Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye dangane da irin wainar da ake toyawa a fadin duniya musamman batutuwan da suka shafi Najeriya da Nijar da makwabtansu.
Rahoto kai-tsaye
Buhari Muhammad Fagge and Umar Mikail
Mun zo ƙarshen rahotannin
Masu bibiyarmu nan muka kawo ƙarshen rahotanni ka-tsaye a wannan shafi.
Umar Mikail ke cewa mu haɗu da ku gobe idan Allah ya kai mu.
Ku duba ƙasa domin karanta labaran abubuwan da suka faru a Najeriya da sassan duniya a ranar Asabar.
Jihar Jigawa ta buɗe iyakokinta da sauran jihohi
Asalin hoton, @Badaru_Abubakar
Gwamnan Jihar Jigawa Mohammed Badaru Abubakar ya sanar da buɗe iyakokin jihar da sauran jihohi, waɗanda aka rufe tun 24 ga watan Maris saboda annobar cutar korona, a cewar rahoton NAN.
Gwamnan wanda ya bayyana haka a taron manema labarai ranar Asabar a Dutse babban birnin jihar, ya ce za a buɗe zirga-zirga tsakanin jihar da sauran jihohi cikin tsauraran matakan kariya daga cutar.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya rawaito cewa buɗewar tana zuwa ne mako guda bayan an buɗe kasuwannin jihar da ke ci sati-sati.
Tuni aka sallami mutum 307 daga cikin 317 da suka kamu da cutar bayan sun warke, yayin da tara suka mutu.
"Muna ta addu'ar kada mu koma cikin irin wancan lokacin da ba shi da tabbas," in ji gwamnan.
"Yanzu haka mutum ɗaya ne yake jinya [ta cutar korona], inda sauran da ke cibiyar killace masu korona suka warke kuma aka sallame su.
"Muna kuma gode wa Allah, a cikin kwana huɗu da suka gabata ba a samu wani da ya kamu da cutar ba. Da addu'a da kuma taimakon 'yan Jigawa, za mu kawo ƙarshenta," in ji Badaru.
NAN ya ce gwamnan ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta bai wa jihar tallafin naira biliyan ɗaya, ƙari a kan mota 150 cike da hatsi domin raba wa marasa ƙarfi.
Sai dai gwamnan ya ce makarantu za su ci gaba da kasancewa a rufe har zuwa lokacin da al'amura suka lafa a ƙasa baki ɗaya.
Littafin John Bolton: Trump ya yi rashin nasara a kotu
Asalin hoton, AFP
Gwamnatin Shugaba Donald Trump na Amurka ta yi rashin nasara a kotu, inda ta buƙaci a hana buga littafin da tsohon mai bai wa shugaban shawara kan sha'anin tsaro ya rubuta.
Alƙalin wata kotu da ke Washington ya ce gwamnatin ta yi latti, kuma ya rage ga Mista John Bolton ya fitar da abin da ya san ba zai zama matsala ba a nan gaba.
A ranar Talata mai zuwa ne za a buga littafin, wanda tuni aka fara wallafa wasu shafukansa a jaridu da dama.
Wakilin BBC ya ce: ''Mista Trump ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa John Bolton zai yaba wa aya zaƙi kan abin da ya yi, don a cikin littafin akwai inda Mr Bolton ya ce Trump ya buƙaci shugaban Chana Xi Jin Ping ya taimaka masa ya samu lashe zaɓe a karo na biyu.''
An kuma bayyana Mista Trump a littafin a matsayin shugaban da ba ya iya bambancewa tsakanin ra'ayinsa da na ƙasa kan abin da ya shafi harkokin ƙasashen waje.
An ɗaure shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin Kongo shekara 20 a gidan yari
Asalin hoton, Reuters
An yanke wa shugaban ma'aikata a Fadar Gwamnatin Dimokuraɗiyyar Kongo hukuncin shekara 20 a gidan yari bisa laifin cin hanci da rashawa na dala miliyan 50.
An tsara saya wa 'yan sanda da sojoji gidaje da kuɗin da Vital Kamerhe ya karkatar a matsayin ɗaya daga cikin ayyukan da za a gabatar yayin bikin cika kwana 100 na mulkin Shugaba Tshisekedi.
Lauyoyinsa sun ci alwashin ɗaukaka ƙarar, wadda ta tanadi cewa ba zai yi wata takarar muƙamin siyasa ba cikin shekara 10 da kammala hukuncin da aka yi masa.
Sannan kotun za ta ƙwace dukkanin asusun ajiyarsa na banki da kuma na wasu 'yan uwansa da dama har ma da kadarorin da ya saya da kuɗin da ya karkatar.
