Masu cutar korona a duniya za su kai miliyan 10 zuwa makon gobe - WHO

Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye dangane da irin wainar da ake toyawa a fadin duniya musamman batutuwan da suka shafi Najeriya da Nijar da makwabtansu.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya and Buhari Muhammad Fagge

  1. Kotu ta yi watsi da tuhumar da ake yi wa Micheal Flynn

    Getty

    Asalin hoton, Getty Images

    Kotun daukaka kara a Amurka ta kori karar zargin aikata laifin ta'addanci da ake yi wa tsohon mai bai wa shugaba Trump Shawar kan sha'anin tsaro Micheal Flynn.

    A cewar wakilin BBC mai shari'ah a kotun daukaka karar ya naɗa wani alkali na daban mai zaman kansa wanda kuma bayan sake sauraren karar ya kore ta.''

    A wani hukunci na daban wata kotun a Washington ta bai wa Ma'aikatar shari'a umurnin janye tuhumar da ake yi wa Mista Flynn duk da tabbatar da cewa ya yi wa hukumar leken asiri asirin kasar karya kan hirarsa da jakadan Rasha.

    Mista Flynn na daga cikin jami'an gwamnatin Trump da aka tuhuma a binciken Mueller, kan katsalandan a zaben Amurka na 2016.

  2. Shugaban Kosovo na fuskantar tuhuma bisa laifukan yaki

    Getty

    Asalin hoton, Getty Images

    Masu shigar da kara a kotun duniya da ke Hague sun maka shugaban Kosovo kotu, kan zargin aikata laifukan yaki.

    Shugaba Hashim Thaci na fuskantar laifukan yakin Kosova da aka yi a shekarar 1990, a lokacin yana jagorancin wata kungiyar 'yan tawaye.

    Shi ma tsohon shugaban majalisar wakilai Kadri Veseli na daga cikin wadanda ake tuhuma.

    Masu shigar da karar sun ce shugaban da sauran wadanda ake tuhuma ne ke da alhakin kisa da kuma azabtar da kusan mutun 100 a lokacin.

    To amma Mista Thaci da Mista Veseli sun musanta zarge-zargen.

    Wakiliyar BBC tace masu shigar da karar sun kafa hujja da cewa Mista Thaci da Mista Veseli sun yi ta kokarin kawo wa kotu matsala a kokarin kaucewa tuhumar da ake musu.''

  3. Dan majalisar da ya sha barasa ya shiga shirin talabijin a Mozambique ya bar abin fada

    STV

    Asalin hoton, STV

    Babbar jami'iyyar adawa a Mozambique Renamo ta nemi ahuwa kan abin kunyar da Antonio Muchnga wanda daya ne daga cikin fitattun 'yan majalisa ya yi, na shiga wani shirin siyasa na wani gidan talabijin bayan ya sha barasa ya yi mankas.

    Mista Muchanga ba ya cikin hayyacinsa lokacin da ake gabatar da shirin a gidan latabajin na STV, inda daga baya mai gabatar da shirin ya nemi da ya fita daga dakin da ake gabatar da shirin.

    Hakan ya jayo suka tare da nuna kaduwa game da abin da ya yi a kasar, sai dai sama da kwana biyu jam'iyyarsa ba ta ce komai kan batun ba.

    Sai dai mai magana da yawun jam'iyyar Jose Manteigas, ya shaida wa wata kafa cewa abin da Muchanga ya yi ba karamin zubar da kima ba ne.

    Ya ce jam'iyyar ba ta zaton mambanta ya shawu sannan ya shiga shirin talabijin - dan haka zai bayyana gaban kwamitin ladabtarwa na jam'iyyar.

  4. Corona na kara dabaibaye tattalin arzikin duniya - IMF

    Getty

    Asalin hoton, Getty Images

    Asusun ba da lamuni na duniya IMF ya bayyana cewa halin da tattalin arzikin duniya zai shiga saboda annobar Korona ya wuce yadda ya yi hasashe.

    Sabon rahoton da ya fitar ya nuna cewa kason abubuwan da aka shirya gudanarwa zai yi ƙasa da kusan kashi a shekarar da ake ciki.

    IMF ya kara da cewa annobar za ta yi mummunar illa ga masana'antu fiye da yadda yayi hasashe tunda farko.

    India na cikin kasashen da asusun ba da lamunin ya yi hasashen ba za su shiga matsala sosai ba, to amma yanzu ya ce ita ma ka iya shiga matsala.

