Gobara ta tashi a Gandun Namun Daji a Kenya
Wata gagarumar gobara ta lalata wasu bangarori na Gandun Namun Dajin Tsavo a Kenya cikin makonnin da suka gabata, al'amarin da ya sanya rayuwar dabbobin wajen cikin hadari da kuma lalata muhalli.
Wutar ta baya-bayan nan ta tashi ne a karshen makon nan kuma hukumar gandun daji ta Kenya KWS, ta ce wasu ne suka ta da wutar ba bisa ka'ida ba.
Hukumomi sun tura sojoji don taimakon 'yan kwana-kwana da ke kokarin kashe wutar. Sojojin na amfani da helikwafta don zuba wa wutar ruwa daga sama.
An kira daruruwan masu aikin sa kai daga yankunan da ke kusa da wajen don su taimaka wajen kashe gobarar.
A wata sanarwa hukumar KWS ta ce 'yan sanda na kokarin gano wadanda suka tayar da wutar.
An shafe makonni wutar na ci gaba da ruruwa a lokacin bazara.
KWS ta wallafa wani hoto a wani sakon tuwita da ke nuna masu aikin sa kai na kokarin kashe wutar:
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X