Kotu ta tuhumi ministan lafiya a Zimbabwe da karkatar da kuɗin yaƙi da korona
Asalin hoton, EPA
An bayar da belin ministan lafiya na ƙasar Zimbabwe a yau Asabar bayan ya bayyana a gaban kotu bisa zargin rashawa.
An kama Obadiah Moyo ne ranar Juma'a bayan 'yan adawa sun sako gwamnati a gaba da kuma a shafukan sada zumunta game da zargin cin hanci da rashawa kan sayo kayayyakin yaƙi da cutar korona a ƙasar.
Moyo ya fuskanci tuhuma kan rashawa da ta kai dala miliyan 20 na kwangilar da aka bai wa wani kamfanin ƙasar Hungary, wadda aka yi zargin cewa ba a bi ƙaida ba.
Har yanzu gwamnati ba ta ce komai ba.
Moyo ne na biyu da ya fuskanci tuhumar cin hanci daga cikin 'yan majalisar ministocin Shugaba Emmerson Mnangagwa.
Ya hallara a kotun cikin wata motar ƙasaita da gwamnati ta ba shi tare da rakiyar hadimansa, kamar yadda wakilin BBC a Harare, Shingai Nyoka ya bayyana.
Yayin shari'ar, an tuhume shi da laifuka daban-daban na karya ƙa'idojin ofishinsa sannan aka umarce shi da ya bayar da fasfonsa na tafiye-tafiye.
Ana sa ran zai sake bayyana a gaban kotun nan da ƙarshen watan Yuli.
Ma'aikata 1,000 sun kamu da korona a wata mahauta
Asalin hoton, AFP
Hukumomi a Jamus sun ce ma'aikata fiye da 1,000 ne suka kamu da cutar korona a wata mahauta da ke arewa maso yammacin ƙasar.
Hakan ya faru ne bayan an samu ƙarin mutum 226 ranar Asabar, a cewar Sven-Georg Adenauer, wani jami'in yankin.
"Cutar ba ta yaɗu sosai ba a tsakanin mazauna yankin," in ji shi, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na dpa ya rawaito.
An dakatar da aiki a mahautar mai suna Tönnies da ke arewacin Rhine-Westphalia da tsakar ranar Laraba.
Sojoji sun 'kashe masu garkuwa da mutane guda uku' a Filato
Asalin hoton, Nigerian Army
Masu garkuwa da mutane uku ne aka kashe a wani samame da rundunar sojojin Najeriya ta kai a yankin Ƙaramar Hukumar Qua'an Pan da ke Jihar Filato, a cewar hedikwatar tsaro da ke Abuja.
Wata sanarwa da hedikwatar tsaron ta fitar yau Asabar ta ce dakarun musamman na rundunar Operation Accord mai yaƙi da garkuwa da mutane a arewa maso yamma da kuma tsakiyar Najeriya ne suka kai harin ranar Juma'a.
Ta ƙara da cewa an samu nasarar ceto wasu da aka yi garkuwa da su sannan ta kwace bindiga guda biyar da babur ɗaya da wayar salula ɗaya daga hannun mutanen.
Kazalika a dai wannan rana, rundunar ta yi nasarar kama wani mai garkuwa da mutane mai suna Alhaji Idris da kuma wasu mutum uku a Ƙaramar Hukumar Riyom da ake zargi da yin garkuwa da wani mai suna Abdullahi Abdullahi.
Sanarwar ta ce an miƙa mutanen ga hukumomin da suka dace domin ɗaukar mataki na gaba.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Ana zargin mahaifi da cin zarafin 'yarsa mai shekara bakwai a Najeriya
Asalin hoton, Getty Images
Kwamishinar Harkokin Mata ta Jihar Oyo ta ce gwamnatin jihar ta ceto wata yarinya 'yar shekara bakwai, wadda mahaifinta ya riƙa cin zarafinta ta hanyar duka da gallazawa.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito Kwamishina Alhaja Faosat Sanni tana siffanta lamarin da "dabbanci ga ƙaramar yarinya" a wata sanarwa da ta fitar ranar Juma'a.
Kwamishinar ta ce an kama mahaifin ne bayan kwamitin karɓar ƙorafe-ƙorafe kan lalata da cin zarafi na ma'aikatarta ya samu rahoto.
Ta ce: "Mun samu rahoton cin zarafin ne ta kafar sada zumunta na wani da ke zaune a yankin."
Ta ci gaba da cewa: "Ana zargin mahaifin yarinyar da ke zaune a Bodija na birnin Ibadan da zargin ji wa 'yarsa ciwo, wadda sakamakon haka ta samu tabo da kumburi a jikinta.