  5. Ba matsalar na'ura ce ta haddasa hadarin jirgin Pakistan ba - Ghulam Sarwar Khan

    EPA

    Asalin hoton, EPA

    Binciken farko farko da aka gudanar kan faduwar jirgin saman fasinja a Pakistan da ya kashe mutun 97 ya nuna cewa matsalar ba ta na'ura ba ce.

    Ministan sufurin jiragen sama Ghulam Sarwar Khan ya shaida wa yan majalisa cewa jirgin sam bashi da matsala.

    Wakilin BBC ya ce ministan ya bayyana cewa direban jirgin ne ya kasa sarrafa giyar jirgin a lokacin da ya yi niyyar sauka a karon farko wanda hakan ya haifar da matsala ga wani inji.

    Kuma duk da haka yaki ya sanar da masu duba na'ura a filin jirgi yayin da jirgin ke dab da faduwa.''

    An kuma gano cewa ko lokacin saukar maimakon ya mai da hankalinsa wuri daya sai aka ji suna hira kan annobar Korona.

    Jirgin kirar Airbus ya fada ne kan gidajen jama'a a Karachi kuma mutun biyu ne kawai suka tsira.

  6. Masu cutar korona a duniya za su kai miliyan 10 zuwa makon gobe - WHO

    Reuters

    Asalin hoton, Reuters

    Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce tana tsammanin adadin masu dauke da cutar korona zai kai miliyan 10 a fadin duniya nan da makon gobe.

    "An bayyana wa WHO akwai sama da mutum miliyan 9.1 da ke fama da cutar a yanzu, kuma sama da 470,000 sun mutu a duniya," kamar yadda shugaban hukumar Dakta Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya shaida wa maneman labarai a Geneva.

    "A watan farko na barkewar annobar, kasa da mutum 10,000 ne suka kamu, amma a watan da ya gabata kimanin mutum miliyan 4 ne aka ba da rahoton kamuwarsu.

    "Muna zaton masu dauke da cutar za su kai miliyan 10 nan da sati mai zuwa."

    Ya kira wannan lamari "wata tunasarwa mai daci don bukatar daukar matakin gaggawa da za mu iya mu takaita yaduwar cutar da kuma ceton rayuka".

  7. An kara tsawaita dokar kulle a India

    Getty

    Asalin hoton, Getty Images

    Jihar West Bengal da ke India ta kara tsawaita dokar kulle har zuwa ranar 31 ga watan Yuli sabado shawo kan cutar Covid-19 bayan ci gaba da yaduwa da cutar take yi a fadin kasar.

    Dokar kullen da aka sanya za ta kare ne a ranar 30 ga watan Yuni,

    Amma ana kara samun sabbin masu dauke da cutar a kasar, Wani babban jami'i a gwamnatin yankin ya ce wajibi ne a kara tsawaita dokar domin taimakawa wajen ceto India daga halin da ta tsinci kanta.

    Makarantu da kwaleji da kuma jami'o'i za su ci gaba da kasancewa a rufe, amma za a sassauta wani bangare na dokar nan gaba.

    An samu karin mutum 16,000 masu fama da cutar wanda ya kai addain masu cutar 456,000 a ranar Laraba, wanda wannan shi ne adadi mafi yawa da aka taba samu a kasar.

    Kuma adadin wadanda suka mutu a kasar ya kai 14,000.

  8. An kwace lasisin wata jarida a Tanzania

    Tanzania Daima

    Asalin hoton, Tanzania Daima

    An kwace lasisin jaridarar The Tanzania Daima sakamakon "karya dokar ladubban aikin jarida na kasar", in ji ministan yada labarai na kasar.

    Daga ranar Laraba ba, an haramtawa jaridar mai zaman kanta ta buga wani abu ko kuma raba jaridar a fadin kasar da ke gabashin Afrika ko kasashen waje.

    "An yi ta kokarin jan kunnen da kuma tunatar da mai tace labaran jaridar da su rika bin dokokin da suka sanya hannu kai lokacin karbar lasisinsu, amma suka gaza yin hakan, ba su da aiki sai buga labaran da ke yamutsa hazo da kuma mummunar niyya," minintan ya kara da cewa.

    Ya kara da cewa amma za su iya kara neman siyan lasisin wata jaridar dan ci gaba da aiki.

    Ba dai wannan ne karon farko da aka taba kwace lasisin jaridar ba.

