Dalilin 'yan sanda na kama shugaban waɗanda suka yi zanga-zanga a Katsina

Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye dangane da irin wainar da ake toyawa a fadin duniya musamman batutuwan da suka shafi annobar korona na ma karin wasu daban.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya, Halima Umar Saleh and Buhari Muhammad Fagge

  1. Rufewa

      • Marubuci, Mustapha Musa Kaita
      • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multi-Media Broadcast Journalist

    Masu bibiyarmu a wannan shafin a daidai wannan lokaci muka kawo ƙarshen kawo muku labarai da rahotanni kai-tsaye, sai kuma gobe idan Allah ya kai mu za mu ci gaba da kawo muku wasu labaran.

    Ga wasu daga cikin labaran da muka wallafa a wannan shafin a yau:

    • Abin da ya sa aka dakatar da bude wuraren ibada a Lagos
    • Ganduje ya yi watsi da rahoton kwamitin Buhari kan mace-macen Kano
    • An kama wani mutum bayan samun gawar budurwa a rataye
    • Shugaban kasar Honduras ya kamu da cutar korona
    • COVID-19: Har yanzu Yarima Charles ba ya jin ƙamshi da ɗandano
    • Sabuwar dambarwa a APC a yayin da Giadom ya ce shi ne shugaban riko
    • Mutum 35,000 sun kamu da korona cikin kwana daya a Brazil
    • An bukaci Afrika Ta Kudu ta sake haramta sayar da giya
    • Amurka ta buƙaci gwamnatin Buhari ta kawo ƙarshen zub da jini a arewacin Najeriya
    • Covid-19: Kamfanin China ya bai wa Gombe gudunmawar kayayyakin kariya

    Za ku iya duba ƙasa domin karanta waɗannan labaran da wasu muhimmai...

  2. Dalilin 'yan sanda na kama shugaban waɗanda suka yi zanga-zanga a Katsina

    Adamu

    Asalin hoton, NPF

    Gamayyar Kungiyoyin Arewacin Najeriya,Coalition of Northern Groups (CNG), ta ce rundunar 'yan sandan ƙasar ta kama Nastura Ashir Sharif, shugaban kwamitin amintattunta saboda zargin ya zagi Femi Adesina, mai magana da yawun Shugaba Muhammadu Buhari.

    Mai magana da yawun gamayyar kungiyoyin, Abdul-Azeez Suleiman, ya shaida wa BBC ranar Laraba cewa an kama Ashir Sharif bayan sun kammala zanga-zanga a birnin Katsina inda suka yi kira a ɗauki mataki game da kashe-kashen da ke faruwa a yankin.

    Ya ce an tafi da shi hedikwatar rundunar da ke Abuja, babban birnin kasar inda yake tsare yanzu haka.

    Sanarwar da suka fitar tun da fari ta ce "kungiyar CNG ta yi matuƙar kaɗuwa ganin cewa gwamnatin da ke iƙirarin kare mulkin dimokradiyya za ta iya hantarar mutanen da suka fito don kare nauyin da ƙundin tsarin mulki ya dora musu".

    Masu zanga-zangar, mai taken#ArewaIsBleeding a turance, wato 'Jini yana kwarara a Arewa', sun bayyana matuƙar ɓacin ransu kan halin ko-in-kula da suke zargi gwamnatocin kasar na yi kan yawaitar kashe-kashe a yankin.

    Sun ce za su gudanar da irin wannan zanga-zanga a jihohi 19 da ke arewacin ƙasar don matsa lamba ga gwamnati ta ɗauki matakin da ya dace kan masu kashe-kashen.

  3. Gwamnatin Birtaniya na shan suka kan fentin jirgi

    Gwamnatin Birtaniya na shan suka bayan da ta yanke shawarar kashe dala miliyan ɗaya wurin yi wa jirgin da Firaiminista da kuma 'yan gidan sarauta ke shiga fenti.

    Fadar Downing street ta ce za a yi fentin tutar Birtaniya a jiki wanda duk inda firaiminista ya shiga a duniya za a ga tambarin ƙasar.

    To amma 'yan jam'iyyar adawa ba su gamsu da dalilan gwamnati ba.

