Zanga-zangar Katsina: 'Yan sanda sun saki Nastura Ashir
Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye dangane da irin wainar da ake toyawa a fadin duniya musamman batutuwan da suka shafi annobar korona na ma karin wasu daban.
Rahoto kai-tsaye
Nasidi Adamu Yahaya, Halima Umar Saleh and Mustapha Musa Kaita
Rufewa
Bayani kan maƙala
Marubuci, Mustapha Musa Kaita
Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multi-Media Broadcast Journalist
Masu bibiyarmu a wannan shafin a daidai wannan lokaci muka kawo ƙarshen kawo muku labarai da rahotanni kai-tsaye, sai kuma gobe idan Allah ya kai mu za mu ci gaba da kawo muku wasu labaran a wannan shafin.
Za ku iya duba ƙasa domin karanta wasu labaran da muka wallafa.
Ɓarayi sun yi sata a ofishin ‘yan sanda a Ghana
Asalin hoton, Getty Images
Hukumomi a ƙasar Ghana sun fara
bincike don gano dalilin da ya sa wasu da ake kyautata zaton ɓarayi ne suka
kutsa kai ofishin ‘yan sandasuka yi sata.
Barayin dai sun fasa ofishin 'yan sandan ne da ke garin Nima, inda suka yi awon gaba da wasu
kayyayaki ciki har da talabijin da kwamfiyutoci.
A cewar hukumomin ‘yan sandan
kasar dai kawo yanzu babu wanda suka kama, lamarin dai ya girgiza ‘yan sandan
da suke aiki lokacin da al’amarin ya afku.
An yanke wa 'yan sanda 4 hukuncin zaman gidan yari na shekaru 20
Wata kotu a Mozambique ta yanke wa 'yan
sanda huɗu hukuncin ɗaurin sama da shekaru 20 bayan kama su da laifin kisan
wani mai sa ido kan zaɓen da aka yi bara a kasar.
An harbe Anastacio Matavele a garin Zai-Zai da ke kudancin Mozambique.
Masu bincike sun ce an harbi motarsa har
sau sha uku, an kuma kama 'yan sandan a lokacin da suka yi taho mugama da wata
mota yayin ƙoƙarin guduwa daga inda abin ya faru.
Ana
samun rahotannin kisa ko garkuwa da masu fafutuka da 'yan jarida da kuma 'yan
adawa a Mozambique, ana kuma zargin yaran ƙusoshin 'yan siyasa da aika aikar.
Zanga-zangar Katsina: 'Yan sanda sun saki Nastura Ashir
Asalin hoton, YB Multimedia
Gamayyar Kungiyoyin Arewacin Najeriya,Coalition of Northern Groups (CNG), ta tabbatar da sakin shugaban kwamitin amintattu na ƙunigyar wato Nastura Ashir Sharif bayan ya shafe kwanaki biyu a hannun 'yan sanda.
A sanarwar da mai magana da yawun gamayyar kungiyoyin, Abdul-Azeez Suleiman ya sanya wa hannu, an saki Nastura ne sakamakon matsin lamba da ƙungiyarsu ta yi wa gwamnati tare da Ƙungiyar Dattawan Arewa da wasu kuma masu faɗa a ji na arewacin Najeriya da dai sauraren ƙungiyoyi.
A hirarsa da BBC, Abdul-Azeez Suleiman, ya shaida wa BBC a ranar Laraba cewa an kama Ashir Sharif ne bayan sun kammala zanga-zanga a birnin Katsina inda suka yi kira a ɗauki mataki game da kashe-kashen da ke faruwa a yankin.
Hajjin 2020: Nijar ta soke zuwa Aikin Hajjin bana
Gwamnatin jamhuriyyar Nijar ta ce ta dauki matakain cewa asar ba za ta je Aikin Hajjin bana ba saboda annobar cutar korona.
Ta dauki wannan matsaya ne bayan ta yi wata ganawa da masu ruwa da tsaki kan sha'anin Aikin Hajj da Umara don bayyana musu matsayar ƙasar game da tafiya hajjin na 2020 a ranar Alhamis.
Gwamnatin ta ce hakan na zuwa ne bayan da ta yi nazari kan sharuɗɗan da hukumomin Saudiyya suka gindaya.
Gwamnatin ta kuma kira ga masu kamfanonin zirga-zirga Aikin Hajji da su daina karbar kuɗin mutane, su kuma biya basussukan da ke kansu don bai wa hukumar da ke da alhakin shirya Aikin Hajji da Umara damar ita ma ta biya masu kamfanonin jiragen sama da ke bin ta bashi.