  9. Hotunan bikin Rasha na ranar samun nasara kan Nazi

    Reuters

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Sama da dakaru 13,000 ne suka halarci wannan faretin a wannan shekara
    EPA

    Asalin hoton, EPA

    Bayanan hoto, An keɓe waɗanda suka halarci yaƙin kafin fara faretin bikin ranar
    Reuters

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, A watan Mayu ya kamata a yi bikin amma shugaba Putin ya jinkirta shi saboda korona
    Getty Images

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Jirage na tashi a saman dandalin da ake bikin suna fitar da hayaƙin da yake hada tutar Rasha
    Getty

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Daruruwan motoci masu sulke da kuma dakaru ne suka halarci bikin
    Getty

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Ma'aikata daga kasashen daban-daban ne suka halarci taron ciki har da na India
  10. Shugaba Peter Mutharika na dab da shan kaye a zaben Malawi

    EPA

    Asalin hoton, EPA

    Sakamakon zabe da aka tattara daga matakin gundumomi a Malawi ya nuna cewa shugaba Peter Mutharika na dab da shan kaye a zaben da aka gudanar jiya Talata.

    Duk da ba a fitar da sakamakon ba a hukumance, yan takarar sun taka rawa sosai a yankunan da suka fito, to amma dan takarar jam'iyyar adawa Lazarus Chakwera ya fi yin abun azo a gani sosai a arewacin kasar da babu wanda ya fito daga nan.

    A yanzu hukumar zabe za na duba yiwuwar tafka magudi kafin bayyana sakamakon a cikin kwanaki takwas.

    A bara ne Mr Mutharika ya lashe zaben dakyar a zaben da kotu ta soki saboda zargin tabka magudi

  11. Rasha na bikin ranar samun nasara kan Nazi

    Reuters

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaban Rasha Vladmir Putin ya jinjina wa dakarun Soviet kan rawar da suka taka wurin murƙushe gwamnatin Nazi ta Jamus a yaƙin duniya na biyu.

    Mista Putin ya bayyana hakan a bikin shekara-shekara da ake gudanarwa duk da annobar Korona da ake ci gaba da fuskanta a bana.

    Haka ma bikin na zuwa a daidai lokacin da shugaban ke fuskantar ƙuri'ar raba gardama da za ta bashi damar ci gaba da shugabancin Rasha har zuwa shekarar 2026.

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    A cewar Putin, haɗin kan ƙasashen Yamma ne ya ba da nasarar da ake matuƙar buƙata a lokacin yakin.

    Manyan baƙin da aka gayyata don bikin na cika shekaru 75 da kammala yaƙin duniyar sun saka takunkumin rufe fuska sun kuma ba da tazara.

    Bugu da ƙari an killace 'yan mazan jiya da suka yi yaƙi da dakarun Jamus a lokacin.

  12. An kama ministan lafiyar Zambia kan cin hanci

    Kennedy Gondwe

    Asalin hoton, Kennedy Gondwe

    An kama ministan lafiya na Zimbabwe Chitalu Chilufya saboda zargin cin hanci da rashawa.

    An kama likitan mai shekara 47 tare da wani ɗan siyasa, sai dai 'yan sanda sun sake su a matsayin beli, bayan wani bincike da hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasar ta gudanar.

    "Ana tuhumar Dakta Chitalu Chilufya da laifuka huɗu, ciki har da na mallakar wata kadara wadda ake zargin zai aikata wani babban laifi da ita," in ji mai magana da yawun ACC Jonathan Siame.

    Ministan dai har yanzu bai ce komai ba kan zargin da ake masa, ana sa ran zai bayyana gaban kotun ne a Lusaka babban birnin ƙasar a ranar Alhamis 9 ga watan Yuli.

    Hukumar dai za a iya cewa ta samu nasara wajen gurfanar da manyan jami'an da ke riƙe da manyan muƙaman gwamnati a kasar.

  13. 'Yan sanda sun tarwatsa masu zanga-zanga a Congo

    Mbelechi Msoshi/BBC

    Asalin hoton, Mbelechi Msoshi/BBC

    'Yan sanda a Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo, sun yi amfani da hayaƙi mai sa hawaye wajen tarwatsa zanga-zangar magoya bayan shugaban ƙasar Félix Tshisekedi.

