'Za mu bayar da saniya 2 kan ko wace bindigar AK-47 ɗaya'

Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye dangane da irin wainar da ake toyawa a fadin duniya musamman batutuwan da suka shafi Najeriya da Nijar da makwabtansu.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Mustapha Musa Kaita

  1. Rufewa

      • Marubuci, Mustapha Musa Kaita
      • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multi-Media Broadcast Journalist

    Masu bibiyarmu a wannan shafin a daidai wannan lokaci muka kawo ƙarshen kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye, sai kuma gobe idan Allah ya kai mu zai mu ci gaba da kawo muku wasu labaran.

    Ga wasu daga cikin labaran da muka wallafa a wannan shafin a yau:

    • Goodluck Jonathan ya isa Mali don sasanta rikicin siyasa
    • Ma'aikatan lafiya 57 sun kamu da korona a Jihar Filato
    • Za a buga gasar Kofin Afirka ta 2023 a watannin Yuni/Yuli
    • An gudanar da addu'ar neman zaman lafiya a Katsina
    • Sojojin Kamaru na neman yaran da 'yan a-ware suka sace
    • Majalisa na son a daina ƙayyade shekarun neman aikin gwamnati a Najeriya
    • 'Yar autar Nelson Mandela ta kamu da korona kafin rasuwarta
    • Za a buɗe makarantu a birnin Leicester na Ingila
    • 'Yammacin Afrika ta zama cibiya ta garkuwa da mutane a teku'

    Ku duba ƙasa domin karanta waɗannan labaran da wasu muhimmai...

  2. Minti Ɗaya Da BBC Hausa - Na Yamma

  3. Mata sun samu 'yancin zama su kaɗai a Saudiyya

    Lulwa Shalhoub

    Asalin hoton, Lulwa Shalhoub

    Wata kotu a Saudiya ta yanke hukunci kan 'yancin mata na kasancewa za su iya zaman kansu su kaɗai ba tare da kowa ba.

    Wannan hukunci wani sabon babi ne a tarihin ƙasar Saudiyya

    Matan sun samu wannan 'yancin ne bayan wata tuhuma da aka yi wa wata mata da ake zargi da barin gida ba tare da yardar mahaifinta ba.

    Lauyan da ke kare matar ya ce hukuncin ya nuna cewa ba laifi bane mace ta zauna ita kaɗai.

    A bisa al'ada a kasar ta Saudiya, an bai wa iyaye maza da kuma mazajen aure iko sosai a kan mata.

    Sai dai wasu sauye-sauye da aka yi a dokokin ƙasar na baya-bayan nan sun bayar da dama ga matan ƙasar su yi walwala.

    A halin yanzu mata a ƙasar kan iya tuƙin mota har da zuwa kallon ƙwallo.

  4. 'Za mu bayar da saniya 2 kan kowace bindigar AK-47 ɗaya'

    ..

    Asalin hoton, @Bellomatawalle1

    Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta bayar da saniya biyu a matsayin diyya kan kowace bindiga ɗaya ƙirar AK-47 da ɓarayin da suka tuba za su kawo.

    Jaridar Daily Trust a Najeriya ta ruwaito cewa gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da ya karɓi baƙuncin Babban Sifeto na 'yan sandan Najeriya Mohammed Adamu da kuma Shugaban hukumar DSS Yusuf Bichi.

    A cewar gwamnan, ba za su biya ɓarayin diyya da kuɗi ba sai dai shanu sakamakon Fulani sun fi buƙatar Shanu domin ci gaban tattalin arziƙinsu.

  5. 'Yammacin Afrika ta zama cibiya ta garkuwa da mutane a teku'

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Gaɓar tekun Yammacin Afrika na ƙara zama cikin haɗari ga masu jigilar kayayyaki da jiragen ruwa sakamakon yawan fashi da ake yi.

    A wani rahoto da hukumar da ke sa ido kan ruwan teku ta duniya ta fitar, ta bayyana cewa kashi 90 cikin 100 na garkuwa da mutane da ake yi ana yin sa ne a gaɓar tekun Yammacin Afrika.

    A watanni uku da suka wuce kaɗai, an kama mutane 32 a mashigar ruwan Guinea.

    Daraktan hukumar Michael Howlett ya ce, harin da ɓarayin ke kai wa da bindigogi da wuƙaƙe ya zama ruwan dare ga masu jiragen ruwa.

  6. Shugabannin Majalisa sun ziyarci Shugaba Buhari

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya karɓi baƙuncin Shugaban Majalisar Dattawa na ƙasar Ahmed Lawan da kuma Kakakin Majalisar Wakilai Femi Gbajabiamila a Fadar Shugaban da ke Abuja.