Alhaji Bukari Sani Zilly shi ne wakilin kampanin MaxAir ya bayana wa Wakiliyarmu Tchima Illa Issoufou dalilan da suka kai gwamnatin Nijar ga daukar wannan mataki.
Ga yadda hirarsu ta kasance da Tchima Illa Issoufou:
Bayanan sautiHira da wakilin Maxair a Nijar
Trump ya sha kaye a Kotun Koli kan matakin bai wa 'yan ci rani kariya
Shugaba Donald Trump ya sha kaye, bayan da Kotun Kolin Amurka ta dakatar da matakin da ya dauka na soke shirin tsohon Shugaba Obama na bai wa 'yan ci rani kariya.
Kafin saukar Mr Obama ne ya kirkiro da shirin ba da kariya ga wadanda suka shiga kasar ta haramtacciyar hanya a lokacin da suke kanana.
Matakin Kotun Kolin na nufin zama Amurka daram ga sama da 'yan ci rani dubu dari biyar ne da suka zo daga kasashen Latin Amurka, kuma za a basu takardun damar neman ayyuka tamkar 'yan kasa.
A martaninsa, Mr Trump ya bayyana hukuncin a matsayin mai cike da takaici da ban tsoro.
Ya kara da cewa abunda ya rage shine hana yan Amurka hakkinsu na mallakar makami, matsawar bai koma kan mulki ba ya nada sabbin alkalai.
A yanzu gwamnatin Trump za ta nemi wata hanya ta daban don kawowa shirin cikas, to amma kuma lokaci na kure mata ganin cewa a watan Nuwamba ne za a gudanar da zabe.
Asalin hoton, Getty Images
Buhari ba ya ɗaukar shawara - Bashir Tofa
Ku latsa hoton da ke kasa don kallon bidiyon bayanin da tsohon dan takarar shugaban Najeriyar a 1993 ya yi.
Bayanan bidiyo, Hira da fittacen dan siyasa Bashir Usman Tofa
An wallafa littafi kan haramta horo mai tsanani ga yara
Wata ƙungiya mai suna Global Initiative ta wallafa littafi da harsuna 15, ciki har da Hausa kan batun haramta duk wani horo mai tsanani ko kuma gallazawa ga yara.
Littafin na ɗauke da amsoshi kan tambayoyi masu yawa game da dalilan da aka bayar na hana horo ga yara.
Babbar jami’ar ƙungiyar a nahiyar Afirka, Dr Sonia Vohito, ta ce:“Wannan littafin zai bai wa iyaye da masu raino, da jami’an gwamnati, da masana kan ilimi, da kuma sauran mutane da ke fafutukar ganin an hana gallaza wa yara ƙwarin gwiwar ɗaukar mataki na shari’a sannan su tabbatar da ganin yara sun samu kariya daga dukkan na’uka na gallazawa”.
An fara wallafa littafin ne a 2009, amma a halin yanzu an buga shi zuwa harsuna 15 ciki har da Hausa.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Kocin Manchester ya jinjina wa Rashford kan taimakon marasa ƙarfi
Asalin hoton, Getty Images
Kocin Manchester United Ole Gunner Solskjaer ya jinjina wa ɗan wasan gaban kulob dinsa Marcus Rashford kan ƙoƙarin da ya yi wajen tallafa wa yara 'yan makaranta lokacin annobar korona.
A ranar Talata ne dai Rashford ya nemi a tallafa wa yara da miliyan 1.3 domin samun abinci kyauta a lokacin wannan bazarar.
Tuni ɗan wasan na Manchester ya tara fam miliyan 20 domin kai abinci ga marasa ƙarfi.
Musulmin Uighur: China ta yi barazanar ɗaukar mataki kan Amurka
China ta yi barazanar ɗaukar mataki a kan Amurka bayan da Shugaba Trump ya rattaɓa hannu kan wata sabuwar doka da ta ba da izini a riƙa zaɓe ana sanya takunkumi kan wasu manyan jami'an jam'iyyar kwaminisanci, kan wasu manufofinsu da ke uzzura wa Musulmin ƙasar marasa rinjaye.
An ɓullo da dokar ne da nufin hukunta jami'ai da kuma kamfanoni da ke da hannu wajen tsare mutane da dama 'yan kabilar Uighur a sansanonin tsare jama'a, matakin da hukumomin China ke cewa suna ɗauka ne a wani ɓangare na yaƙi da ta'addanci.
Babban Bankin Ingila ya ware biliyan $120 don ceto tattalin arziƙin ƙasar
Babban Bankin Ingila ya ware dala biliyan
120 a wani yunƙuri na ceto tattalin arzikin Birtaniya daga shiga mayuwacin
hali.