"Sannan an rawaito cewa mutumin wanda yake aikin gadi, yana azabtar da yarinyar bisa dalilin da har yanzu ba a kai ga ganowa ba.
"Kazalika mun samu labarin cewa mahaifiyarta ta tafi garinsu a Jihar Akwa Ibom domin ta haihu, inda ta bar wa mijinta yarinyar."
Kwamishinar ta ƙara da cewa an kai yarinyar asibitin yara na Oni and Sons da ke Ibadan domin duba lafiyarta, yayin da ma'aikatar ke niyyar ba ta duk tallafin da ya dace.
Saudiyya za ta sassauta dokar kulle daga ranar Lahadi
Asalin hoton, Getty Images
Saudiya ta ce zata cire dokar kulle a fadin kasar tare bude harkokin kasuwanci nan da ranar Lahadi, a wani matakin sassauta dokar duk da cewa ana kara samun masu kamuwa da cutar.
Za a janye dokar kullen daga karfe 6:00 safe na kasar tare da barin ci gaba da sallah a masallatai da bude kasuwanni a kasar.
Jiragen kasa da kasa za su ci gaba da kasancewa a dakace, an kuma hana taron sama da mutum 50 a waje daya, in ji gwamnatin kasar.
Har yanzu hukumomin kasar ba su bayyana ko za a yi aikin hajji wannan shekarar ba, wanda kusan mahajjata miliyan biyu ne ke zuwa ko wacce shekara a fadin duniya.
Har yanzu ana samun masu kamuwa da cutar korona a Saudiyya, wadda ke da sabbin masu cutar da suka kai 3,941 cikin sa'a 24, wanda ya kai adadin masu cutar a kasar 154,233.
Har zuwa ranar Asabar, kasar na samun masu cutar korona sama da 4,000 kwana shida a jere.
Akwai wadanda suka mutu 1,230 ya zuwa yanzu a kasar, tare da karin sanar da mutum 46 a ranar Asabar.
A karon farko Fafaroma Francis ya yi bayani bayan sassauta dokar kulle
Asalin hoton, EPA
Fafaroma Francis ya yi godiya ga likitoci da ma'aikatan jinya game da irin rawar da suka taka a Italiya wajen yaki da annobar korona, a wani bayani na farko da ya yi tun bayan fara sassauta dokar kulle da aka yi a kasar.
Fafaroma ya matukar nuna godiyarsa ga ma'aikatan lafiyar kasar, da suka yi aiki a Lombardy da ke yankin arewacin Italiya wanda ya zama daya daga cikin inda cutar ta yi matukar kamari.
"Kun zama daya daga cikin wasu dirkokin da suka ba da gudunmawar kasar nan ta tsaya da kafafuwanta," Fafaroma ya shaida wa wakilcin da suka je wajensa a dakin taro na Clementine da ke fadar Vatican.
Matakan dokar kullen an sassauta su ne a ranar 3 ga watan Yuni a kasar, wadda mutum 34,000 suka mutu sakamakon cutar a kasar, ciki har da 238,000 da aka tabbatar suna dauke da cutar ya zuwa yanzu, kuma mafiya yawansu a Lombardy suke.
Za a bude filayen wasan kwallon kafa a Faransa ga magoya baya 5,000
Asalin hoton, Getty Images
Za a fara barin magoya bayan wasanni a Faransa su rika shiga kallo daga 11 ga watan Yuli, in ji gwamnatin kasar, a kokarin da take na sassauta dokar kullen da aka kakaba saboda korona.
Amma za a bar mutum 5,000 ne kawai su rika shiga kallon da farko, kuma ana sa ran za a kara adadin daga baya.
"Za a kara fitar da wasu sabbin hanyoyin shawo kan cutar nan da tsakiyar watan Yuni tare da duba yiyuwar kara sassautawa a karo na biyu cikin Agusta," in ji gwamnatin.
Wannan sanarwar na nufin za a ci gaba da buga wasannin French Cup da League Cup a gaban masoya kwallo - duka gasar biyu an dakatar da su ne sakamakon annobar korona.
An soke gasar French League ne a watan Afirilu, kuma yadda jerin jadawalin kungiyoyin yake haka aka tsayar da shi.
PSG da ke saman tebirin da tazarar maki 12 kan tsayar da gasar ce aka bayyana a matsayin wacce ta lashe gasar, yayin da Amiens da Toulouse aka bayyana su a matsayin wadanda suka fada rukuni na biyu na gasar.
