An yi 'ruwan wata uku cikin kwana ɗaya' a Senegal
Shugaban ƙasar Senegal Macky Sall ya ƙaddamar da shirin bayar da taimako bayan da mamakon ruwan saman da aka yi na tsawon sa'a bakwai ya jawo ambaliyar ruwa.
Ministan harkokin ruwa ya ce an yi ruwan saman da yawanci ana mai yawa irin haka ne cikin wata uku a cikin rana guda kacal.
Ambaliyar ta yi ɓarna sosai inda ta lalata abubuwa da dama a mafi yawan yankunan ƙasar.
Mutum ɗaya ya ɓata a Kaolack da ke yankin tsakiyar ƙasar.
An kashe gwamman mutane sannan dubbai kuma sun rabu da muhallansu a wannan makon sakamakon ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da ke jawo ambaliya a wasu ƙasashen da ke yankin Sahel.