Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Zanga-zangar Katsina: 'Yan sanda sun saki Nastura Ashir

Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye dangane da irin wainar da ake toyawa a fadin duniya musamman batutuwan da suka shafi annobar korona na ma karin wasu daban.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya, Halima Umar Saleh and Mustapha Musa Kaita

  1. Amurka ta sake ƙaƙabawa Syria takunkumin tattalin arziki

    Amurka ta sake ƙaƙabawa Syria takunkuman tattalin arziki masu tsanani da nufin hana gwamnatin Bashar al-Assad harkokin kasuwanci da kasashen waje.

    Matakan wadanda suke cikin daftarin dokar Caesar Act, na son gwamnatin ta dakatar da ''mummunan ta'addancin da take yi'' kan fararen hula ta kuma yarda da miƙa mulki ga farar hula.

    A karon farko an tsoma matar Mista Assad, Asma cikin lamari irin wannan.

    Amma akwai fargabar cewa takunkuman za su sanya rayuwar 'yan Syria cikin matsala sosai.

    Kasar na cikin tabarbarewar tattalin arziki mai muni.

    Darajar kudinta ya fadi a kasuwar bayan fage, abin da ya sa farashin abinci da magunguna suka yi sama wanda hakan ke janyo zanga-zangar da ba a faye yi ba don nuna adawa da gwamnatin Shugaba Bashar al-Assad a yankunan da yake da iko.

    An kashe fiye da mutum 380,000 sannan mutum miliyan 11 sun rasa muhallansu tun bayan fara rikici a kasar a shekarar 2011.

  2. Labaran Duniya Cikin Minti Daya

  3. 'Yan hamayya sun yi kira da a yi zanga-zangar adawa da gwamnati a Mali

    Bangaren 'yan hamayya a Mali sun yi biris da bukatar Shugaba Ibrahim Boubacar Keita ta tattaunawa inda a maimakon haka suka yi kira ga mutane da su gudanar da zanga-zanga a ranar Juma'a.

    A ranar Talata ne Shugaba Keita ya ce ya shirya tattaunawa da gamayyar kungiyoyin hamayya a yayin da ake ci gaba da yin kira cewa ya yi murabus sakamakon gaza magance rikicin kabilanci da na masu ikirarin jihadi da ke ci gaba a arewacin kasar.

    Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ambato daya daga cikin fitattun 'yan hamayya mai fada a ji Imam Mahmoud Dicko, yana shaida wa wata kafar yada labaran kasar cewa shugaban kasar yana yin biris da bukatun mutane.

    ''Bai koyi darasi ba, ba ya saurarar mutane. Amma a wannan karon zai gane.''

    Dubban mutane ne suka gudanar da zanga-zanga a Bamako babban birnin Mali a farkon watan nan wacce Imam Dicko ya jagoranta, wanda ya dade yana kira da a tattauna da masu ikirarin jihadi.

    Fiye da dakarun kasashen waje 13,000 ne suke Mali don shawo kan rikicin kungiyoyin masu tayar da kaya a arewaci da tsakiyar kasar, da suka hada da masu ikirarin jihadi masu alaka da kungiyar al-Qaeda da kuma IS.

  4. Masu Coronavirus na karuwa a Afrika Ta Kudu bayan sassauta matakan kulle

    Shugaban kasar Afrika Ta Kudu Cyril Ramaphosa ya dauki matakin sassauta dokar kulle sakamakon tabarbarewar da tattalin arzikin kasar ke yi, sai dai ana samun karuwar masu kamuwa da cutar bayan sassauta matakan.

    Amma a wani jawabin ke-ke da ke-ke da ya gabatar wa 'yan kasar ya ce akwai bukatar ceto tattalin arzikin al'umma.

    A sakamakon hakan ya ce za a bude bangarorin yawon bude ido ma nan ba da dadewa ba.

    A karshen watan Maris, kasar ta shiga matakil kulle ma fi tsauri a duniya, ta yadda aka hana duk wata zirga-zirga da kuma haramta sayar da sigari da barasa.

  5. Labarai da dumi-dumi, COVID-19: Bankin Ingila zai sanya karin £100bn a harkokin tattalin arzikin kasar

    Bankin Ingila zai sanya karin £100bn a harkokin tattalin arzikin kasar domin taimaka mata farfadowa daga matsin da ta shiga sanadin cutar korona.

    Masu tsara harkokin kudi na bankin sun jefa kuri'a kan batun nda mutum 8 suka amince a zuba kudi, yayin da mutum 1 ya hau kujerar na ki.

    Kazalika bankin ya sanya kudin ruwa ya zama kashi 0.1.

