Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Trump ya goyi bayan masu nuna wariyar launin fata

Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye dangane da irin wainar da ake toyawa a fadin duniya musamman batutuwan da suka shafi Najeriya da Nijar da makwabtansu.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya and Buhari Muhammad Fagge

  1. Refuwa

    A nan ne muka kawo karshen labarai da rahotonni da muke kawo muku kai tsaye a wannan shafi, sai kuma idon Allah ya kai mu gobe, ku kasance da mu domin kawo muku labarai da rahoton kama daga Najeriya Nijar da sauran makwabta na nahiyar Afrika, har ma da sauran sassan duniya baki baya.

    Ni Buhari Muhammad Fagge nake cewa mu kwana lafiya.

  2. Kotu ta hana belin dan jarida a Bangladesh

    Wata kotu a Bangladesh ta hana ba da belin dan jaridan nan da ya yi wani binciken kwakwaf a kasar.

    Ana binciken Shafiqul Islam Kajol bayan binciken da ya gudanar kan zargin safarar mata masu zaman kansu da ake yi a Bangladesh.

    Masu fafutuka na ci gaba da sukar gwamnati kan yunkurin danne masu fadar gaskiya..

    Dama Bangladesh na daga kasashen da ake muzgunawa yan jarida a duniya.

  3. Trump ya goyi bayan masu nuna wariyar launin fata

    Shugaban Amurka Donald Trump ya saka wani hoton bidiyo da ya haifar da matsala, bayan da ya nuna wani mai goyon bayansa na fadin farar fata na da karfi a duniya.

    Shugaban na ci gaba da fuskantar suka musamman daga kungiyoyin kare bakake da ke cewa ana nuna musu wariya.

    Sanata Tim Scott wanda dan jam'iyyarsa ne ta Republican na cikin wadanda suka yi Allah wadai da wannan lamari, kuma ya yi kira ga shugaban da ya sauke hoton bidiyon daga shafinsa na Twitter.

    To sai dai fadar White House ta musanta kalaman da ake cece kuce akansu a nata nazarin na hoton bidiyon.

  4. Ceballos ya kai Arsenal wasan daf da karshe a FA Cup

    Dani Ceballos ne ya ci wa Arsenal kwallo na biyu da ya kai kungiyar wasan daf da karshe a FA Cup, bayan doke Sheffield United 2-1 ranar Lahadi.

    Gunners ce ta fara cin kwallo ta hannun Nicolas Pepe a bugun fenariti, bayan da Chris Basham ya yi wa Alexandre Lacazette keta a da'ira ta 18.

    Daga baya ne mai masukin baki, Sheffield ta farke ta hannun McGoldrick saura minti uku a tashi daga karawar.

    Bayan da alkalin wasa ya kara lokaci ne Arsenal ta ci kwallo na biyu ta hannun Ceballos wanda ke buga wa kungiyar wasannin aro.

  5. Coronavirus: sama da mutum miliyan 10 sun kamu kusan 500,000 sun mutu

    Akwai sama da mutum miliyan 10 da aka tabbatar suna dauke da cutar korona a fadin duniya. kuma sama da miliyan hudu a Amurka suke, sai miliyan 2.6 da ake Turai.

    Kimanin mutum 500,000 ne suka mutu a fadin duniya dalilin cutar tun bayan bullarta watanni shida baya.

    Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce an rika samun yaduwar cutar cikin gaggawa tun daga tsakiyar Mayu kuma yanzu an fi fuskantar karuwar tata a kasashen Brazil da Mexico da kuma Chile.

    Haka kuma ana samun karuwar cutar a Afrika da yankin kudancin Asiya, yayin da Indiya ke da masu cutar da suka haura rabin miliyan.

  6. Coronavirus: Babu mutuwa cikin awa 24 a Madrid

    Akwai labarai masu daɗin ji daga Spaniya, wadda takasance daya daga cikin kasashen da annobar korona ta yi wasa kaca-kaca a Turai.

    A ranar Asabar ba a samu ko rahoton mutum daya da ya mutu ba a birnin a karon farko ton lokacin da cutar ta isa birnin, Kamar yadda shugabar yankin na Madrid Isabel Díaz Ayuso, ya sanar.

    "Mu hada hannu tare domin ganin wannan annoba ta zo karshe," ta rubuta a shafinta na tuwita ranar Lahadi.

    Wannan ba karamin sauyi ba ne aka samu idon aka kwatanta da 'yan watannin da suka gabata, kuma ta ce akalla mutum 3,000 ne suka mutu a yankin,

    Sama da mutum 28,000 ne suka mutu a Spaniya tun barkewar annobar, kuma akwai sama da 250,000 da aka tabbatar suna dauke da cuatar a kasar.

