Shugaban majalisar wakilan Najeriya zai je Ghana kan rikicin kasashen biyu

Asalin hoton, Twitter/@SpeakerGbaja
Shugaban majalisar wakilan Najeriya Femi Gbajabiamila zai je Ghana ranar Laraba domin tattaunawa da takwaransa na kasar kan rikicin jakadancin da ke tsakanin kasashen biyu.
Mr Gbajabiamila ya shaida wa kafofin watsa labaran Najeriya cewa babban abin da ziyararsa za ta mayar da hankali a kai shi ne batun da ya shafi lafiyar 'yan kasarsa da ke Ghana.
Ministocin watsa labaran kasashen biyu sun yi cacar baki a kan batun inda ministan watsa labaran Najeriya Lai Mohammed ya zargi Ghana dacin zarafin 'yan Najeriya da ke kasar da rufe shagunansu da kuma fitar da su daga kasar.
A nasa martanin, ministan labaran Ghana Kojo Nkrumah ya ce sun fitar da 'yan Najeriya daga kasarsu ne sabodaan same su da hannu wajen aikata laifuka.
Rikicin difilomasiyya ya ta'azzara tsakanin kasashen biyu a watan jiya bayan wani dan kasar Ghana ya rufe wani ginin ofishin jakadancin Najeriya da ke Ghana.


