Rahotanni daga jihar Rivers da ke kudancin Najeriya sun rawaito cewa ana zaman dar-dar bayan an kashe wasu Hausawa guda biyu.
Ana zargin ‘yan kungiyar IPOB da ke neman ɓallewa daga Najeriya da kai wa Hausawan mazauna unguwar Oyigbo hari a Ƙaramar Hukumar Oyigbo.
Ya zuwa yanzu 'yan sandan Rivers ba su bayyana adadin waɗanda aka kashe ba a harin duk da cewa sun tabbatar wa da BBC faruwarsa.
Sai dai ƙungiyar ta IPOB ta nesanta kanta daga faruwar wannan rikici.
Shugaban 'yan arewa mazauna Kudu maso Gabashin Najeriya Alhaji Musa Sa'idu wanda kuma ya shaida lamarin, ya faɗa wa BBC cewa wannan hari shi ne na biyar da ƙungiyar ta kai wa Hausawa a yankin.
"Sun harbi mutum biyar sannan suka sassari mutum huɗu, inda biyu suka mutu ranar Lahadi kuma shi ne [karo] na biyar," in ji shi.
Alhaji Musa ya yi kira ga mutane da kada su yi ramuwar gayya a kan al'ummar Igbo mazauna arewa.
Lauyan ƙungiyar ta IPOB ya ce wasu ne suka kai harin domin su ɓata musu suna.