Wakilin BBC ya ce bankin Ingila ya bayyana
makomar tattalin arzikin Birtaniya da ma na duniya a matsayin wanda bai da
tabbas, inda ya ce "zai dogara ne ga yadda abubuwa suka sauya bayan wucewar
annobar korona''.
Birtaniya na daga cikin ƙasashen da suka
tsunduma cikin matsin tattalin arziƙi saboda ɓarkewar annobar korona.
To amma bankin ya ce ba lalle bane annobar
ta jefa tattalin arziƙin cikin matsanancin halin da ake hasashe.
Tunda
farko bankin ya yi gargaɗin cewa za a iya fuskantar matsin tattalin arziƙi a
Birtaniya mafi muni a cikin sama da shekaru 300.
Me ya sa gumaka suke da muhimmanci, kuma ake kafa su a manyan birane?
An yi ta karya gumaka ko mutum-mutumi a wasu sassa na duniya a makon da ya gabata... amma mene ne muhimmancinsu muka me ye amfanin kafa su?
Ku latsa hoton da ke kasa don kallon bidiyon:
Bayanan bidiyo, Me ya sa gumaka suke da muhimmanci?
Ana zargin kifi na kara yaduwar cutar korona a China
Asalin hoton, Getty Images
A cikin makon da ya gabata an ga karuwar masu kamuwa da cutar korona a birnin Beijing na China - wadanda aka alakan su da wata babbar kasuwar sarin kayan abinci.
Kafar yada labaran kasar ta ce an gano kwayar cutar a katakwayen yanka kayan abinci da aka yi amfani da su wajen yanka kifi dangin salmon a kasuwar Xinfadi - abin da ya jawo fargabar a kasar.
Manyan kantuna da wuraren cin abinci sun yi gaggawar fitar da kifin daga shagunansu, an kuma dakatar da shigar da kifin kasar da Turai.
A ranar Laraba ne aka sanar da cewa an gano wani mutum mai shekara 22 dauke da cutar, wanda ke aikin wanke kifi - a garin Tianjin da ke kusa da Beijing.
Amma hukumar da ke kula da dakile yaduwar cututtuka ta China ta ce ba zai yiwu a ce kifi na dauke da cutar ba.
Asalin hoton, Glenna Gordon
Babbar Kotun Uganda ta yanke hukuncin cewa za a bar fursunoni da 'yan kasar mazauna kasashen waje su kada kuri'unsu a zabuka masu zuwa.
Wani lauya Stephen Kalali ne ya gabatar da korafi shekara biyu da suka wuce, an kuma yanke hukuncin a ranar Laraba.
Ya ce hana wadannan mutane yin zabe take hakkinsu na 'yan kasa ne.
Hukumar zaben kasar ta ce babu wani tsarin doka da ya tanadar wa mutanen da ke zama a wasu kasashen ko a gidan yari damar yin zabe.
Alkalin ya ce cire wadannan mutane daga masu yin zabe na nuna cewa hukumar zaben tana yin abin da ya kauce wa hakkokin 'yan kasa da kundin tsarin mulki ya ba su.
A shekarar 2021 ne Uganda za ta yi manyan zabukan kasar.
Annobar cutar korona ta matukar shafar shirye-shiryen wannan zabe, inda aka haramta manyan taruka.
Otel-otel a Afrika za su fuskanci koma baya saboda coronavirus
Asalin hoton, Getty Images
Ana sa ran otel-otel a fadin nahiyar Afrika za su fuskanci koma baya da kashi 40 cikin 100, saboda annobar cutar korona.
An samu gagarumin sauyi idan aka hada da hasashen da aka yi na bunkasar kasuwar bangaren otel-otel a bana.
A farkon wannan shekarar, wasu kungiyoyi sun shirya gina otel 408 a Afrika, masu dakuna 78,000.
Sai dai masu sharhi sun ce ba za a samu cimma ko rabin wannan buri ba a bana.
An haramta goyo a babur a Kano
Gwamnatin jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta haramta yin goyo a
kan babur mai kafa biyu a daukacin jihar.
Shugaban
hukumar kula da zirga-zirga a titunan Kano ta KAROTA Baffa Babba Dan
Agundi ya shaida wa BBC cewar an dauki matakin ne kasancewar wasu mazauna jihar
na kokarin dawo da sana’ar achaba a jihar.
Dokar ta hana yin goyo a kan babur mai kafa biyu ta fara aiki
ne daga yau Alhamis.
Sai dai masu Babura a jihar ba su ji dadin wannan doka ba.
