Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Korona: China ta yi watsi da buƙatar wasu lauyoyi ta biyan Najeriya diyyar biliyan $200

Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye dangane da irin wainar da ake toyawa a fadin duniya musamman batutuwan da suka shafi Najeriya da Nijar da makwabtansu.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya and Halima Umar Saleh

  1. An hango gwaggwan birrai dauke da jarirai a Najeriya

    A karon farko cikin shekaru da dama an hango rukunin wasu gwaggwan birrai, wasu ma goye da jariransu, a kan wasu tsaunuka da ke kudancin Najeriya.

    Masu kare gandun daji sun bayyana fatansu cewa gwagwan birran da aka dauko hotunansu a jihar Cross River za su ci gaba da hayayyafa duk da fargabar da ake yi cewa sun kusa karewa.

    Kungiyar da ke kare gandun dazuka ta Wild Conservation Society in Nigeria, ta ce an dauki hotunan gwaggwa birran ne da wata na'urar daukar hoto da aka ajiye a matsayin tarko a farkon shekarar nan.

    An ce gwaggwa na Cross River na cikin nau'in gwaggwan birran da ke da yiwuwar karewar daga doron kasa, domin kuwa gaba dayansu ba su wuce 300.

    Suna rayuwa ne a yankuna da ke cike da tsaunuka a kasashen Najeriya da Kamaru, ko da yake ba kasafai ake ganinsu ba.

  2. COVID-19: alƙalin alƙalan Ghana ya killace kansa

    Alƙalin alƙalan Ghana, Mai shari'a Kwasi Anin Yeboah, ya killace kansa bayan rahotanni sun nuna cewa wasu alƙalai sun kamu da cutar korona.

    Alƙalin alƙalan zai killace kansa tsawon kwana 14 daga ranar Laraba, a cewar sanarwar da sakataen shari'a ya fitar.

    Zai ci gaba da aiki daga gidansa da ke babban birnin kasar Accra.

    Shi ma shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo ya soma aiki daga gida a karshen mako bayan ya yi mu'amala da wani mutum da ya kamu da cutar korona.

  3. Barkanmu da warhaka

    Nasidi Adamu Yahaya ne yake yi muku barka da warhaka.

    Da fatan za ku kasance da mu domin sanin halin da ake ake ciki dangane da cutar korona, wacce ta addabi kasashen duniya.

    Baya ga batun wannan cuta, za kuma mu kawo muku sauran labarai da rahotannin da suka shafi rayuwarku, musamman daga kasashen Najeriya da Nijar da ma wasu sassan duniya.

    Kuna iya tafka muhawara da bayyana ra’ayoyinku a shafukanmu na sada zumunta a BBC Hausa.