  7. An yi jima’i cikin motar Majalisar Dinkin Duniya

    Majalisar Dinkin Duniya ta ce ta yi matukar kaɗuwa tare da damuwa da wani hoton bidiyo da ke yawo wanda ya nuna yadda aka yi jima'i a daya daga cikin motocinta a Isra'ila.

    Hoton bidiyon ya nuna yadda wata mata sanye da jajayan tufafi ta yi dare-dare kan wani mutum sanye da bakaken kaya a kujerar baya a wata farar mota 4x4 mai tambarin MDD.

    Bidiyon da ake ta ci gaba da yada shi a shafukan sada zumunta ya nuna yadda aka dauki hoton a kan daya daga cikin manyan titunan birnin Tel Aviv.

    Majalisar Dinkin Duniya ta ce tana bincike kan al'amarin kuma tana daf da gano mutanen da aka dauka.

    Ta ce ta yi amannar wadanda suka aikata wannan abu mambobin dakarun wanzar da zaman lafiya ne da ke aiki a Isra'ila.

    Ana kuma iya ganin wani mutum a zaune a gaban motar amma ba a iya ganin matukin tun da tafiya motar take.

    MDD na da tsauraran manufofi kan duk wani nau'i na jima'i da ba bisa ƙa'ida ba ga mambobinta.

  8. An rantsar da sabon shugaban Malawi

    An rantsar da Lazarus Chakwera a matsayin sabon shugaban kasar Malawi bayan sake zabe a karo na biyu.

    "Lokaci ya zo da zamu farka daga barci mu cika wa kasarmu burinta," in ji Lazarus Chakwera yayin bayanin rantsuwar da ya gabatar.

    Mista Chakwera ya doke shugaba mai ci Peter Mutharika da kashi 58.57 na ƙuri'un da aka kaɗa a zaben da aka gudanar ranar Talata, kamar yadda hukumar zaɓen ƙasar ta sanar ranar Asabar.

    A watan Fabrairu, Kotun kundin tsarin mulki ta Malawi ta doke nasarar da shugaba Mutharika ya samu a zaben watan Mayun 2019, inda ta ce an yi maguɗi a zaben.

    Zaɓen zagaye na biyu da aka gudanar makon nan ya raba kan al'ummar ƙasar.

    Karo na biyu kenan a Afirka ana soke zaɓen shugaban kasa kan zargin maguɗi bayan Kenya a 2017

  9. Rikici ya barke a Myanmar

    Majalisar Dinkin Duniya ta ce rikici na ƙara zafi a yankin arewa maso yammacin Myanmar, ta na mai ba da shawarar a dauki matakan gaggawa domin kare fararen hula da ke yankin.

    Rahotanni daga jihar Rakhine na cewa, dubban mazauna kauyuka sun tsere daga gidajensu, bayan jami'ai sun yi gargadin cewa sojoji na shirin kakkabe mayakan Buddhist da ke neman 'yanci.

    Irin wannan ikirarin ne ya sanya dubban musulman Rohingya guduwa zuwa Bangladesh da ke makwabtaka a 2017, amma daga baya gwamnati ta ce wani dan atisaye ne kawai za a gudanar kan 'yan tawayen Buddhist.

    Majalisar Dinkin Duniya ta ce an kashe gwammai kuma an kora dubbai daga muhallansu a rikicin.

  10. An kara sanya dokar kulle a China

    Sake barkewar annobar Covid - 19 a wajen birnin Beijing ya sanya hukumomin China sun kara dokar kulle kan kusan mutum 500,000.

    Jam'ai sun ce wannan gagarumin al'amari ne yake tunkarar lardin Anxin bayan an gano mutum 12 masu dauke da cutar.

    An shawarci duka mazauna yanke da su ci gaba da kasancewa a gida - an kuma yarda mutum daya a ko wanne iyali ya fita domin bukatar yau da kullum.

    An takaita harkokin sufuri na ciki da na wajen birnin.

  11. Iran za ta sanya dokar takunkumi

    Iran wadda ita ce kasar da annobar korona ta fi yi wa illa a kasashen gabas ta tsakiya ta ce za ta mayar da sanya takunkumi ya zama wajibi daga ranar Lahadi mai zuwa.

    Da yake bayani ta kafar talabijin, shugaba Hassan Rauhani ya ce za su mayar da amfani da takunkumin ya zama wajibi a yankunan da aka rufe kuma ake da cunkoson mutane, sai dai bai fadi hukuncin da za a yi wa wadnda suka karya dokar ba.

