaron Kamaru sun ƙaddamar da wani shiri na "dawo da zaman lafiya" a Bamenda, babban birnin lardin Arewa maso Yamma.

    Hafsoshin sojojin ƙasar ne suka bayyana hakan a wata sanarwa da suka fitar ranar Talata, a cewar rahoton shafin jaridar Cameroon-Info.

    Birgediya Janar Nka Valere shugaban gendarmerie ta biyar da Birgediya Janar Ekongwese Divine Nnoko da kwamishinan 'yan sanda Gousmo Emile sun ce an ƙaddamar da shirin ranar Talata mai laƙabin "Bamenda clean".

    "Ana sanar da mazauna birnin Bamenda da kewaye cewa manyan kwamandojin tsaro na DSF na sanar da cewa an ƙaddamar da shiri na musamman a Bamenda da kewaye mai suna 'Bamenda clean' ranar Talata 8 ga watan Satumba," a cewar sanarwar.

    Hafsoshin sojojin sun ce shirin ya biyo bayan ƙaruwar tashin hankali ne sakamakon ayyukan "'yan ta'adda da masu laifi".

    Lardin arewa mai nisa wanda ƙasar Ingila ta yi wa mulkin mallaka, ya daɗe a cikin rikicin neman ɓallewa daga Kamaru da ayyukan Boko Haram da sauran ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi.

  18. Gobara ta lalata sansanin ƴan gudun hijira mafi girma a Girka

    Gobara ta lalata sansanin ƴan gudun cirani mafi girma a Girka, wanda ke cike da mutane a Tsibirin Lesbos.

    Kusan ƴan kwana-kwana 25 da motar kashe gobara 10 sun yi ta ƙoƙarin kashe gobarar tare da ceto mutane.

    Wasu sun ji rauni ta hanyar fita hayyacinsu bayan shaƙar hayaƙi.

    Rahotanni sun ce ƴan gudun ciranin da ke zanga-zangar adawa da dokokin hana yaɗuwar cutar korona ne suka tayar da gobarar, amma ba a tabbatar da hakan ba.

    Ƴan sanda sun rufe hanyoyin da ke sada mutane da sansanin don hana ƴan ciranin shiga garuruwan da ke kusa da yankin.

    Akwai kusan mutum 13,000 da ke zama a wajen, inda suka nunka yawan waɗanda hukumomi za su iya kula da su sau huɗu.

    A cewar kafar, kusan kashi 70 cikin 100 na mutanen sansanin ƴan ciranin Afghanistan ne sai kuma ƴan wasu ƙasashen fiye da 70.

  19. Yawaitar ruwan sama ka iya jefa mutane cikin matsi a Sudan - MDD

    Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) ta yi gargadin cewa za a iya shiga cikin matsin rayuwa a Sudan, yayin da ake dakon ruwan sama mai ƙarfi da ambaliya a 'yan kwanaki masu zuwa.

    Tuni gwamnati ta kafa dokar ta-ɓaci, amma MDD ta ce lokaci na kurewa.

    Yanzu haka kusan mutun miliyan ɗaya ne ambaliya ta shafa a yankin bayan da aka shafe makonni ana tafka ruwan sama.

    Ana fargabar mamakon ruwan zai haifar da ambaliya a ɗaukacin yankin Sahel.

  20. An dakatar da gwajin rigakafin korona bayan mutanen sun kamu da rashin lafiya

    An dakatar da gwajin rigakafin cutar korona a Birtaniya bayan da mutanen da ake yin gwajin a kansu sun kamu da rashin lafiya.

    Wannan shi ne karo na biyu da aka dakatar da cigaba da gwajin rigakafin, wanda jami'ar Oxford da ke Birtaniya ke kokarin samarwa tare da haɗin gwiwar kamfanin samar da magunguna na AstraZeneca.

    Mai magana da yawun kamfanin AstraZeneca ya ce an garzaya da mutum ɗaya asibiti bayan kamuwa da rashin lafiya mai tsanani a dalilin gwajin rigakafin.

    Sama da mutum 10,000 ne a ƙasashen Birtaniya da Brazil da Amurka da kuma Afrika ta Kudu aka yi wa gwajin.

    Yanzu haka ana kan gwajin rigakafin cutar korona guda 30 a faɗin duniya amma wannan din ne aka fi gamsuwa da ingancinsa.