Yara hudu 'yan gudun hijirar Syria sun mutu a Jordan
Yara hudu ne suka mutu yan asalin Syria bayan wata gobara da ta tashi a inda suke zama a kusa da Amman babban birnin Jordan.
Jami'ai a Jordan sun ce yaran 'yan uwa ne daya bai wuce shekara daya ba dayan kuma 10.
Gobar ta kama ne a wani sansani da aka hada da tantuna ga manoman da ke aiki a kudancin Amman.
Mafi yawa daga cikin 'yan gudun hijirar Syrian da suka kai 650,000 na zaune a Jordan ne suna aikin leburancin noma.
Sojojin Najeriya sun ce sun kashe 'yan Boko Haram a Borno
Asalin hoton, Nigerian Army
Hedikwatar rundunar tsaro ta sojojin Najeriya da ke Abuja ta ce dakarun rundunar musamman ta Operation Lafiya Dole sun kashe mayaƙan ƙungiyar Boko Haram da dama a kusa da dajin Sambisa da ke Jihar Borno.
A wata sanarwa da ta wallafa a yau Asabar, rundunar ta ce jiragen yaƙinta sun kai harin ne ranar Laraba, inda suka yi nasarar lalata wata tankar yaƙi ta mayaƙan amma ba ta faɗi adadin waɗanda ta kashe ba.
Kazalilka ba ta bayyana rauni ba ko halaka daga ɓangaren nata dakarun.
A makon nan ne shugabannin rundunar tsaron suka gana da Shugaba Muhammadu Buhari, inda rahotanni ke cewa shugaban ya ja kunnensu da cewa sai sun zage dantse.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
An kama mutum 50 masu safarar mutane a Bangladesh
Jami'an 'yan sanda a Bangladesh sun ce sun kama sama da mutum 50 da ke da alaka da safarar mutane biyo bayan mutuwar wasu 'yan cirani 30 a Libya a watan jiya, wadanda yawancinsu 'yan kasar Bangladesh ne.
An nemi kudin fansa daga 'yan uwansu bayan an sace su a yakin da ake a kasar da ke arewacin Afrika, yanzu hukumomi a Bangladesh na daukar hukunci kan wadanda aka ce sun taimaka musu tsallakwa Libyan.
Wadanda ake tsare da su ana zargin su ne da karbar kudi daga mutane tare da yi musu alkawarin ayyukanyi.
Bangladesh na daga cikin kasashen da ke samar da 'yan cirani a duniya.
Breonna Taylor:Za a kori dan sandan da ya kashe bakar fatar Amurka
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, An harbi Mr Taylor sau takwas lamarin da ya yi sanadin mutuwarta
Hukumomi a birnin Louisville na jihar Kentucky da ke Amurka sun ce za a kori dan sandan da ke da hannu a kisan budurwar nan bakar fatar kwanakin baya.
'Yan sandan sun harbi Ms Taylor, mai shekara 26, sau takwas lokacin tana bacci a dakinta yayin da suka shiga gidansu ranar 13 ga watan Maris.
Sun je gidan ne domin yin samame kan zargin da aka yi cewa an boye miyagun kwayoyi a cikinsa, lamarin da aka gano babu kanshin gaskiya a cikinsa.
Lokacin da suka shiga gidan, sun yi musayar wuta da saurayin Ms Taylor, wanda ya yi zaton barayi ne suka shiga gidan.
Magajin birnin Louisville Greg Fischer ya ce Brett Hankison, daya daga cikin 'yan sandan da suka harbe ta, zai rasa aikinsa. An dakatar da sauran daga aiki
Masu fafutukar 'yancin bakar fata sun yi ta zanga-zangar neman a hukunta mutanen a suka kashe Ms Taylor.
Mayor Fischer bai yi cikakken bayani kan matakin da suka dauka na korar Mr Hankison daga aiki ba.
Asalin hoton, POLICE HANDOUT
Bayanan hoto, Hukumomi sun ce za a kori Brett Hankison daga aiki
Halin da ake ciki game da korona a Latin Amurka
Kamar yadda muke kawo muku bayanai kan cutar korona a duniya, Yanzu yankin Latin Amurka ne ke fama da karuwar masu cutar, ga kuma yadda annobar take kara yaduwa a cikin manyan kasashen yankin.
Wadanda aka tabbatar na da cutar a Brazil sun haura miliyan daya, yayin da sama da mutum dubu 54 suka mutu cikin awa 24.
Mexico ta zama kasa ta bakwai da a hukumance ta sanar da mutuwar mutane sama da 20,000 da ke da alaka da wannan annoba.