Amma shugaban hukumar ta KAROTA Bappa Babba Dan agundi ya ce gwamnati ba wai ta
dauki wannan mataki ba ne don takurawa al’umma, illa sai don ta yi maganin masu
daukar mutane a kan babura suna shigo da su ta barauniyar hanya duk kuwa da dokar
hana hsiga da fita da ke aiki a jihar.
A shekarar 2013 ne dai gwamnatin jihar ta Kano ta
fara kafa dokar hana daukar mutane a babur mai kafa biyu sakamakon matsalar
tsaro ta hare-haren Boko Haram da jihar ta yi fama da ita a wancan lokacin.
Faransa ta zargi Amurka da lalata shirin kaddamar biyan harajin dijita
Asalin hoton, Getty Images
Faransa ta zargi Amurka da lalata shirin kaddamar biyan harajin dijita, a lokacin da ake dab da kulla yarjejeniya.
A cewar wakilin BBC ''Ministan kudin Faransa Bruno Le Maire ya zargi kamfanonin intanet da mafi yawancinsu a Amurka suke da ci da gumin kwastomomi miliyan 450 ta hanyar kin biyan haraji yadda ya kamata.''
A kan haka ya ce idan har gwamnatin Amurka ta ki ba su hadin kai to Faransa za ta fito da nata tsarin na kashin kanta.
Dama gwamnatoci da dama na korafin cewa kamfanoni kamar Amazon da Facebook na anfani da wani tsari mai rudani don kauce wa biyan haraji a kasashen da suke gudanar da ayyukansu.
To amma kamfanonin sun musanta zargin.
Gwamnatin Amurka na ganin cewa tun da a nan aka samar da kamfanonin, to kuwa dole a kyale su su fara biyan haraji a gida kafin su biya a waje.
Sojoji a Kamaru sun kashe 'yan aware 24
Sojoji a Kamaru sun ce sun kashe mayakan
yan aware 24 yayin wani hari a yankin masu mnfani da harshen Ingilishi.
Janar Valere Nka ya sanar da cewa an kashe 13 daga ciki a wani hari da aka shafe kwanaki biyar ana kai wa kan hanyar
da ke makwabtaka da Najeriya.
Sanarwar ta kuma ce soja guda ya rasa
ransa a bata kashin.
Mutun 3,000 suka mutu tsawon
shekaru uku da ake tashin tashinar, yayin da dubu 700 suka rasa
matsugunansu.
'Yan
awaren na ƙokarin ɓallewa ne don kafa sabuwar ƙasa da suke kira Ambazonia.
Jama'atu Nasril Islam ta koka kan matsalar tsaro a arewacin Najeriya
Kungiyar Jama'atu Nasril Islam da ke karkashin mai alfarma Sarkin Musulmin Najeriya ta koka kan halin rashin tsaro da ake fama da shi a wasu sassan arewacin kasar.
A wata sanrwa da kungiyar ta fitar, ta yi kira ga gwamnatin Najeriya ta dauki kwararan matakan kawo karshen hare-haren da ake fama da su a yankin, tana mai cewa alkawuran da gwamnatin ke yi ba tare daukar wani mataki ba ba za su taba wadatarwa ba.
Dr. Khalid Aliyu shi ne babban sakataren kungiyar wanda kuma shi ne ya sa hannu kan sanarwar, daga Abuja Yusuf Ibrahim Yakasai ya nemi karin bayani daga gare shi kan abin da sanarwar ta kunsa.
Ga yadda hirar tasu ta kasance, sai ku latsa alamar lasifikar da ke kasa don sauraro:
Bayanan sautiHira da Dr. Khalid Aliyu na JNI kan matsalar tsaro a arewacin Najeriya
An yankewa mutum uku daurin rai da rai a Pakistan kan kisan dan siyasa
Kotu a Pakistan ta yankewa wasu mutum uku daurin rai da rai saboda kama su da laifin kisan wani dan siyasar kasar a birnin London.
An dabawa Dr Imam Farooq wuka a wajen gidansa da ke birnin London a shekarar 2010.
Mr Farooq jagora ne a jam'iyyar Muttahida Qaumi Movement, kuma 'yan sanda na ganin an kashe shi ne saboda hamayyar siyasa.
To amma 'yan sandan Burtaniya sun gabatar wa kotun Pakistan da shaidun kisan nasa bisa sharadin cewa ba za a aiwatar da hukuncin kisa kan wadanda ke da alhaki ba.
Dama tun a shekarar 1990 ne ya'yan jam'iyyar MQM suka rika tserewa zuwa Burtaniya, a lokacin da jami'an tsaro suka takura musu a Pakistan.