    Ɗaruruwan masu zanga-zangar ne suka halarci wajen a kan babura domin zanga-zanga a wajen majalisar ƙasar da ke babban birnin Kinshasa, kan ƙoƙarin sauya tsarin shari'ar ƙasar.

    Walikin BBC Mbelechi Msoshi ya gansu suna kona tayoyi suna wake lokacin zanga-zangar.

    Mbelechi Msoshi/BBC

    Asalin hoton, Mbelechi Msoshi/BBC

    Mbelechi Msoshi/BBC

    Asalin hoton, Mbelechi Msoshi/BBC

    Suna cewa wannan kuduri da aka gabatar gaban majalisar wani yunkuri ne na tabbatar da kariya ga abokan tsohon shugaban kasar Joseph Kabila daga fuskantar shari'a.

    Sun kuma kara da cewa wannan kudurin zai bai wa ministan shari'ar kasar damar daukar hukunci da ya ga dana kan su waye za a hukunta.

    Masana na cewa Mista Kabila har yanzu na da karfin fada a ji a kasar tun bayan saukarsa daga shugabancin kasar a watan Janairun 2019 - kuma mambobin gamayyar jam'iyyar siyasarsa ne suka mamaye majalisar.

    Mbelechi Msoshi/BBC

    Asalin hoton, Mbelechi Msoshi/BBC

  14. Da wuya a cimma manufar kirkirar kudin bai-ɗaya na Eco - Buhari

    Getty

    Asalin hoton, Getty Images

    Masana sun fara tofa albarkacin bakinsu a kan gargadin da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jaddada cewa matukar kasashen Afirka ta yamma ba su fara amfani da kudin bai daya na Eco lokaci guda ba, da wuya a cimma manufar da ta sa aka kirkiri kudin.

    Kasashen shiyyar Afirka ta yamma sun yanke shawarar amfani da sabon kudin ne bisa yakinin cewa zai taimaka wajen saukaka harkar kasuwanci tare da bunkasa tattalin arziki a shiyyar.

    Dr Obadia Mailafia, tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya ne, wanda a tattaunawarsa da BBC ya ce gargadin da shugaba Buhari ke yi yana da ma`ana.

  15. 'Yan majalisar wakilan Gabon ba sa so a hukunta masu auren jinsi daya

    Mambobin majalisar wakilan Gabon sun kada kuri'ar amincewa a daina hukunta masu auren jinsi daya a kasar.

    Idan kudurinsu ya samu amincewar takwarorinsu na majalisar dattawa da shugaban kasa, Gabon za ta kasance cikin kasashe kalilan na Afira kudu da hamadar sahara da suka y wats da dokar hukunta masu auren jinsi daya.

    A bara, kasar ta Tsakiyar Afirka ta zartar da dokar hukunta masu auren jinsi sannan ta ce 'yan luwadi za su rika shan daurin wata shida a gidan yari da kuma cin su babbar tara.

    masu fafutuka sun ce matakin ya sa masu auren jinsi daya sun rika buya.

      Auren jinsi daya

      Asalin hoton, Getty Images

    • An fara gwajin riga-kafin cutar korona a Afrika Ta Kudu

      coronavirus

      Asalin hoton, Getty Images

      An fara yin gwajin maganin cutar korona a Afrika Ta Kudu da Brazil, wanda Jami'ar Oxford da ke Burtaniya ta samar.

      Za a yi wa mutum 2,000 gwajin a Afrika Ta Kudu, a wani abu da ake kallo a matsayin gwajin na wurwuri na riga-kafin da zai shawao kan wannan annoba.

      An fara yin gwajin farko na riga-kafin a birnin Johannesburg a wannan makon.

      An zabi Afrika Ta Kudu ne ba kawai don kwarewarta ba, sai don yadda cutar korona ke yaduwa cikin sauri a kasar.

      Hakan zai saukaka wa masana kimiyya samun wata al'umma da ke fuskantar barazanar kamuwa da cutar, sannan su gane ko wannan riga-kafin na Burtaniya yana aiki.

      Ana gudanar da irin wannan gwajin a Burtaniya, amma ana samun raguwar masu kamuwa da cutar.

      Wannan gwaji ba Afrika Ta Kudu kawai zai shafa ba, har da ma Brazil inda za a yi wa mutum 5,000 gwajin riga-kafin.

    • An kama Indiyawan da suka kulle mutum 300 a kamfani a Kano

      Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce ta kama hudu daga cikin Indiyawan da suka kulle ma'aikatansu kusan 300 a kamfanin shinkafa da ke jihar Kano.

