Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana yadda ta kasance tsakaninsa da Shugaban Amurka Donald Trump yayin da suka gana a Fadar White House game da zargin kashe Kiristoci a Najeriya.
Shugaban ya bayyana haka ranar Talata a Abuja lokacin da yake magana a wurin taron duba ayyukan ministoci na shekara ɗaya bayan fara wa'adin mulkinsa na biyu.
Ya ce: "Ina ganin ni kaɗai ne shugaba daga Afirka da shugaban Amurka ya gayyata fadarsa. Kuma lokacin da nake ofishinsa, ni da shi kaɗai, ya kalli tsabar idanuna ya ce me ya sa kuke kashe Kiristoci?
"Zan yi mamakin martanin da za ku mayar idan ku ne a wurin. Ina fatan abin da zuciyata ta riƙa raya mani a lokacin ba ta yaudare ni ba. Saboda haka na fahimce shi.
"Matsalar da ke tsakanin Fulani makiyaya da kafaffun manoma - wadda ta girme ni ba ma shi ba [Donald Trump] don na san na girme shi - ta sha faruwa.
"Matsalar sauyin yanayi ce da kuma ƙaruwar yawan al'umma da rashin fahimtar al'adun Fulani [ita ce matsalar].
"Idan kana da saniya 50 kuma suna cin ciyawa ko wani abu to fa duk hanyar da za ta kai su wurin shan ruwa za su bi ta, ba ruwansu da ko gonar wacece.
"Saboda haka na yi ƙoƙarin yi masa bayani cewa matsalar ba ta da alaƙa da ƙabilanci ko addini. Matsalar al'adu ce wadda shugabanni ke ƙara ta'azzarawa a ƙasar.
"Na umarci ministan noma ya tattatara bayanai na shekarun 1960, waɗanda suka zayyana hanyoyin da ake bi na kiwo, ta yaya suka yi amfani da kuɗi kaɗan suka ƙirƙiri madatsun ruwa da na'urorin samar da wutar lantarki har ma da na tsafta."