    Davey wanda jigo ne a jam'iyyar Liberal Democrats ya ce dala miliyan ɗaya da ake shirin kashewa wurin fentin za ta sayi maganin steroid 180,000 da aka gano zai iya taimaka wa waɗanda cutar korona ta yi wa mugun kamu.

  4. Masari ya yi tattaunawar sirri da wasu shugabannin tsaron Najeriya

    ..

    Asalin hoton, Katsina State Government

    Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ya yi tattaunawar sirri da wasu daga cikin shugabannin tsaron Najeriya.

    Tattaunawar ta biyo bayan zanga-zangar da aka gudanar a jihar a ranar Talata sakamakon kashe-kashen da ake yi a arewacin Najeriya.

    Cikin waɗanda suka je birnin na Katsina domin tattaunawar akwai mai bai wa shugaban ƙasar shawara kan harkokin tsaro Babagana Monguno da Babban Sifeto na 'Yan sandan Najeriya Muhammad Adamu.

    Akwai kuma Shugaban Hukumar Tattara Bayanan Sirri ta ƙasar Ahmed Rufai Abubakar da kuma Shugaban Hukumar Tsaro ta Farin Kaya Yusuf Magaji Bichi da kuma Shugaban Sashen Tattara Bayanan Sirri a Hedikwatar Tsaro AVM MS Usman.

    Ko da BBC ta tuntuɓi gwamnan jihar ta Katsina kan abubuwan da suka tattauna da suka garƙame ƙofa, ya bayyana cewa abu ne na sirri wanda bai kamata a bayyana ba.

  5. Covid-19: Kamfanin China ya bai wa Gombe gudunmawar kayayyakin kariya

    ...

    Asalin hoton, Gombe State Government

    Kwamitin da ke yaƙi da cutar korona a jihar Gombe ya samu tallafin kayayyaki daga wani kamfanin gine-gine na 'yan China.

    Kamfanin mai suna Ganan Construction ya ce ya bai wa jihar ta Gombe tallafin ne a matsayin gudunmawarsa domin a kawo ƙarshen cutar korona a jihar.

    Daga cikin kayayyakin da aka bai wa kwamitin yaƙi da cutar akwai takunkumi 30,000 da kuma mai na wanke hannu (sanitizer) 4,800, da kuma inji na feshi da ake goyawa guda 40.

    ..

    Asalin hoton, Gombe State Government

  6. Shugaban 'yan adawar Mali da aka sace yana nan a raye

    Shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keita ya sanar da cewa shugaban 'yan adawa Soumaïla Cissé, wanda ake zargin masu kishin addini sun sace a watan Maris yana raye, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito.

    An ruwaito shugaban na cewa gwamnati na da hujjar Mista Soumaïla Cissé na nan a raye.

    Ya ce " munsan wadanda suka dauke shi. kuma in muka dage da addu'a zai dawo."

    Soumaïla Cissé, wanda shi ne shugaban jam'iyyar URD an sace shi ne a ranar 25 ga watan Maris yayin da yake yakin neman babban zabe mai zuwa.

    Dakarun Mali dai sun yi da fama da 'yan bindiga da ke arewacin kasar tun 2012.

    Mali, tare da wasu kasashe da ke yankin, na fuskantar karuwar hare-haren masu tsattsauran ra'ayin addini.

    Kuma dakarun kasar na samun taimako daga sojin yankin da kuma na Faransa.

    Getty

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, An sace Soumaïla Cissé kwana daya gabanin kwarya-kwaryar zaben da ya gudana a watan Maris
  7. Cutar korona: Mutum 184 sun sake mutuwa a Birtaniya

    An sake samun mutum 184 da suka mutu sakamakon cutar korona a faɗin Birtaniya.

    Hakan ya kawo yawan waɗanda suka mutu sakamakon cutar zuwa 42,153.

    Hukumomi a ƙasar sun bayyana cewa akwai ƙarin mutum 1,115 da suka kamu da cutar a rana guda.

  8. An hana baƙar fata aiki a cocin Turawa a Birtaniya

    Augustine

    Asalin hoton, Augustine Tanner-Ihm

    An ƙi amincewa da wani baƙar fata mai koyon aikin coci ko kuma son zama fasto sakamakon nuna wariyar launin fata daga shugabannin wata coci.

