Me ya sa a bayar da cikakkun alƙaluman matan da ke kamuwa da korona?
Wata ƙungiyar ba da agaji na gargaɗin cewa ba a bayar da cikakkun alƙaluman matan da ke kamuwa da cutar korona a wasu ƙasashe.
Ƙungiyar mai suna International Rescue Committee na fargabar cewa ana barin mata a baya cikin shirye-shiryen gwajin korona a ƙasashen Somaliya da Yemen da kuma Afghanistan.
Ta ce a ƙasashen ciki har da Chadi da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya fiye da kashi saba'in cikin 100 na mutanen da suka kamu da korona, maza ne, gagarumin yawa kan adadin da aka saba gani na kashi 51% a ƙasashen duniya.
Gidauniyar ta ce hakan ba abu ne mai yiwuwa ba don kuwa matan sun fi yiwuwar kamuwa da ƙwayar cutar a irin waɗannan ƙasashe saboda su ne suka fi yin ayyukan kula da lafiya.

