Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Ba a ga komai ba a bala'in annobar coronavirus - WHO

Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye dangane da irin wainar da ake toyawa a fadin duniya musamman batutuwan da suka shafi Najeriya da Nijar da makwabtansu.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya, Nabeela Mukhtar Uba, Buhari Muhammad Fagge and Halima Umar Saleh

  1. Rufewa

    A nan muka kammala bayanai da muka kwashe wunin yau muna kawo muku game da halin da duniya take ciki.

    Ku tare mu gobe da safe domin samun sabbin labarai da rahotanni.

    Kafin na, za ku iya lekawa kasa don karanta abubuwan da muka wallafa a wannan shafi tun daga safiyar yau.

    Kuna iya ci gaba da tafka muhawa da bayyana ra'ayoyinku kan dukkan labarai da rahotannin da muke kawo muku a shafukanmu na sada zumunta.

    A madadin abokan aikina Nabila Mukhtar Uba da Nasidi Adamu Yahaya da kuma Buhari Muhammad Fagge, ni Halima Umar Saleh nake cewa mu kwana lafiya.

  2. Kotu a Paris ta yankewa tsohon firaminista Francois Fiyon hukuncin daurin shekara 5 a gidan yari

    Kotu a Paris ta yankewa tsohon firaminista Francois Fiyon hukuncin daurin shekaru biyar gidan yari, uku na gyara halinka, saboda kama shi da laifin biyan matar shi kudi daga aljihun gwamnati bisa karyar cewa ma'aikaciyar shi ce.

    Alkalin ya ce hakan cin amanar al'umma ne.

    Ita ma mai dakin nasa Penelope Fiyon an yanke mata shekaru uku na gyara halinka, kuma dukansu za su biya tarar dala dubu dari hudu.

    Masu shigar da kara na zargin Mr Fiyon da wawashe miliyoyin daloli daga asusun gwamnati.

  3. Ba ma goyon bayan abin da Isra'ila ke shirin yi - Michelle Bachelet

    Babbar jami'a a hukumar kare hakkin bil'adama ta Majalisar Dinkin Duniya ta gargadi Isra'ila da ka da ta ci gaba da shirin mamaye wani yanki daga gabar Yamma da Kogin Jordan.

    Michelle Bachelet ta ce ta damu matuka, don abin da Is'raila ke shirin yi ba ya bisa ka'ida, kuma zai iya haifar da rasa rayuka.

    Dama shirin na mamaye yankin na daga cikin abubuwan da Shugaba Trump ya sha alwashin taimakawa Isra'ilar ta yi, a wani bangare na rikicinta da Falasdin.

  4. An kara sanya dokar ta ɓaci a Brazil

    An kakaba dokar ta baci a babban birnin Brazil wato Brazilia, bayan da annobar korona ta daɗa ruruwa.

    Asibitocin gwamnati da masu zaman kansu sun cika makil.

    Babban daraktan Hukumar Lafiya ta Duniya Michael Ryan ya bukaci gwamnatin tarayya da na sauran jahohi da su yi aiki tare don samun nasara.

    A farkon watan nan ne mafi yawan jahohin suka sassauta dokar ba da tazara.

    Brazil ce ta biyu a duniya a yawan masu dauke da cutar korona bayan Amurka.

  5. Ba a ga komai ba a bala'in annobar coronavirus - WHO

    Shugaban Hukumar Lafiya Ta Duniya ya yi gargadi cewa annobar cutar korona ba za ta wuce nan kusa ba.

    Yanzu kusan wata shida kenan tun bayan da aka fara samun bular cutar korona a birnin Wuhan na China.

    A lokacin an yi fargabar cewa za mu ga maimaicin abin da ya faru na annobar cutar Sars a shekarar 2002 zuwa 2004, wacce ta kashe 774.

    A yanzu da mutum fiye da 500,000 suka mutu sannan miliyan 10 suka kamu da cutar, shugaban WHO Dr Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce ''wannan lokaci ne sake tunani.''

    Amma ya yi gargadi cewa "bala'i na nan tafe" - yana mai cewa "duba da irin yanayin da mukae ciki, muna fargabar cewa bala'in na nan tafe.''