  6. Buhari yana ganawa da jami'an tsaron Najeriya

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yana ganawa da hafsoshin tsaron kasar a fadarsa da ke Abuja, babban birnin kasar.

    Mai taimaka wa shugaban kasar kan shafukan sada zumunta, Bashir Ahmad ne ya bayyana hakan a sakon da ya wallafa a Twitter ranar Alhamis.

    Wannan ganawa na zuwa ne kwanaki kadan bayan wasu matasa sun yi zanga-zanga a jihar Katsina, mahaifar shugaban kasar, wacce ta dade tana fama da tabarbarewar tsaro.

    Masu lura da lamura da 'yan kasar suna zargin Shugaba Buhari da rashin yin abin da ya kamata wajen magance matsalar tsaron da ke addabar musamman arewacin kasar.

    A farkon makon nan, kungiyar kare hakkin Dan adam ta Amnesty International ta ce gwamnatin Najeriya ta gaza kare rayukan 'yan kasar a yayin da matsalar tsaro take ci gaba da yin kamari musamman a arewacin kasar.

  7. An fitar da fasinja daga jirgi saboda ƙin sa takunkumi

    A karon farko an fitar da fasinja daga jirgin American Airlines bayan ya ki sanya takunkumin kare fuska.

    An nemi Brandon Straka ya sauka daga jirgin da kansa kafin ya tashi daga birnin New York zuwa Dallas.

    Mutumin mai fafutukar kare muhalli - wanda yake da mabiya sosai a shafin Twitter -ya bayyana abin da ya faru da shi a wani bidiyo da ya wallafa, yana mai cewa matakin "rashin hankali ne."

    Da yake yi masa raddi, Astead Herndon - dan jaridar New York Times wanda yake cikin jirgin- ya kalubalanci Straka sannan ya wallafa bidiyon ainihin abin da ya faru.

    A halin da ake ciki babu wata doka da ta wajabta sanya takunkumi ga masu shiga jirgi a Amurka, amma an kyale kamfanonin jirage su tilasta wa fasinjoji bin dokokinsu.

  8. Barcelona na son riƙe Messi har 2023, Ronaldo na son komawa MLS

    Barcelona ta yi wa kaftin ɗinta ɗan ƙasar Argentina Lionel Messi, mai shekara 32 tayin sabuwar yarjejeniya domin ya ci gaba da murza leda a kulob din har 2023.(Mundo Deportivo via Metro)

    Dan wasan gaba na Sifaniya Pedro, mai shekara 32, ya amince ya koma Roma amma zai yanke shawarar ko zai tsawaita zamansa na ɗan wani lokaci aChelseahar zuwa ƙarshen kaka.(Guardian)

    Pedro ba ya son kammala kaka tare da Chelsea domin ba ya son a samu cikas kan komawarsa Roma.(The Athletic - subscription only)

    Dan wasan tsakiya dan kasar Scotland Ryan Fraser, mai shekara 26, yana son sama da fan £100,000 duk mako domin samun wakili bayan ya yi watsi da yarjejeniyar daBournemouthta taya masa kan ya ci gaba da taka leda har zuwa ƙarshen kaka.(The Times - subscription only)

    Kaftin ɗin Orlando City ɗan ƙasar Portugal Nani, mai shekara 33, ya ce tsohon ɗan wasan Manchester United kuma abokin wasansa a Portugal Cristiano Ronaldo, mai shekara 35, ya shaida masa cewa yana son ya taka leda a gasarMajor League Soccerta Amurka kafin ya yi ritaya.(ESPN)

  9. #NorthernLivesMatter: Bashir Tofa ya gargaɗi Buhari kan kama masu zanga-zanga

    Fitaccen dan siyasar nan na Najeriya, wanda ya tsaya takara a zaben 1993, Alhaji Bashir Usman Tofa, ya gargadi shugaban Najeriya da ya sa a saki shugaban kungiyoyin da suka yi zanga-zanga kan tabarbarewar tsaro a Arewacin kasa kafin matasa su hasala su soma tayar da hankali.

    Ranar Talata rundunar 'yan sandan ƙasar ta kama Nastura Ashir Sharif, shugaban kwamitin amintattunta na Gamayyar kungiyoyin Arewacin Najeriya, Coalition of Northern Groups (CNG) bayan sun yi zanga-zanga a birnin Katsina.

    Masu zanga-zangar, mai taken#ArewaIsBleeding a turance, wato 'Jini yana kwarara a Arewa', sun bayyana matuƙar ɓacin ransu kan halin ko-in-kula da suke zargi gwamnatocin kasar na yi kan yawaitar kashe-kashe a yankin.

