Koriya ta Arewa ta ce babu amfanin alaƙa tsakaninta da Trump
Koriya ta Arewa ta ce ba ta ga wata fa'ida ba a ci gaba da alaƙa tsakanin shugabanta Kim Jong-un da Shugaba Donald Trump na Amurka.
Ministan harkokin wajen Koriya ta Arewa, Ri Son-gwon, ya ce manufofin Amurka sun tabbatar cewa Amurkar ta ci gaba da zama babbar barazana ga jama'ar Koriya ta Arewa.
Ya ce Koriya ta Arewan za ta shirya sojojinta domin tunkarar barazanar da dakarun Amurka.
Har yanzu ba a samu wani ci gaba ba a tattaunawa game da kawo ƙarshen shirin nukiliyar Koriya ta Arewa duk da wasu taruka da aka sha yi tsakanin Mista Kim da Mista Trump.