    Duk da irin ci gaban da ake samu a kasashe, ya ce annobar na karuwa sosai kuma duniya na bukatar kara jajircewa da hakuri a watanni masu zuwa.

    "Wata shida da suka gabata, babu wanda ya yi tunanin duniya za ta zama haka,'' kamar yadda Dr Tedros ya shaida wa wani taron WHO.

  6. Iran ta bukaci a kama Donald Trump kan kisan Qassem Soleimani

    Iran ta bayar da sanarwar kama shugaban Amurka Donald Trump kan kisan babban kwamandanta Janaral Qassem Soleimani.

    Hukumomin Iran sun ce Mista Trump da wasu mutane sama da 30 za su fuskanci tuhumar kisan kai da kuma ta'addanci, sun kuma nemi agajin 'yan sandan kasa da kasa a shari'ar.

    An kashe Janaral Soleimani a wani harin sama da dakarun Amurka suka kai Baghdad babban birnin kasar a watan Janairu.

    Masu sharhi sun ce umarnin kamun kawai wata magana ce ta fatar baki wadda ba za ta yi tasiri ba, sai dai yana nuna wata tsantsar kiyayyar da shugabancin Iran ke yi wa Donald Trump.

  7. Labarai da dumi-dumi, Covid-19: Za a rufe kananan hukumomi 18 a Najeriya

    Kwamitin shugaban kasa kan yaki da cutar korona a Najeriya ya sanar da matakin rufe kananan hukumomi 18 cikin 774 da ke Najeriya.

    A cewar kwamitin, wadan nan kananan hukumomin su ne suke da kashi 60 cikin 100 na mutum 24,077 da suka harbu da cutar korona.

    Kwamitin ya bayyana haka ne ranar Litinin.

    Shugaban kwamitin kuma Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ya kuma ce za a bude makarantu ga daliban da ke shirin rubuta jarrabawa - 'yan aji shida a firamare da 'yan aji uku na karamar sakandare da kuma 'yan aji uku na babbar sakandare.

  8. Kimanin mutum 32 sun mutu a hadarin jirgin ruwa a Bangladesh

    Kimanin mutum 32 ne suka mutu, wasu da dama kuma sun yi batan dabo bayan da wani jirgin ruwa ya kife a Bangladesh kusa da Dhaka babban birnin kasar.

    Masu aikin ceto sun ce jirgin mai lakabin Morning Bird ya kife bayan ya yi taho mu gama da wani jirgin a kogin Buriganga, kusa da tashar ruwa mafi girma a kasar, Sadarghat.

    Kafafen yada labaran kasar sun ce jirgin ya taso ne daga wani kauye da ke tsakiyar kasar dauke da fasinjoji 50.

    Irin wannan hadari na jirgin ruwa na yawan faruwa a Bangladesh saboda cunkoso.

  9. An samu karuwar mace-mace a Iran saboda Covid-19

    Hukumomi a Iran sun ba da rahoton karin mutuwar sama da mutum 162 sakamakon cutar korona - adadi mai girma cikin kwana daya da aka taba samu tunb bayan barkewar cutar a Fabrairu.

    Tun watan Aprilu ne Iran take sassauta wasu daga cikin matakan kullen da ta dauka tare da bude wasu harkokin kasuwanci da wuraren ibada.

    Amma kuma a 'yan makonnin nan ana samun karuwar masu kamuwa da korona lamarin da ya haifar da fargaba.

    A yanzu da aka dage wasu takunkuman, mutane sun ci gaba da gudanar da harkokinsu - amma jami'ai suna ganin za a iya samun raguwar masu kamuwa da cutar idan aka fadada gwajin cutar.

    Sama da mutum 225,000 hukumomi suka rawaito sun kamu da cutar, 10,670 kuma sun mutu, abin da ya sa Iran ta zama daya daga cikin kasashen duniya da cutar ta korona ta fi yi wa illa.

  10. An zargi Faransa da sace wa Najeriya ɓutum-ɓutumi

    Wani fitaccen malamin tarihi wanda dan asalin Najeriya ne kuma malami a jami'ar Princeton University da ke Amurka, Farfesa Chika Okeke-Agulu ya nemi da a soke wani gwanjon butum-butumi da za a yi a birnin Paris yau Litinin.

