Yawan masu kamuwa da korona na ƙaruwa a Rasha
Kusan mutum 9,000 suka kamu da cutar korona a rana guda a ƙasar Rasha, hakan ya sa jumullar waɗanda suka kamu da cutar a ƙasar ya kai 467,673.
Ƙasar ta kuma bayar da rahoton cewa mutum 134 suka sake mutuwa a rana guda inda jumullar waɗanda suka mutu a ƙasar ya kai 5,859.
Ƙasar ta rasha na fama da ƙaramin matsi na tattalin arziƙi kamar yadda wasu manyan ƙasashe ke fama.