    A sakon da ya fitar ranar Laraba tsohon dan siyasar ya yi kira ga shugaba Buhari da Babban Sufeton 'yan sanda da shugaban hukumar DSS "su yi gaggawa su sake shi [Nastura] domin idan samarin nan suka kufula suka fara barna a kasar nan, wallahi ba a san inda za ta tsaya ba."

    Alhaji Bashir Tofa ya kara da cewa "ba karamin rashin dabara ba ce, ba karamin rashin hikima ba ce" kama Nastura Ashir Sharif ganin cewa babu wanda ya tayar da hankali lokacin zanga-zangar.

  10. China za ta soke bashin-da-ba-ruwa da take bin kasashen Afirka

    Shugaban China Xi Jinping ya sanar cewa kasarsa za ta za ta soke basukan-da-ba-ruwan da take bin kasashen Afirka, wadanda suka kamata a soma biya a karshen 2020.

    Ya shaida wa mahalarta taron da ake yi ta intanet tsakanin China da Africa kan shawo kan cutar korona ranar Laraba cewa kasarsa za ta tsawaita lokutan biyan bashi mai ruwa da take bin kasashen Afirka da Covid-19 ta fi iya illa.

    Ya kuma bukaci cibiyoyin da ke harkokin kudin kasar da su gudanar da "tattaunawa irin ta abokai" da kasashen Afirka domin "tsara yadda za su ba su bashin kasuwanci".

    "China za ta hada gwiwa da Majalisar Dinkin Duniya, da Hukumar Lafiya ta Duniya da sauran kawayenta domin taimaka wa Afirka wajen yaki da Covid-19, kuma za mu yi hakan ne ta hanyar da Afirka take so," in ji Shugaba XI.

    A game da riga-kafin cutar korona, shugaban na China ya ce nahiyar Afirka za ta kasance daya daga cikin wadanda za su soma cin moriya idan kasarsa ta samu riga-kafin cutar. Ya ce China za ta ci gaba da gina asibitoci a Afirka.

    Ya kara da cewa za su gina cibiyar yaki da cutuka masu yaduwa ta Afirka a Addis Ababa, babban birnin Ethiopia.

  11. An ƙirƙiri fasahar da za ta amsa tambayoyinku da Hausa

    Wasu matasa dalibai 'yan asalin arewacin Najeriya da ke karatu a jami'ar Imperial College da ke birnin Landan sun kirkiri wata fasaha mai tunani irin na dan adam da suka yi wa lakabi da suna Amina.

    Fasahar wadda ta ci sunan sarauniya Amina ta Zazzau na amsa tambayoyi ne a harshen Ingilishi da na Hausa dangane da bayanai da suka shafi annobar korona.

    Amina dai ba batun-butumi ba ce wato mai zati irin na dan adam, fasaha ce mai kwakwalwar dan adam da ake tattaunawa da ita a kan intanet da ake kira 'chatbot'. Za a iya cewa Amina ce fasahar bot irinta ta farko da aka kirkira da harshen Hausa.

    Al-amin Bugaje wanda daya ne daga cikin wadanda suka kirkiri wannan fasaha, ya shaida wa BBC cewa "abu na gaba da muke son yi shi ne samar da damar aikewa da sakon murya ga Amina maimakon rubutu."

    Latsa wannan alamar lasifika da ke ƙasa domin sauraron Al-amin Bugaje

  12. APC 'za ta sha kaye a zaɓen 2023 idan bata gyara gidanta ba'

    Masana harkokin siyasa a Najeriya sun yi hasashen cewa jam'iyyar APC za ta shaya kaye a zaben 2023 idan bata yi gaggawar dinke barakar da ke cikinta ba.

    Jam`iyyar APC mai mulkin kasar ta fada cikin rikicin, har ta kai ga mutum biyu na ikirarin shugabancin jam`iyyar.

    Kuma lamarin y araba kan manyan `ya`ya da kananan magoya bayan jam`iyyar.

    Wasu dai na ganin rashin tsoma bakin Shugaba Muhammadu Buhari a cikin al`amuran jam`iyyar na cikin manyan dalilan da suka jefa ta cikin wannan rudani, wanda suke cewa idan jam`iyyar ba ta gaggauta kintsa gidanta ba, da wuya ta yi tasiri a zaben 2023.

    Ku latsa alamar lasifika da ke kasa don sauraren rahoton Ibrahim Isa:

  13. Buɗewa

    Nasidi AdamuYahaya ne yake yi muku barka da warhaka.

    Muna fatan ku kasance tare da mu tsawon wannan rana domin sanin halin da duniya take ciki.

    Za mu kawo muku labarai da rahotannin da suka shafi rayuwarku, musamman kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da makwabtansu, har ma da sassan duniya.