    Kamar yadda mataimakin ministan lafiya na kasar ya bayyana cewa, babu wanda za a bari ya yi aiki ba tare da sanya takunkumin ba daga hukumomin gwamnati zuwa manyan kantuna.

    Shugaba Rauhani ya ce mahukunta za su kara mayar da hankali kan dokar kulle a yankunan da ake fama da hadarin annobar korona.

    Iran ta bayar da rahoton wadanda suka kamu da cutar akalla 222,669 kuma 10,508 sun mutu sakamakon Covid -19 din.

  12. Yadda aka yi jana'izar Abiola Ajimobi

    Da misalin karfe 12 na rana ne aka yi jana'izar Ishaq Abiola Ajimobi a Oke-Ado, kuma an gudanar da jana'izar ne a takaice da mutanen da basu fi 20 ba.

    An sanya tsattsauran tsaro a yankin unguwar da gidan mamacin yake saboda masu son halartar jana'izar.

    Cikin wadanda suka halarci jana'izar akwai Alhaji Kunle Saani, Shik Muideen Bello, babban limamin masallacin Ibadan, Sheik Abubakri Abdulganiyu Agbotomokere da sauransu.

    Ya mutu ya bar mace daya Florence Ajimobi da kuma yara biyar. Daya daga cikin 'ya'yansa Idris Ajimobi ya auri 'yar gidan gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, wato Fatima.

  13. Coronavirus: Delhi ya zama wuri mafi hadaria a Indiya

    Tare da samun masu dauke da Covid-19 da suka kai 77,000, babban birnin Indiya Delhi ya zamo wuri mafi hadari a fadin kasar.

    Mahukuntan birnin sun ta magana kan yadda mutane ke watsi da dokar kullen da aka sanya a brinin, wadda yanzu ta haura wata biyu.

    Rashin bibiyar masu cutar, da karfa-karfa kan hukunce-hukunce da rashin sanya idanu kan asibitoci masu zaman kansu duk suna cikin abubuwan da suka ta'azzara cutar a jihar.

    Wasu daga cikin kananan biranen Indiya sun dauki matakan kariyar da suka fi na Delhi, inda nan ne gwamnatin kasar ke zaune.

    Birnin Bangalore da ke kudancin kasar ya mayar da hankali kan bibiyar marasa lafiyar, yayin da Chennai wanda aka fi sani da Madras yake da karancin wadanda suka mutu sakamakon cutar duk da cewa ana samun karuwar masu kamuwa.

  14. Sri Lanka ta janye dokar kullenta

    Wasu labarai masu dadin ji: Sri Lanka ta janye duka dokar kullen da ta sanya a watan Maris a wani mataki na shawo kan yaduwar cutar korona.

    Hukumomin kasar sun rika janye dokar kullen da aka sanya da rana a hankali, amma sun ci gaba da daukar tsauraran matakai kan dokar dare.

    Yanzu kuma duka an janye dokar, amma hukumomin lafiya na shawartar al'umma da su rika tabbatar da matakan kariyar da aka ce a rika dauka da kuma dokoki.

    Dokar kullen ba sani ba sabon da aka sanya da kuma gwajin da aka rika yi a fadin kasar ya tai maka wa Sri Lanka wajen rashin samun wadanda suka mutu sakamakon cutar idon aka kwatanta da sauran kasashen yankin kudancin Asia

  15. Labarai da dumi-dumi, Masu cutar korona a duniya sun haura miliyan 10

    Sama da mutum miliyan 10 ne aka tabbatar sun kamu da cutar korona a fadin duniya, kamar yadda jami'ar Johns Hopkins ta Amurika da ke bibiyar cutar ta bayyana.

    A gefe daya kuma adadin mutanen da suka mutu sakamakon cutar ya kai 499,124, da kuma yiwuwar ya kai rabin miliyan nan da 'yan awanni.

  16. 'Yan Kannywood suna taya Ganduje yaƙi da cutar korona

    Taurarin fina-finan Kannywood sun bi sahun gwamnatin jihar Kano da ke arewacin Najeriya wajen yaki da cutar korona.

    Taurarin sun dukufa wajen wayar da kan jama'a kan illar cutar da kuma matakan da jama'a za su bi wurin kauce wa kamuwa da ita, kamar yadda Ma'aikatar Lafiyar jihar ta bayyana a shafinta na Twitter ranar Lahadi.

    An ga fuskokin taurari irin su Yakubu Mohammed, Saratu Gidado (Daso) Aminu Shariff (Momo), Rukayya Dawayya, Dan Azumi Baba Chediyar, Abba Al-Mustapha da makamantansu a taron wayar da kan jama'a da gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta hada ranar Asabar.

