Ƙasa biyar da suka fi fama da cutar korona
Ƙasashe biyar ne suke da rabin masu cutar korona a duniya, inda a yanzu masu dauke da cutar suka haura miliyan bakwai, a cewar taswirar da Jami'ar Johns Hopkins take fitarwa.
Amurka ce ta fi yawan masu cutar a yanzu - inda take da fiye da mutum miliyan daya da dubu 900.
Brazil ce ta biyu inda masu cutar suka kai 700,000, sai Rasha ta uku mai mutum 467,073, Burtaniya ta hudu da mutum 287,621 sannan Indiya mai mutum 257,486.
Amma salon yin gwaji ya bambanta a wadannan kasashe - a Amurka an samu ci gaba wajen yin gwaji akai-akai a makonnin baya-bayan nan, amma kwararru a Brazil da Indiya sun ce ba a yin gwajin sosai, don haka akwai yiwuwar da masu dauke da cutar da dama da ba a sani ba.
Haka zalika ana duba yawan al'ummar kowace kasa. Amurka na da yawan mutane har miliyan 330, yayin da Indiya ke da biiyan 1.3. Sannan akwai kananan kasashen da suke da masu dauke da cutar da yawa duk da cewa yawan al'ummarsu bai kai na manyan kasashe biyar din can ba.