    Bayo Omoboriowo

    Asalin hoton, Bayo Omoboriowo

    Bayo Omoboriowo

    Asalin hoton, Bayo Omoboriowo

  7. Masu garkuwa sun saki sama da mutum 60 a Kamaru

    Wasu da ake zargin 'yan aware ne da ke yankin rainon Ingilishi a Kamaru sun saki sama da mutum 60 da ake zargin sun yi garkuwa da su.

    Babu wani cikakken bayani kan ko an biya kudin fansa kafin sakinsu.

    Mutanen sun shafe kwanaki a hannun masu garkuwar.

    A baya dai mun ruwaito cewa wani kwamandan 'yan awaren da ake kira Janar Ayeke ya ɗauki nauyin garkuwa da mutanen.

    Sama da mutum 60 ne aka yi garkuwa da su a ƙauyen Mmouck Leteh a ranar Lahadi, wanda hakan ya jawo sojojin Kamaru suka bazama neman mutanen.

    'Yan awaren dai sun ƙaddamar da tawaye a yankuna biyu na rainon Ingilishi a Kamaru a 2016.

    Tun bayan nan, kusan mutum 3,000 aka kashe a ƙasar.

    A farkon watan nan ne dai wasu daga cikin shugabannin 'yan awaren da aka kama suka tattauna da gwamnatin ƙasar a yunƙurin fara yarjejeniyar zaman lafiya.

  8. Yadda Gwamna Wike ya ƙwaci tsohuwar shugabar NDDC daga hannun ƴan sanda

    JOY YIMEBE NUNIEH

    Asalin hoton, FACEBOOK/JOY YIMEBE NUNIEH

    Bayanan hoto, Joy Yimebe Nunieh

    Gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike ya 'ceto' Joy Nunieh - tsohuwar shugabar hukumar Raya Yankin Neja Delta daga hannun wasu ƴan sanda da suka isa gidanta domin kama ta.

    Joy Nunieh ta sanar da Arise TV, wata tashar talabijin da ke birnin cewa da misalin karfe 4 na asubar Alhamis 16 ga watan Yuli, wasu jami'an tsaro sun zagaye gidanta kuma sun yi ƙoƙarin kutsawa gidan nata.

    Ta kuma ce ta hana su shiga gidan nata ne saboda sun kasa nuna ma ta takardar sammaci.

    Daga baya ta ce ta kira gwamnan jihar Nyesom Wike wanda ya tafi gidan nata kuma ya fitar da ita bayan sun yi sa-in-sa da jami'an tsaron da suka zagaye gidan tsohuwar shugabar ta NDDC.

    A wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar bayan afkuwar dambarwar, gwamna Wike ya nemi masu hannu kan binciken da su tabbatar da babu abin da ya faru ga matar.

    Amma rundunar ƴan sandan Najeriya ba ta ce uffan ba duk da buƙatar da BBC ta yi na sanin abin da ya afku.

  9. Za a buɗe makarantu a birnin Leicester na Ingila

    ..

    Asalin hoton, AFP

    Sakataren Lafiya na Birtaniya Matt Hancock ya bayyana cewa za a iya buɗe makarantu a birnin Leicester da ke Ingila daga 24 ga watan Yuli.

    Ya ce jihar za ta ɗauki wani mataki na rufe shagunan da ba su sayar da muhimman kayayyakin amfani na yau da kullum.

    Ya kuma bayyana cewa gidajen giya da kuma na sayar da abinci da aka buɗe a sauran sassan Ingila - za a rufe su.

  10. 'Yan bindiga sun kashe 'yan agaji a Sudan

    'Yan bindiga a Sudan sun kashe wasu mutum shida - biyu daga cikinsu ma'aikatan bayar da agaji ne.

    An kashe mutanen ne yayin wani harin da 'yan bindigar suka kai a jihar Jonglei.

    An kashe 'yan agajin ne ne yayin da suke bayar da taimako irin na kiwon lafiya a garin Pajut na jihar ta Jonglei.

    Ɗaruruwan mutane ne aka kashe a hare-hare da suka haɗa da na ramuwar gayya a jihar Jonglei a wannan shekara, rikicin kan shafi satar shanu a yankin.

  11. Sojojin Kamaru na neman yaran da 'yan a-ware suka sace

    'Yan a-waren sun kwashe shekara da shekaru suna fafutukar ballewa daga kasar

    Asalin hoton, Getty Images

    Dakarun sojin Kamaru sun kaddamar da gagarumin bincike domin gano yaran nan da ake zargin masu fafutukar a-waren yankin rainon Ingilishi da ke Kudu maso Yammacin kasar sun sace.

    Wani babban jami'i a yankin ya ce wasu mutane dauke da makamai sun farmaki kauyen Mmouck Leteh da ke gundumar Lebialem inda suka sace yara maza 60, galibinsu masu tsakanin shekara 12 zuwa 16.

    Ya shaida wa BBC cewa 12 daga cikin yaran sun tsere inda suka koma kauyen da aka sace su.