    Ya zuwa ranar Asabar da almuru, mutum 1,195 aka tabbatar sun kamu da cutar a jihar Kano ko da yake an sallami mutum 835 bayan sun warke, amma ta kashe mutum 51.

    A kwanakin baya, Ministan Lafiya Osagie Ehanire ya bayyana wa manema labarai a Abuja cewa binciken da tawagar gwamnatin tarayya ta gudanar game da ƙaruwar mace-mace a jihar Kano ya nuna cewa mutum 979 ne suka mutu a kwanan nan sanadin mace-macen da ba a saba gani ba a jihar.

    Sai dai gwamnatin Kano ta musanta rahoton tana mai cewa: "Mutum 255 cikin 1604 da suka mutu, wato kashi 15.9... ne suka mutu sanadin cutar korona. Wasu daga cikin mace-macen suna da alaka da rashin samun magunguna da kuma dakatar da harkokin rayuwa da na kasuwanci saboda fargabar annobar korona."

  17. Man U na son Sancho, Ronaldinho ya amsa kiran Maradona

    Borussia Dortmundtana cike da fatan dan wasanta mai shekara 20 dan Ingila Jadon Sancho zai ci gaba da murza leda a kulub din inda har yanzu babu wanda ya taya dan wasan.(Sport Buzzer, via Goal).

    Jurgen Klopp ya ce yana ganin Sancho ya fi dacewa daLiverpoolamma ba tare da kocin ya ce zai dauko dan wasan ba a bana.(Bild, via Liverpool Echo)

    KocinManchester UnitedOle Gunnar Solskjaer bai yanke kauna ba kan Sancho idan an bude kasuwar musayar 'yan wasa a bazara.(Manchester Evening News)

    Liverpoolda ta lashe kofin Premier tana shirin taya dan wasan baya naNapolida Senegal Kalidou Koulibaly, mai shekara 29.(Tuttomercato, via Mail)

  18. Cutar korona tana ci gaba da mamaya a Najeriya

    Mutum 779 ne aka ba da rahoton sun sake kamuwa da cutar korona a ranar Asabar a Najeriya kenan adadin masu cutar a kasar ya kai 24,077.

    Alkalumman da hukumar dakile cutuka masu yaɗuwa, NCDC ta fitar sun ce cutar ta sake kashe mutum huɗu a kasar ranar Asabar inda yanzu jimillar wadanda cutar ta kashe suka kai 558.

    Alƙaluman na Hukumar ta NCDC sun nuna har yanzu jihar Legas ce ke kan gaba inda ta sake kama mutum 285 a jihar.

    Sai dai kuma an samu mutum 11 da suka kamu da cutar a jihar Sokoto, jihar da a baya ta yi ikrarin gusar da cutar daga ban kasa.

  19. Dakarun Saudiyya sun yi harbin gargaɗi kan jiragen ruwan Iran

    Dakarun kasar Saudiyya sun yi harbi irin na kifin-na-ganinka-mai-jar-koma kan wasu jiragen ruwan kasar Iran guda uku da aka gani na shawagi a gabar ruwan Saudiyya.

    Wani jami'i mai magana da yawun masu tsaron gabar ruwan Saudiyyar ya ce jiragen sun ki tsayawa duk da gargadin da aka yi musu ranar Alhamis.

    Kasar Iran ta ce jiragen ruwan nata na yin su ne kuma santsi ya kwashe su suka fada iyakar ruwan na Saudiyya.

    Kasashen musulmin guda biyu dai sun kwashe shekaru ba sa ga maciji da juna.

  20. Cutar korona ta kama mutum fiye da milyan 2.5 a Amurka

    Cutar korona ta kama mutum fiye da milyan biyu da rabi a duk fadin Amurka, inda rahotanni suka ce an samu karuwar masu kamuwa da ita a jihohin Florida da Texas.

    An samu wannan karuwa ne sakamakon sake bude kasuwanni da sauran harkoki a makwannin baya bayan nan.

    Ranar Asabar, an samu karin mutum fiye da 9,500 da suka harbu da cutar a Florida.

    Hakan ne ya sa hukumomi suka sake daukar tsauraran matakai na hana zirga-zirga a a jihar ta Florida, kamar yadda aka yi a Texas ranar Juma'a.

    Shugaban kwamitin yaki da cutar korona na kasar, Dr Anthony Fauci, ya yi gargadi a makon jiya cewa Amurka tana "cikin gagarumar matsala".