Jihar Jigawa ta buɗe iyakokinta da sauran jihohi

Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye dangane da irin wainar da ake toyawa a fadin duniya musamman batutuwan da suka shafi Najeriya da Nijar da makwabtansu.

Rahoto kai-tsaye

Buhari Muhammad Fagge and Umar Mikail

  1. An gudanar da zanga-zangar neman shugaban Mali ya sauka daga mukaminsa

    AFP

    Asalin hoton, AFP

    Bayanan hoto, Ana neman sauyi ne kan tsarin siyasa da kuma tattalain arzikin kasar

    Dubban masu zanga-zanga a Mali sun taru a babban birnin kasar Bamako, suna kira da shugaban kasar ya sauka daga mukaminsa.

    Limamin nan mai ra'ayin rikau Mahmoud Dicko ne ya jagoranci zanga-zangar tare da goyan bayan gamayyar 'yan adawa, suna bukatar kawo sauyi a tsarin siyasar kasar da kuma tattalain arzikinta.

    Suna bukatar shugaba Ibrahim Boubacar Keïta da ya yi murabus saboda karuwar aikin masu tsattsauran ra'ayin addini da kuma karuwar rikicin kabilanci.

    AFP

    Asalin hoton, AFP

    Bayanan hoto, Dubban masu zanga-zanga ne suka taru a babban birnin kasar ta Mali

    Sai dai shugaban ya nemi a sake kafa wata gwamnatin gambiza da mambobin jam'iyyun adawa.

    Amma duk da tattaunawar neman mafitar da aka yi a farkon makon nan, an gudanar da zanga-zangar kamar yadda aka tsara.

    Mista Keita mai shakara 75, an fara zabar shi ne a matsayin shugaban kasar a 2013. Ya kuma koma zagaye na biyu na milkinsa a 2018.

    Sai dai a bayan nan yana fama da matsin lamba saboda tabarbarewar tattalin arzikin kasar, ga cutar korona, ga kuma yajin aikin malaman makarantu.

    An kuma fara fuskantar rikicin siyasa da ya bullo kai bayan zaben 'yan majalisa a kasar da ya gudana mai cike da rikici a watan Maris, da kuma zargin cin hanci da rashawa.

    AFP

    Asalin hoton, AFP

    Bayanan hoto, Shugaba Kaita ya tattauna da 'yan adawa domin shawo kan matsalar amma hakarsa bata cimma ruwa ba.
  2. Mutum fiye da miliyan daya sun kamu da cutar korona a Brazil

    Reuters

    Asalin hoton, Reuters

    Kasar Brazil ta zamo kasa ta biyu bayan Amurka wajen yawan masu dauke da cutar korona inda yanzu take da fiye da milyan daya masu dauke da cutar sannan kuma kimanin dubu 49 sun mutu sakamakon annobar.

    Wakiliyar BBC ta ce wannan ce rana ta hudu a jere da ake samun masu dauke da cutar fiye da 1200 da ke mutuwa.

    Alkaluman ba sa raguwa amma kuma gwamnati ta fara bude muhaimman wurare sannan jama'a sun fara komawa bakin aiki.

    Har wa yau kasar ta Brazil ta samu karin wadanda suka kamu da cutar ta korona fiye da dubu 20 a awanni 24.

    Yanzu dai alamu na nuna cewa da sannu annobar na yaduwa zuwa yankunan karkara musamman wadanda ke cikin dajin Amazon.

  3. An ƙone mutum-mutumin Albert Pike a Amurka

    Masu zanga-zanga a birnin Washinton DC sun kone mutum-mutumin wani fitaccen ba-Amurke Albert Pike bayan da suka ballo shi zuwa kasa.

    Danzadon masu zanga-zangar sun bushe da shewa da kirarin rayuwar bakin fata na da muhimmanci.

    Mutum hudu ne dai suka zargo mutum-mutumin da igiya inda suka janyo shi kasa da misalin karfe 10 na daren Juma'a.

    'Yan sanda suna wurin da abin ya faru amma su ma ido kawai suka zuba.

    Shugaba Trump na Amurka a shafinsa na Twitter ya wallafa cewa 'yan sandan ba sa aikinsu sannan ya nemi da a kama duk wadanda suka aikata al'amarin.

  4. Budewa

    Masu bibiyar mu barkanmu da wannan lokaci ku kasance tare da ni Buhari Muhammad Fagge domin kawo muku labarai kai tsaye a wannan shafin, wadanda suka shafi Najeriya da makwabtanta da ma sauran sassan duniya baki daya