Shugaba Donald Trump ya sha kaye, bayan da Kotun Kolin Amurka ta dakatar da matakin da ya dauka na soke shirin tsohon Shugaba Obama na bai wa 'yan ci rani kariya.
Kafin saukar Mr Obama ne ya kirkiro da shirin ba da kariya ga wadanda suka shiga kasar ta haramtacciyar hanya a lokacin da suke kanana.
Matakin Kotun Kolin na nufin zama Amurka daram ga sama da 'yan ci rani dubu dari biyar ne da suka zo daga kasashen Latin Amurka, kuma za a basu takardun damar neman ayyuka tamkar 'yan kasa.
A martaninsa, Mr Trump ya bayyana hukuncin a matsayin mai cike da takaici da ban tsoro.
Ya kara da cewa abunda ya rage shine hana yan Amurka hakkinsu na mallakar makami, matsawar bai koma kan mulki ba ya nada sabbin alkalai.
A yanzu gwamnatin Trump za ta nemi wata hanya ta daban don kawowa shirin cikas, to amma kuma lokaci na kure mata ganin cewa a watan Nuwamba ne za a gudanar da zabe.