    Jami'in ya ce kwamandan 'yan a-waren, wanda ake kira Janar Ayeke, ya yi ikirarin daukar nauyin sace yaran, kuma ya bukaci a ba shi $2,500 a matsayin kudin fansa.

    Gundumar ta Lebialem ta kasance wata cibiya ta 'yan a-ware.

    Jami'an yankin sun ce 'yan a-waren da dama sun tsere lokacin da sojoji suka kai samame a Arewa Maso Yammacin kasar, inda suka samu mafaka a Lebialem yankin da ke wa sojoji matukar wahalar zuwa.

    'Yan a-waren sun kwashe shekara da shekaru suna fafutukar ballewa daga kasar.

    Yakin ya yi sanadin mutuwar akalla mutum 3,000 sannan ya raba miliyoyin mutane da gidajensu, a cewar Majalisar Dinkin Duniya.

  12. Minti Daya da BBC Hausa na Rana

    Bayanan sautiMinti Daya BBC na Rana 16.07.2020
  13. An gudanar da addu'ar neman zaman lafiya a Katsina

    Mazauna Ƙaramar Hukumar Charanchi da ke Jihar Katsina sun gudanar da addu'ar neman zaman lafiya daga tashe-tashen hankula suke fuskanta a baya-bayan nan.

    Katsina na fuskantar hare-haren 'yan fashi da ke kashe mutane babu gaira babu dalili.

    Batsari

    Wani bidiyo da shafin Mobile Media Crew ya ɗauka kai-tsaye a Facebook ya nuna yadda mutane suka taru a masallaci domin yin addu'ar.

  14. Za a buga gasar Kofin Afirka ta 2023 a watannin Yuni/Yuli

    Africa Cup of Nations

    Asalin hoton, Getty Images

    Za a buga gasar cin Kofin Ƙasashen Afirka ta 2023 a tsakanin watan Yuni zuwa Yuli, a cewar muƙaddashin Sakatare na Hukumar Ƙwallon Ƙafar Afirka (Caf), Abdel Bah.

    An yi ta hasashe game da lokacin da za a yi gasar tun bayan da Shugaban Caf ya faɗa a watan Yuni cewa za a yi ta a 2023 "amma bai san wane watan ba".

    "Ya zuwa yanzu, an tsara gudanar da gasar Kofin Ƙasashen Afirka a watan Yuni zuwa Yuli saboda haka muka saka a kundin dokokinmu," Bah ya bayyana a wata hira da BBC Sport Africa.

    A shekarar 2017 ne Caf ta mayar da gasar zuwa waɗannan watannin, inda ta sanya su cikin kundin dokokinta.

    Za a buga gasar mai zuwa ta 2022 a Kamaru duk da cewa babu yanayi mai kyau a watannin Yuni da Yuli a ƙasar, inda ake samun tsananin zafi.

  15. Majalisa na son a daina ƙayyade shekarun neman aikin gwamnati a Najeriya

    Sanata Ahmad Lawan

    Asalin hoton, Nigerian Senate

    A ranar Laraba, Majalisar Dattawa ta nemi Shugaba Muhammadu Buhari da ya umarci Ma'aikatar Ƙwadago da ta kafa wani kwamiti da zai duba daina amfani da ƙayyade shekarun neman aiki a ƙasar.

    Majalisar ta cimma wannan matsaya ne biyo bayan ƙudirin da Sanata Ibrahim Gobir ya gabatar, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

    Sanatan ya ce "'yan Najeriya da dama na rage shekarunsu na haihuwa a ƙoƙarinsu na shiga cikin rukunin waɗanda za a ɗauka aikin".

    Ya ƙara da cewa: "Duk sanda mutum ya san cewa ba za a ɗauke shi aiki ba to zai bi wasu hanyoyi da ba su dace ba, abin da ke jawo ƙaruwar aikata laifuka da kuma rashin tsaro a ƙasar."

    Da yake magana yayin yin kiran, Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan ya yi Allah-wadai kan yadda ake nuna wa wasu masu neman aiki wariya saboda shekarunsu.

    "Babu laifin da suka aikata da zai sa a nuna musu wariya. Sai ka ji an ce 'yan shekara 30 kawai ake neman; sai ka tarar wani shi kuma ya gama jami'a shekara 10 da suka wuce," in ji shi.

  16. Mayaƙan IS da aka kora daga Syria 'suna tunkarar Afirka da Asia'

    ISIS

    Asalin hoton, AFP

    Wani binciken ƙwararru daga Burtaniya ya yi gargaɗin cewa mayaƙan ƙungiyar IS na sake gamuwa a sauran sassan duniya, bayan an yi galaba kan 'yan ta-da-ƙayar-bayan a yankin Gabas ta Tsakiya.

