Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Ba a ga komai ba a bala'in annobar coronavirus - WHO

Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye dangane da irin wainar da ake toyawa a fadin duniya musamman batutuwan da suka shafi Najeriya da Nijar da makwabtansu.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya, Nabeela Mukhtar Uba, Buhari Muhammad Fagge and Halima Umar Saleh

  1. Coronavirus: Sri Lanka ta janye dokar hana fita sakamakon raguwar masu ɗauke da cutar

    Sri Lanka ta janye dokar hana fita ta sa'oi 24 da ta sanya cikin watan Maris inda a watan Aprilu ta sassauta dokar zuwa dare.

    A ranar Lahadi, da aka cire dokar, jami'ai suka sanar cewa sun yi nasara wajen dakile bazuwar cutar korona a kasar.

    A cikin watan Mayu ne aka samu ƙaruwar masu ɗauke da cutar inda mutum 150 suka harbu.

    Tun daga nan ne kuma aka riƙa samun raguwa - a ranar Asabar, mutum 19 aka tabbatar sun kamu da cutar. Sri Lanka ta sanar da mutum sama da 2,000 sun kamu da korona sai 11 da suka mutu.

    Amma hukumomi za su ci gaba da tsaurara matakai. Misali, mutanen da aka samu cikin taron jama'a ba tare da sanya takunkumin fuska ba, za su fuskanci killacewa ta kwana 14, kamar yadda kafafen yada labarai a kasar suka rawaito.

  2. Tsohon Shugaban mulkin soji a Nijar na neman takarar shugaban kasa

    Tsohon Shugaban kasar Nijar a karkashin mulkin soji, Janar Salou Djibo zai tsaya takarar shugaban kasa a zaben bana da za a yi a kasar.

    A ranar Lahadi ne aka sanar da Janar Djibo a matsayin wanda zai yi wa jam'iyyar PJP takara.

    Tsohon shugaban kasar ne ya jagoranci tawagar sojojin da suka hamɓarar da mulkin Mahamadou Tandja a watan Fabarairun 2010 bayan ya yi kokarin zarcewa kan kujerar mulki har fiye da ka'idar zango biyu.

    Janar Djibo ya mika mulki ga farar hula bayan da Mahamadou Issoufou ya lashe zaben da ya biyo baya.

    Janar Djibo dai ya yi ritaya daga rundunar sojin kasar a 2019.

    Yana fatan zama magajin Shugaba Issoufou wanda kundin tsarin mulkin kasar ya haramtawa mulkar kasar a karo na uku.

    Za kuma a gudanar da zaben shugaban Nijar ɗin ranar 27 ga watan Disambar 2020.

  3. Cutar korona ta kashe mutum fiye da 500, 000

    Sama da mutum 501,000 sun mutu bayan kamuwa da cutar korona, a cewar kididdigar da Jami'ar Johns Hopkins da ke Amurka ta fitar.

    Ga ƙasashe 10 da mace-mace suka fi yawa saboda korona.

    • Amurka:125,803
    • Brazil:57,622
    • Burtaniya:43,634
    • Italia:34,738
    • Faransa:29,781
    • Spaniya:28,343
    • Mexico:26,648
    • India:16,475
    • Iran:10,508
    • Belgium:9,732

    Amurka ce ke kan gaba a ƙasashen da cutar ta fi yi wa illa da mutuwar mutum 125,803.

    Brazil ce ta biyu da mutum 57,622 da suka mutu sai Burtaniya da Italiya da Spaniya.

    Sama da rabin mace-macen sun faru ne a kasashen biyar - wanda yake da nasaba da tsarin gwaje-gwajensu da yadda suke ba da rahoton cutar.

  4. Sojojin Najeriya tara sun mutu a harin masu da'awar Jihadi

    Wasu majiyoyin tsaro a arewa maso gabashin Najeriya sun ce sojoji tara da mambobi daga hukumar tsaro ta farin kaya sun mutu sakamakon harin da masu da'awar jihadi suka kai musu.

    Majiyoyin sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na Faransa cewa farar hula da dama sun yi ɓatan dabo, ko dai an halaka su ko kuma an yi garkuwa da su.

    Masu da'awar jihadin sun yi amfani da bindigogi da gurneti wajen yi wa jerin gwanon farar hular cikin sama da motoci 100 bisa rakiyar sojoji kwanton ɓauna kusa da Damboa a jihar Borno - kusa da wani daji inda 'yan Boko Haram ke da sansani.

    Rikicin na Boko Haram dai ya halaka mutum 36,000 cikin shekara 10 tare da fantsama zuwa makwabta kasashe.

  5. Shugaban Guinea-Bissau ya sallami wasu ministocinsa

    Shugaban kasar Guinea-Bissau Umaro Sissoco Embaló ya sallami ministoci biyar daga aiki.

    Ministocin su ne na Tsaro, da Harkokin Cikin Gida, da Aikin Gona, da Makamashi.

    An kore su ne ranar Lahadi ba tare da bayyana dalilin daukar matakin ba.

    Lamarin na faruwa ne gabanin muhawarar da za a yi a zauren majalisar dokokin kasar ranar Litinin, kan gamayyar jam'iyyun da ta fi cancanta ta mulki kasar.

    Kasar ta dade tana fama da rikcin siyasa. An ayyana Shugaba Embaló a matsayin mutumin da ya lashe zaben watan Disamba. Sai dai jam'iyyar da ta dade tana mulkin kasar PAIGC ta ce an tafka magudi a zaben.

    Wasu daga cikin ministocin da aka kora magoya bayan jam'iyyar Madem-15 ta shugaban kasar ce, yayin da wasunsu masu yi masa biyayya ne, a cewar kamfanin dillacin labaran Reuters.

    Sau tara ana yin juyin mulki ko kuma yunkurin yinsa a Guinea-Bissau tun shekarar 1980.

    Mr Embaló, wanda tsohon Janar na soji ne, ya ce yana so ya kawo karshen zaman dar-dar din da ake yi a kasar sannan ya sauya ta.

  6. COVID-19: Ghana ta kara wa likitoci tallafi

    Shugaban Ghana Nana Akufo-Addo ya sanar da bayar da karin tallafi na wata uku ga ma’aikatan lafiyar kasar.

    Likitocin za su ci gaba da more karin kashi 50 na albashinsu kuma ba za su biya haraji ba a watannin Yuli, Agusta da Satumba.

    Tun wata uku da suka gabata shugaban kasar ya sanar da wannan mataki bayan barkewar annobar korona a kasar.

    A jawabin da Shugaba Akufo-Addo ya ya yi ga ‘yan kasar ta gidajen talbijin ranar Lahadi da daddare, ya ce sun bayar da Karin tallafin ne saboda ma’aikatan lafiya su samu kwarin gwiwar ci gaba da yi wa kasar hidima a wannan hali da ake ciki.

    Ya zuwa yanzu, an tabbatar kusan mutum 17, 000 sun kamu da cutar korona a Ghana yayin da ta yi ajalin mutum 112. An yi wa mutum 294,867 gwajin cutar korona – daya daga cikin mafi girma a nahiyar Afirka.

  7. Buɗewa

    Barkanmu da safiyar Litinin. Da fatan kuna nan lafiya.

    Muna fatan za ku kasance tare da mu a wannan rana domin sanin halin da duniya take ciki.

    Za mu kawo muku labarai da rahotannin da suka shafi rayuwarku, musamman kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da makwabtansu, har ma da sassan duniya.

    Kuna iya tafka muhawara a ko da yaushe a shafukanmu na sada zumunta da muhawara a BBC Hausa.