    A wani saƙon email da aka tura masa domin mayar masa da martani dangane da takardar neman aikin da ya kai, an faɗa wa Augustine Tanner-Ihm cewa "ba lallai ya samu sakewa ba" idan aka ba shi aikin da ya nema a cocin.

    A martanin da aka mayar masa ɗin, an ce duk da ƙwarewarsa, babu amfani a ci gaba da dogon bayani dangane da batun neman aikinsa a kudancin Ingila.

    Cocin Ingilar ta ba shi haƙuri. Mista Tanner-Ihm wanda ɗan asalin Chicago ne, mai muƙamin Rabarand ne a Amurka, kuma ya nemi a ba shi aiki a wata coci a kudancin Ingila.

  9. An kama mutum 8 kan 'gagarumin cin hanci da rashawa da aka tafka' a Afrika Ta Kudu

    AFP

    Asalin hoton, AFP

    Bayanan hoto, Asnath Khuba wadda ke tafiyar da bankin da yayi asarar kudade

    An kama mutum takwas da ake zargi da wani gagarumin cin hanci da rashawa da aka tafka a Afrika Ta Kudu.

    Wakilin BBC ya ce ''an kama mutanen takwas ne a wani samame da aka kai da sanyin safiya, kuma daga cikin su akwai jami'an Bankin VBS da ya durkushe a shekarar da ta gabata, da kuma kamfanin kasa da kasa na KPMG.''

    Ana zargin jami'an bankunan da hada baki da sanannun 'yan siyasa wurin sace sama da dala miliyan 100 daga wani banki da aka kirkira don taimaka wa mutanen karkara.

    Yawancin kudaden na mutanen karkara ne da ke tariyar kudin mallakar gidajen kansu.

    Ana zargin masu shigar da kara da kin gurfanar da masu fada a ji a gaban kotu, duk da zargin cin hanci da rashawa da ake musu.

  10. Kenya ta fara bincike kan badakalar korona

    Getty

    Asalin hoton, Getty Images

    Masu bincike a Kenya sun ce suna bincike game da duk wani taimakao da kasashen ketare suka ba da na yaki da annobar korona, bayan an yi zargin a kwai cin hanci da rasha kan yadda aka yi da kudaden.

    Sun shaida wa BBC cewa sun yi amannar an sace kudade da kuma kayayyakin da aka bayar da suka kai na miliyoyin dalar Amurka.

    Binciken ya biyo bayan batan dabon da wani baban kunshin takunkumi da kuma kayan kariya da China ta bayar a matsayin taimako ga kasar.

    Kafafen yada labarai na kasar sun rawaito cewa wani kamfani mai zaman kansa da ke aiki da jami’an gwamnati da kuma wani dan kasuwar China ne suka karbe aikin raba kayayyakin.

    Asusun ba da lamani na duniya da wasu kasashen Turai da hamshakin mai kudin nan na kasar China Jack Ma duk sun bai wa Kenya tallafi.

    Amma har yanzu ma’aikatan lafiya a kasar na korafin rashin kayan kariya.

  11. Kotu ta dakatar da Isra'ila daga yin wani gina a makabartar Musulmi

    Kotu a Isra'ila ta dakatar da gina wani gidan marasa galihu da ake ginawa a wata makabartar Musulmi da ke Jaffa, da aka dade ba a yi amfani da ita ba.

    Shirin gudanar da ginin ya haddasa rikici tsakanin Musulmin yankin da kuma 'yan sanda.

    Yanzu dai kotu ta dakatar da ci gaba da ginin, yayin da za a fara sauraren kara kan rikicin a wata mai zuwa.

  12. Amurka ta buƙaci gwamnatin Buhari ta kawo ƙarshen zub da jini a arewacin Najeriya

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin Amurka ta yi tir da kisan gillar farar hula da ake yi a arewacin Najeriya.

    A sanarwar da ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta fitar, ta bayyana cewa a kwanakin baya, wasu da ake zargin 'yan kungiyar ISWAP ne sun kai hare-hare a Borno inda suka kashe sama da farar hula 120, ciki har da mata da ƙananan yara da tsofaffi.

    Ta kuma ce a ranar 9 ga watan Yuni, wasu ɓarayi da ba a san ko su wane ne ba sun kai hari a wani ƙauye a Katsina inda suka kashe gwamman mutane.