    Rahoton na Jami'ar Kings College London da haɗin gwiwar Cibiyar Nazarin harkokin aikin soja a Duniya ya ce akwai shaidar da ke nuna cewa tsoffin masu iƙirarin jihadi mai yiwuwa suna tunkarar wuraren da ke fama da rikice-rikice.

    A cewar nazarin dai, 'yan ta-da-ƙayar-bayan na nufar yankin Kudu maso gabashin Asiya da kuma Afirka, lamarin da ya sabunta barazanar tsaro ga ƙasashen duniya.

  17. 'Yar autar Nelson Mandela ta kamu da korona kafin rasuwarta

    'Yar autar Nelson Mandela ta kamu da korona kafin ta rasu

    Asalin hoton, DEBBIE YAZBEK/AFP

    Zindzi Mandela, 'yar autar tsohon shugaban Afirka ta Kudu Nelson Mandela, ta kamu da cutar korona a ranar da za ta rasu.

    Ta mutu ne a Johannesburg babban birnin ƙasar a farkon wannan makon tana da shekara 59.

    Ɗanta mai suna Zondwa Mandela ya faɗa wa kafar yaɗa labarai ta SABC cewa babu tabbas ko cutar ce ta yi ajalinta. Iyalanta suna jiran sakamakon gwajin da aka yi na sanadiyyar mutuwar tata.

    "Tun da dai har an tabbatar ta kamu da cutar wajibi ne mu bi dokokin da aka tanada game da waɗanda suka mutu a irin wannan yanayi," a cewarsa.

    An ruwaito shi yana bayyana cewa za a binne mahaifiyar tasa a ranar Juma'a.

  18. Ma'aikatan lafiya 57 sun kamu da korona a Jihar Filato

    Gwamna Lalong

    Asalin hoton, PSG

    Kwamishinan Ilimi a Jihar Filtato, Dr Nimkong Lar ya ce ma'aikatan lafiya 57 ne suka harbu da cutar korona a jihar yayin da suke bakin aikinsu.

    Kwamishinan ya bayyana haka ne a wurin taron manema labarai ranar Laraba a Jos babban birnin jihar, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na NAN.

    Lar ya ce waɗanda suka kamun suna kan gaba ne a yaƙi da annobar korona a cibiyoyin lafiya da asibitoci a jihar.

    A cewarsa, mutum 571 ne suka harbu da korona a Filato zuwa Talata, wanda shi ne adadi mafi yawa na waɗanda suka mutu tsakanin jihohin Najeriya.

    "Mun yi wa mutum 9,039 gwajin cutar, mun samu sakamakon 7,324 kuma muna jiran 1,715, yayin da aka tabbatar 571 sun kamu da cutar," in ji kwamishinan.

    "132 yanzu haka suna jinya a cibiyoyin lafiya huɗu, an sallami 260 sannan 16 sun mutu."

  19. Ta juya 5,000 zuwa 100,000 – Budurwar da ke fito da maza da ƙerarrun takalma a Kano

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama ku ga bayanin Khairat daga bakinta

    A kowanne yanayi ba a rasa mai nasara da wanda ya yi asara, amma dai a wannan yanayin Khairat Ibrahim nasara ta yi, inda ta juya naira 5,000 zuwa 100,000.

    Khairat Ibrahim budurwa ce da ta rungumi sana'ar hada takalman maza a kasuwar Kofar Wambai ta Kano bayan kammala digiri.

    Ta ce a yanzu harkarta tana bunkasa, kuma tana so ta nuna cewa ba wai maza ne kadai suke iya yin wannan sana'a ba, mata ma suna iya zarra matuƙar sun sa kansu.

    Babban fatan Khairat dai shi ne ta bude shagonta na ƙashin kanta, sannan ta bude makarantar koyar da haɗa takalma, musamman ga mata.

  20. Likitoci sun janye yajin aiki a Legas

    Lagos

    Asalin hoton, AFP

    Likitoci a Jihar Legas sun jingine yajin aiki na gargaɗi da suka fara kwana uku da suka gabata a yau Alhamis.

    Likitocin sun shiga yajin aikin ne saboda albashin da ba a biya su ba da kuma kayan kariya da jin daɗinsu yayin aiki da suka buƙaci a riƙa ba su.

    Shugaban ƙungiyar likitocin, Dr Oluwajimi Sodipo ya shaida wa BBC cewa yajin aikin nasu ya yi amfani domin kuwa sun yi nasara wurin jawo hankalin mahukunta game da abubuwan da ke damunsu sannan kuma gwamnati na shirin tattaunawa da su.

    Ya nanata cewa likitocin da ke kan gaba a yaƙi da cutar korona na cikin haɗari, wanda suke buƙatar lallai gwamnati ta kare su ta hanyar samar musu kayan kariya da suke kira Personal Protective Equipment da inshorar lafiya.