    Malamin jami'ar ya ce ya yi kiran ne bisa dalilin cewa Faransar ta yi wa Najeriya sibaren na bayye ne da butum-butumin guda biyu a zamanin yakin basasa na Biafra.

    Sai dai kamfanin da zai yi gwanjon ya ce babu shaidar cewa butum-butumin wadanda aka sassaka su da itace sato su aka yi.

  11. An girke jami'an tsaro gabanin zanga-zangar neman adalci a Sudan, Catherine Byaruhanga BBC News, Kampala

    Jami'an tsaro sun yi tsinke a Khartoum, babban birnin Sudan gabanin wata zanga-zanga da aka shirya gudanarwa ranar Talata.

    An jibge jami'an tsaron a kusa da gadoji sannan an umarci shaguna da kasuwanni su rufe.

    Kungiyar kwararru a Sudan wadda ta jagoranci zanga-zangar data janyo aka sauke Omar al-Bashir a shekarar data gabata na kiran mutane su shiga gangamin domin neman adalci ga mutanen da aka kashe da kuma neman farar hula su zama masu fada a ji kan arzikin kasar.

  12. Al'ummar Mozambique na tserewa rikicin sojoji da Al-Shabab, Jose Tembe BBC News, Maputo

    Jama'a da dama na guduwa daga garin Mocimboa da Praia a arewacin Mozambique sakamakon arangama tsakanin sojoji da masu da'awar jihadi.

    Wasu na ficewa a jiragen ruwa yayin da wasu ke neman mafaka a daji.

    An yi amfani da jirage masu saukar ungulu da manya-manyan makamai lamarin da ya haddasa asara mai yawa ga bangarorin biyu.

    Dakarun gwamnati na kokarin fatattakar masu da'awar da aka fi sani da al-Shabab daga garin wanda suka kwace a karo na biyu kenan cikin shekarar nan.

    Kungiyar IS ce ta dauki nauyin kai hari na farko.

    Kimanin mutum 700 ne suka mutu, dubunnai kuma suka rasa matsugunansu sakamakon rikicin da aka fara a Lardin Cabo Delgado mai arzikin mai fiye da shekara biyu da suka gabata.

  13. Kotu ta umarci 'yan sandan Najeriya su biya 'yan shi'a N15m

    Wata babbar kotun tarayya a Abuja, ta umarci 'yan sandan Najeriya su biya 'yan kungiyar Shi'a mabiya Sheikh Ibrahim Elzakzaky Naira miliyan 15 saboda kisan 'ya'yan kungiyar uku yayin wata zanga-zanga a Abuja.

    Kotun wacce ta yi zamanta a Abuja babban birin kasar ta kuma umarci babban asibitin kasa ya bayar da gawarwakin uku nan take domin yi musu jana'iza.

    A ranar 22 ga watan Yulin 2019 ne aka kashe wasu mabiya kungiyar ta Shi'a yayin wata zanga-zanga da ta rikide zuwa tarzoma.

    A lokacin zanga-zangar su ma 'yan sanda sun yi zargin cewa 'yan Shi'a sun kashe dan sanda, zargin da kungiyar ta IMN ta musanta.

  14. Hotuna: Kwamitin shugaban ƙasa kan yaƙi da cutar korona ya gana da Buhari

  15. Coronavirus: Mozambique ta tsawaita dokar ta ɓaci, Jose Tembe BBC News, Maputo

    Shugaban Mozambique Filipe Nyusi ya tsawaita dokar ta ɓacin da aka sanya a kasar da wata ɗaya sai dai ya sassauta wasu matakai da ke shafar tatalin arziki.

    Za a sassauta tsauraran matakan da suka shafi yawon bude ido da wasanni da kasuwanci da ma'aikata, kamar yadda ya faɗa a jawabin da aka yaɗa ta talbijin.

    Za kuma a buɗe sararin samaniyar kasar ga ƙasashen da ke ɗasawa da Mozambique - amma kuma bai ambaci sunayen ƙasashen ba.