    Duka waɗannan hare-haren sun biyo bayan kashe wani fasto da matarsa mai ciki a ranar 1 ga watan Yuni da kuma kashe wani limami da kuma wani mai gari da farar hula masu dimbin yawa a ranar 5 ga watan Yuni a wani rikicin ƙabilanci a Taraba.

    Dubban farar hula ne suka rasa rayukansu a Najeriya a 'yan shekarun nan sakamakon hare-haren masu tayar da ƙayar baya, da kuma rikicin ƙabilanci ko kuma na addini.

    Gwamnatin Amurka na kira gwamnatin Najeriya da ta ƙara ƙaimi wajen kawo zaman lafiya da kuma hukunta masu hannu a tayar da zaune tsaye.

    Kungiyar kare hakkin Dan adam ta Amnesty International ta ce gwamnatin Najeriya ta gaza kare rayukan 'yan kasar a yayin da matsalar tsaro take ci gaba da yin kamari musamman a arewacin kasar.

  13. An tura kawun shugaban Syria gidan yari

    Gwamnatin Faransa ta tura kawun shugaban ƙasar Syria Bashar al-Assad zaman gidan yari na shekara 4.

    An samu Rifaat al-Assad da laifin almubazaranci da kuɗin Syria inda ya sayi gidaje da ofisoshi a Faransa na fam miliyan 90.

    Tsohon mataimakin shugaban ƙsar mai shekaru 82 ya musanta zarge-zargen da ake yi masa. Lauyoyinsa sun ce za a ɗaukaka ƙara.

    Kotun dai ta yanke hukuncin cewa za a ƙwace ƙadaroroinsa da ke a birnin Paris da Landan.

    ..
  14. Cutar korona ta kama mutum 10,000 a Kamaru

    Hukumomin kiwon lafiyar Kamaru sun bayyana cewa cutar korona ta kama mutane 10,000 jumulla.

    Sai dai duk da haka hukumomin kiwon lafiya sun bayar da tabbacin cewa suna iya shawo bazuwar da annobar ke yi idan mutane suka bi ka’idodin kare kai daga kamuwa da cutar.

    A cear hukumar lafiyar, sun rrubanya gwajin cutar domin a samu shawo kanta da wuri.

  15. Labaran Duniya Cikin Minti Daya

    Bayanan sautiMinti Daya Da BBC Na Rana 17/06/2020
  16. Labarai da dumi-dumi, Shugaban riƙo na APC ya soke zaɓen fid da gwani na gwamnan Edo

    Sabon shugaban riƙo na jam'iyyar APC Victor Giadom ya soke zaɓen fidda gwani na gwamnan jihar Edo a Najeriya.

    Gidan talabijin na Channels ya ruwaito Mr Giadom na cewa ya dauki matakin ne bisa umarnin da kotu ta bayar a baya wanda ya ba shi damar yin hakan.

    A cewarsa, ya samu goyon bayan mambobin Kwamitin Gudanarwa na Jam'iyyar.

    Ga dai umarnin kotun:

    Umarnin Kotu

    Asalin hoton, Chanells TV

    Umarnin Kotu

    Asalin hoton, Chanells TV

  17. An bukaci Afrika Ta Kudu ta sake haramta sayar da giya

    Malema

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban hamayya na Afrika Ta Kudu Julius Malema ya yi kira ga gwamnati da ta dawo da haramcin da ta sanya kan barasa a lokacin kullen cutar korona.

    Shugaban jam'iyyar Economic Freedom Fighters (EFF), yana caccakar matakin Shugaba Cyril Ramaphosa ne na bude harkokin kasuwanci a wani jawabi da ya gabatar na murnar Ranar Matasa Ta Afrika Ta Kudu.

    Afrika Ta Kudu ta shafe wata biyu cikin kullen cutar korona mafi tsauri a duniya - inda har aka dakatar da sayar da giya.

    Ana ganin matakin zai rage cin zarafi da ke faruwa a gidajen aure, da hana tashe-tahsen hankula da kuma saukaka wa asibitoci yanayin da suke ciki a lokacin kulle.

    An alakanta yawan aikata laifuka da dage haramcin sayar da giyar da aka yi a ranar 1 ga watan Yuni.

