Duniya 'ta yi watsi da rikicin Kamaru'
Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Norwegian Refugee Council ta ce rikicin da gwamnatin Kamaru ta kwashe shekara biyu tana yi da 'yan a-waren yankin rainon Ingilishi na kasar shi duniya ta fi rashin bai wa muhimmanci.
'Yan a-waren suna fafutukar ganin sun balle daga Kamaru don samun bisa abin da suka bayyana da cewa danne su da yankin da ke magana da Faransanci yake yi.
Wasu daga cikin 'yan a-waren sun ayyana ballewa daga kasar - matakin da gwamnatin Shugaba Paul Biya ta ki amincewa da shi.
Kazalika kasar ta Kamaru tana fama da kwararowar 'yan gudun hijira daga Jamhuriyar Tsakiyar Afirka da kuma Arewacin Najeriya sakamakon rikice-rikicen da ake yi a can.
Hukumar kula da 'yan gudun hijirar ta ce ta yi amfani da hanyoyi uku ne wajen fitar da wannan matsayi: rashin kudi, rashin bayar da rahotannin abubuwan da ke faruwa a yankin daga wurin 'yan jarida, lda kuma rashin samun kulawa daga wurin 'yan siyasa da jami'an difilomasiyya.
Kasashen Afirka goma ne hukumar ta ce suna cikin jerin wadanda aka yi watsi da su, kuma Venezuela ce kasa daya kawai da ba ta Afirka ba da ke cikin jadawalin.
Rahoton hukumar ya yi tsokaci kan rikice-rikicien da ake yi a yankin Sahel wanda ya kunshi kasashen Mali, Burkina Faso da Jamhuriyar Nijar.

Asalin hoton, Getty Images