    Makarantun firamare da sakandare za su koma karatu amma ba lokaci ɗaya ba yayin da za a ci gaba da sa ido kan masu motocin haya.

    Shugaban kasar ya ce kwalejojin ilimi da jami'oi za su koma karatu nan da wata ɗaya amma dole su bi matakan kariyar da gwamnati za ta sanar.

    Wannan ne karo na uku da ake tsawaita dokar ta ɓaci ta tsawon wata ɗaya a kasar.

    Ya zuwa yanzu mutum 859 ne suka kamu da cutar korona a Mozambique, mutum biyar kuma sun mutu.

  16. Mutum bakwai sun mutu sanadiyyar gobara a asibitin Masar

    Wata gobara da ta tashi a birnin Alexandria a Masar ta halaka maras lafiya kimanin bakwai tare da jikkata karin ma'aikata bakwai.

    Kafofin yada labaran Masar sun ce tartsatsin wuta ne daga na'urar sanyaya daki da ke asibitin Badrawi ta haddasa tashin gobarar a wajen da ke kewaye da mutanen da ke fama da cutar korona.

    An kwashe sauran maras lafiyar da ke asibitin bayan da aka killace wajen da gobarar ta tashi.

    Tuni kuma aka kaddamar da bincike kan musabbabin tashin wutar.

  17. An samu tsohon Firaministan Faransa da hannu a badakalar aikin yi

    An samu tsohon Firaministan Faransa François Fillon da matarsa Penelope da laifi kan wata badaƙalar ayyukan yi na bogi.

    An zarge shi da biyan matarsa maƙudan kudade don wani aiki da ake zargi ba ta aiwatar da shi ba lokacin da aka ɗauke ta a matsayin mataimakiyarsa.

    Badakalar dai ta shafi kudirin Fillon na zama shugaban kasa, lamarin da zai bai wa Emmanuel Macron damar samun nasara.

    Zarge-zargen dai sun rage karsashin da yake da shi.

    Nan gaba ne ake sa ran za a yanke hukunci.

    "Kudin da aka fitar bai kai aikin da aka yi ba," a cewar alkalin. "An dora Mrs Fillon ka n mukamin da ba shi da amfani."

    An kuma same ta da laifin cin amana da boye dukiyar al'umma.

  18. COVID-19: Masana na son a yi wa wadanda suka warke gwajin kwakwalwa

    Wata tawagar masana ilmin kwakwalwa na Burtaniya na kira da a yi wa wadanda suka warke daga cutar korona gwajin kwakwalwa.

    Rahotanni sun ce masanan sun hakkake cewa kaso 30 na wadanda suka warke daga cutar korona bayan samun kulawar gaggawa ka iya fuskantar cutar razani.

    Haka kuma karin kaso 30 da aka killace aka raba su da iyalansu ka iya fuskantar yanayin damuwa ko kuma tsoro na wani dan lokaci.

    Masanan dai na son ganin masu korona na da damar samun tallafi domin duba yanayin tunaninsu.

  19. Minti Ɗaya Da BBC Hausa na Rana

  20. Ana neman ɗage zaɓe a Somalia, Abdi Dahir BBC Monitoring, Nairobi

    Shugabar hukumar zaɓe a Somalia ta bukaci a ɗage zaɓen majalisar dokoki da na shugaban kasa zuwa Agustan 2021.

    Shugabar hukumar Halima Ibrahim ta ce matsaloli kamar rashin kuɗaɗe da tsaro da ambaliyar ruwa da annobar korona ne suka haifar da tsaiko a ayyukan hukumar.

    An tsara gudanar da zaɓen 'yan majalisa cikin watan Nuwambar bana yayin da ake sa ran gudanar da zaɓen shugaban kasar cikin Fabarairun 2021.

    Sai dai manyan jam'iyyun hamayya na kasar sun yi fatali da shawarar jinkirta zaɓen.

    Ƙungiyar jam'iyyun siyasar ƙasar sun yi watsi da ƙarin wa'adin mulkin gwamnati mai ci.

    Wa'adin shugaban kasar zai kawo ƙarshe cikin Fabarairun 2021 yayin da na majalisar zai cika a watan Nuwamba.