  18. Turkiyya na tura dakaru Iraƙi don murƙushe Ƙurdawa

    Turkiyya ta ce tana tura dakaru zuwa arewacin Iraƙi don wani aikin murƙushe Ƙurdawa 'yan ta-da-ƙayar-baya.

    Ma'aikatar tsaron ƙasar ta ce an ɗauki dakarun soja na musamman cikin jiragen sama zuwa yankin Haftanin.

    Turkiyya ta ce matakin wani martani ne ga ƙaruwar barazanar da ake yi wa sansanonin sojinta da ke kusa da iyakar ƙasashen.

    Jiragen yaƙin Turkiyya sun yi luguden wuta kan sansanonin ƙurdawa cikin 'yan kwanakin nan.

    An ba da rahoton cewa hare-hare ta sama sun faɗa kusa da Sinjar, matsugunin mabiya addinin Yazidi da dama waɗanda rikicin 'yan ta-da-ƙayar-baya na IS ya raba da muhallansu.

    Iraƙi dai ta zargi Turkiyya da keta mata haddin iyakokinta.

  19. Mutum 35,000 sun kamu da korona cikin kwana daya a Brazil

    coronavirus ambulance italy

    Asalin hoton, Getty Images

    Brazil ta ba da rahoton samun adadi mafi yawa na mutanen da suka kamu da cutar korona a ƙasar cikin sa'a 24.

    Kusan mutum dubu talatin da biyar ne aka gano da cutar.

    Ƙasar, ta biyu bayan Amurka a yawan masu kamuwa da kuma mutuwa, ta kama hanyar samun adadin mutum miliyan ɗaya da suka kamu da korona nan da ƙarshen makon nan.

    Cutar dai ta yi sanadin mutuwar mutane sama da dubu arba'in da biyar.

    Duk da wannan al'amari, manyan birane sun fara buɗe harkoki sakamakon matsin lamba daga Shugaba jair Bolsonaro wanda ke cewa matakan kulle na da illa ga tattalin arziƙi.

    "Wakiliyar BBC ta ce Shugaba Jair Bolsonaro tabbas zai yi farin ciki da wannan shawara ta gwamnoni da wasu jami'an jam'iyyarsa don sake buɗe birane irinsu Rio da Sao Paolo".

    Masu aiko da rahotanni sun ce gwajin da ake yi a Brazi ya yi kaɗan, don haka gaskiyar yawan masu kamuwar na iya fin haka sosai.

  20. Koriya Ta Arewa za ta tura dakaru kan iyakarta da Kudu

    Koriya

    Asalin hoton, Getty Images

    Ministan tabbatar da hadin kai na Koriya Ta Kudu ya yi murabus sakamakon tashe-tashen hankulan da ake kara samu tsakanin kasarsa da Koriya Ta Arewa.

    Kim Yeon-chul ya ce ya dauki alhakin tabarbarewar dangantaka tsakanin kasashen na Koriya biyu. Hakan na zuwa ne bayan da a ranar Talata Koriya Ta Arewa ta tarwatsa wani ofishin hadaka tsakaninta da Koriya Ta Kudu, wanda aka gina da zummar inganta dangantaka tsakanin su.

    Rundunar sojin Koriya Ta Arewa ta ce za ta tura dakarunta kan iyaka.

    A ranar Laraba ne Korita Ta Arewa ta yi karin haske kan dalilin da ya sa ta tarwatsa ofishin da ke Kaesong.

    Wata makala da kafar yada labarai ta kasar ta fitar ta zargi Koriya Ta Kudu da karya yarjejeniyoyin da aka kulla a shekarar 2018 tana kuma nuna halayyar - yayin da 'yar uwar Shugaba Kim Jong-un kuma ta zargi shugaban Koriya Ta Kudu da zama dan koren Amurka.

    Koriya ta Kudu dai ta ce a shirye take a sasanta, amma kuma ta yi Allah-wadai da matakan ''rashin hankali'' da Arewar ke dauka.

    Tashin hankali na ta karuwa a makonnin baya-bayan nan - sakamakon tura sakonnin da masu farfaganda 'yan Arewa da suka tsere Kudu ke aikawa kan iyakar Arewan.