Chile da Peru suma na fuskantar karuwar masu kamuwa, yayin da ko wacce daya cikin su ta tabbatar da kamuwar sama da mutum dubu 230.
Ministan lafiya a Zimbabwe Obadiah Moyo, zai bayyana gaban kotu a yau bayan an kama shi a ranar Juma'a sakamakon zargin cin hanci da ke da alaka da almundahana kan siyo wasu kayan asibiti dan yaki da cutar Covid-19.
Gwamnatin Harare na fuskantar matsin lamba a kafafen sada zumunta daga 'yan adawa, bayan ta bai wa wani kamfani da aka kafa kasa da kwana 70 (Drax Consult SAGL) kwagilar siyo kayan kariyar cutar korona da suka kai na dala miliyan 20, kai tsaye ba tare da bin hanyoyin ba da kwangila ba.
'Yan adawar sun yi alawadai da wannan al'amari.
Mista Moyo shi ne minista na biyu karkashin gwamnatin shugaba Emmerson Mnangagwa da bata fi shekara uku ba, da yake fuskantar tuhumar cin hanci da rashawa.
Asalin hoton, EPA
Bayanan hoto, Zimbabwe na fama da koma bayan tattalin arziki - ko aranar laraba sai da ma'aikatan lafiya suka yi zanga-zangar neman karin kudi
An kama 'yan adawa da dama a Belarus sakamakon zanga-zanga
Asalin hoton, EPA
Kungiyar kare hakkin dan adam a Belarus ta ce an kama akalla mutum dubu 120 a fadin kasar ranar Juma'a, yayin wata zanga-zanga da ke da alaka da kama wasu masu fafutuka da kuma 'yan hamayyar siyasa.
An kuma fi yin kamen ne a babban birnin kasar Minsk. Amma an saki wasu da dama yanzu.
Ranar juma'a ita ce ranar karshe daga aka dibarwa 'yan takarar shugaban kasar da su sami amincewa daga wasu domin samun damar shiga takarar zaben da za a yi a watan Agusta.
Sai dai hukumomi na ta kokarin dakile wasu da za su iya zama kalubale ga shugaban da ke ci yanzu, Alexander Lukashenko, wanda ke shugabantar kasar shekara 26 baya.
A ranar Alhamis, aka kama babban abokin hamayyarsa, Viktar Babaryko, kan zargin kaucewa biyan haraji da halasta kudaden haram.
Lardin yammacin Australia ya kara tsaurara dokar kulle
Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Jihar Victoria da ke Australia ta ruguje shirinta na sassauta dokar kullen da aka sanya saboda annobar korona sakamakon karuwar masu kamuwa da cutar.
Yawan masu cutar a Victoria ya karu da 25 zuwa 1,817 ranar Asabar, wanda shi ne adadi mafi yawa da aka samu cikin wata guda.
Gwamnan lardin Daniel Andrew ya ce karuwar masu cutar na nufin shirin sassauta dokar tare dokar ba da tazara in an bude kasuwa zai samu tsaiko har zuwa 12 ga watan Yuli.
Za a hana taruwar mutane sama da biyar a gida daya har sai wannan lokacin da aka kayyade, in ji shi.
Andrew ya nuna fusatarsa game da kara wa'adin yana mai zargin haduwar da iyalai ke yi akai-akai da ta'azzara cutar.
Mutuwar mutum 20,000 ta hana sake bude kasuwanci a birnin Mexico
Asalin hoton, Getty Images
Mexico ta dakatar da shirinta na sake bude harkokin kasuwanci har sai adadin masu kamuwa da cutar korona ya ragu, kamar yadda magajin garin ya bayyana.
Birnin dai ya yi fatan sake bude otel-otel da wuraren cin abinci da kuma manyan kantunan zamani a wani mataki na sassauta dokar kulle da aka kakaba.
Amma a ranar Asabar magajin garin Claudia Sheinbaum, ya ce za a rufe birnin ruf cikin dokar kulle - har sai zuwa makon gobe.
Ya zuwa ranar Juma'a, mutane sun cika gadajen asibiti da kusan kaso 65, kuma rashin raguwar masu kamuwa da cutar ba zai bari a sake bude kasuwanni ba.
Har yanzu annobar korona bata kai makurarta ba a Mexico, yayin da adadin wadanda suka mutu sakamakon cutar ya haura 20,000 ya zuwa ranar Juma'a, daya daga cikin mace-mace masu yawa a duniya.
Mexico ta tabbatar da sama da mutum 170,000 da suka kamu da cutar ya zuwa yanzu, kuma ana zaton adadin zai zarce hakan saboda karacin kayan gwaji.