      Ranar Litinin aka ceto mutanen daga kamfanin na shinkafa bayan da suka yi korafin cewa kamfanin ya rufe su tsawon wata uku.

      Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kano, DSP Haruna Kiyawa ya ake a manema labarai sanarwar da e cewa "mun samu korafi daga kungiyar are hakkin dan adam ta Global Community for Human Right Network Kano cewa kamfanin Popular Farms and Mills Limited ya rike wasu leburori ba bisa ka'ida ba."

      Ya ce daga an ne suka aka jami'an 'yan sandan inda ssuka kama hudu daga cikin jamian kamfanin.

      Ya kara da cewa ana ana gudaar da bincike a kansu kuma za su dauki matakin da ya dace.

      'Yan sanda

      Asalin hoton, NPF

    • An kama dan adawa a Tanzania

      Babbar jam'iyyar hamayya a Tanzania ta yi tir da kamun da aka yi wa shugabanta tana mai bayyana kamun a matsayin yunkurin murkushe su da hana su fadar albarkacin baki gabanin babban zaben kasar da za a yi a watan Oktoba.

      Jam'iyyar Alliance for Change and Transparency (Act) ta ce 'yan sanda sun zargi, Mr Zitto Kabwe da abokan gwagwarmayarsa bakwai da gudanar da taro ba bisa ka'ida ba.

      'Yan sanda sun watsa taron siyasa da ska gudaar a garin Linde da ke kudu maso gabashin kasar inda aka kama su aka tsare ba bisa ka'ida ba, a cewar sanarwar da jam'iyyar ta fitar.

      Shugaba John Magufuli, wanda ake sa ran zai sake tsayawa takara, ya rusa majalisar dokokin kasar makon jiya.

      Kungiyoyin kare hakkin dan adam sun koka game da yawaitar kama masu hamayya tun da Shugaba Magufuli ya hau kan mulki a 2015 suna masu cewa ana rufe gidajen watsa labarai saboda suna yin abin da gwamnati ba ta so.

      Zitto Kabwe,

      Asalin hoton, Getty Images

    • Barcelona za ta sayar wa Juventus Arthur a kan £72.5m

      Juventus ta amince ta biya euro 80m domin karbo dan wasan Barcelona mai shekara 22 dan kasar Brazil, Arthur - Amma dole ta rarrashe shi kafin ya koma can.(Sky Sports)

      Dan wasan tsakiya na Portugal William Carvalho, mai shekara 28, ya cimma yarjejeniya da Leicester City, abin da ya rage kawai shi ne kungiyar ta Gasar Firimiya ta daidaita da Real Betis kan farashinsa (Marca)

      Crystal Palace tana dab da da kammala sayen Nathan Ferguson bayan West Brom ta tabbatar cewa dan kasar Ingila mai shekara 19 ya ki amsa tayin sabunta kwangilarsa.(Guardian)

      Ana sa ran Arsenal za ta amince da tsawaita kwangilar dan wasan Portugal Cedric Soares wanda ta karbo aronsa daga Southampton kuma tana so ta sayi dan wasan mai shekara 28 gaba daya idan aka bude kasuwar musayar 'yan kwallon kafa.(ESPN)

      Arthur

      Asalin hoton, Getty Images

    • COVID-19: Yadda kasuwar namun daji take bunkasa a Najeriya

      Namun dadi

      Ana ci gaba da sayar da namun daji a Lagos, babban birnin kasuwacin Najeriya, duk da kiraye-kirayen da ofishin kare muhalli na majalisar dinkin duniya yake yi cewa akan yana da hatsari ga muhalli.

      A kasuwar Olowu da ke yankin Epe, daya daga cikin kasuwannin namun daji mafiya shahara, ana sayar da su kullu yaumin.

      Masu yin wannan sana’a sun dage cewa namun daji ba su da wani hatsarin yada cutar korona, duk da rahotannin da ke cewa cutar, wadda ta somo daga birnin Wuhan na kasar China, ya yadu ne daga jikin jemagu.

      Namun daji

      Wani mai aiko wa BBC rahotanni ya leka kasuwar inda ya ga ana cin kasuwar namun daji irin su kadoji, da guza, da jemagu da jakin dawa.

      Sai dai masu sayar da wadannan namun dajin sun ce an dan samu karancin ciniki a kasuwar.

      Namun dadi