Mataimakiyar shugaban Zambia ta kamu da korona
Mataimakiyar shugabar Zambiya Inonge Wina gwaji ya tabbatar da tana ɗauke da cutar korona.
Ƴarta ma da suke tare ta kamu da cutar kamar shugaba Edgar Lungu ya tabbatar.
Shugaba Lungu ya yi masu fatan samun sauki a wani saƙon da ya wallafa a Twitter.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Zuwa yanzu mutum 10,218 aka tabbatar da cutar korona ta shafa a Zambia.
Hukumar kwallon Zambia ta dakatar da wasannin lig din kasar a watan da ya gabata saboda yaɗuwar cutar korona.


