Rahotannin sun zo ƙarshe
Nan muka kawo ƙarshen rahotanni kai-tsaye a wannan shafi.
Umar Mikail ke cewa mu kwana lafiya, da fatan za ku yi ƙasa domin karanta abubuwan da suka faru a sassan duniya ranar Litinin.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi na kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye kuma da dumi-duminsu game da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya musamman masu alaka da kisan George Floyd da annobar korona da ma karin wasu labaran.
Nasidi Adamu Yahaya, Halima Umar Saleh and Umar Mikail
Nan muka kawo ƙarshen rahotanni kai-tsaye a wannan shafi.
Umar Mikail ke cewa mu kwana lafiya, da fatan za ku yi ƙasa domin karanta abubuwan da suka faru a sassan duniya ranar Litinin.
Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ayyana ranar Juma'a 12 ga watan Yuni a matsayin hutu na Ranar Dimokuraɗiyya ga ma'aikata.
Sanarwar da Sakatariya a ma'aikatar harkokin cikin gida ta fitar, Georgina Ehuriah a madadin Minista Ogbeni Rauf Aregbesola, ta ce ministan ya taya 'yan Najeriya murnar ɗorewar mulkin dimokuraɗiyya.
Wannan ne karo na uku da za a yi bikin Ranar Dimokuraɗiyya ranar 12 ga watan Yuni tun bayan da Shugaba Buhari ya sauya ranar daga 29 ga watan Mayu a ranar 6 ga watan Yunin 2018.
Ministan harkokin cikin gida ya shawarci 'yan Najeriya da su ci gaba da bin umarnin masana harkar lafiya domin kare kansu daga annobar korona, wadda zuwa yanzu ta yi ajalin mutum 354 sannan ta kama 12,486 a ƙasar.
Tsohon ɗan sanda a Minneapolis da ake zargi da kisan bakar fata George Floyd ya bayyana a gaban kotu karon farko, inda aka shata belinsa kan dala miliyan 1.25 - kusan naira biliyan huɗu.
Masu shigar da ƙara sun bayyana "girman tuhumar" da kuma ɓacin ran da mutane suka nuna a matsayin dalilin da ya sa aka saka belin nasa fiye da miliyan.
Derek Chauvin na fuskantar tuhumar kisan kai, yayin da ake tuhumar sauran 'yan sanda uku da laifin taimaka wa wanda ake zargin.
Mutuwar Mista Floyd a watan Mayu ta jawo zanga-zangar mutane a sassan duniya tare da kiraye-kirayen kawo gyara a aikin 'yan sanda.
Mista Chauvin wanda farar fata ne, ya maƙure wuyan Floyd da gwiwarsa na tsawon minti tara lokacin da yake kama shi a Minneapolis ranar 25 ga watan Mayu.
Dokokin kulle sun ceci rayukan mutum miliyan uku daga annobar korona a Nahiyar Turai, a cewar wani bincike.
Tawagar binciken daga Kwalejin Imperial da ke Landan ta ce "mace-macen da sun fi haka yawa sosai" ba don dokar kulle ba.
Sai dai sun yi gargaɗin cewa mutum kaɗan kawai cutar ta kama kuma har yanzu "muna farko-farkon annobar ne".
Wani binciken kuma ya bayyana cewa dokokin kullen sun "ceci rayuka masu yawan gaske a ɗan ƙaramin lokaci fiye da koyaushe".
Binciken na Kwalejin Imperial ya duba tsauraran dokokin da ƙasashen Turai 11 suka saka ne - Austria, Belgium, Denmark, Faransa, Jamus, Italiya, Norway, Spain, Sweden, Switzerland da kuma Birtaniya - har zuwa farkon watan Mayu.
Zuwa wannan lokacin, korona ta kashe kusan mutum 130,000 a waɗannnan ƙsashen.
Bankin Duniya ya sanar da cewa akwai yiwuwar annobar korona ta jefa tattalin arzikin duniya cikin mummunan yanayin da bai taɓa shiga ba tun ƙarni na 19.
A cewar wakilin BBC ''rahoton ya yi hasashen cewa arzikin da al'umma ke samu zai ragu sosai a ƙasashen duniya a karon farko tun a shekarar 1870''.
Shugaban Bankin Duniya, David Malpass ya ce duk shekarun da aka shafe ana faɗi tashin haɓaka tattalin arziki, annobar korona ta mayar da komai baya.
Bankin ya ce hakan zai jefa miliyoyin mutane cikin tsananin talauci.
Allah ya yi wa mahaifin tauraron fina-finan Kannywood, Ali Nuhu, rasuwa a Jihar Gombe da ke arewa maso gabashin Najeriya.
Nuhu Poloma ya rasu ranar Litinin bayan ya shafa fama da jinya, kamar yadda wani makusancin Ali Nuhu ya tabbatar wa BBC.
Da ma dai mahaifiyar Ali ta rasu. Mahaifinsa tsohon ma'aikacin gwamnatin tarayya ne.
Binciken da tawagar gwamnatin tarayya ta gudanar game da ƙaruwar mace-mace a Jihar Kano ya nuna cewa mutum 979 ne suka mutu a kwanan nan biyo bayan mace-mace da ba a saba gani ba a jihar.
Kazalika tawagar ta gano cewa mace-macen na da alaƙa da annobar cutar korona.
Ministan Lafiya Osagie Ehanire ne ya bayyana hakan yau Litinin a wurin taron manema labarai na kullum da kwamitin shugaban ƙasa mai yaƙi da korona ke yi a Abuja.
A cewar ministan, an samu rahotonnin mutuwar ne a ƙaramar hukuma takwas na cikin birni a watan Afrilu.
Ya bayyana cewa an riƙa samun mutuwar mutum 43 a kullum lokacin da cutar na kan ƙololuwarta kafin daga bisani adadin ya zama mutum 11 a kowacce rana.
Ya ƙara da cewa kusan kashi 56 cikin 100 na mace-macen sun faru ne a gida, yayin da kashi 38 suka faru a asibiti.
Shugaban Tanzania, John Magufuli ya bayyana cewa ƙasarsa ta kawo "ƙarshen cutar korona" saboda addu'ar 'yan ƙasa.
"An kawo ƙarshen korona, mun gode wa Allah," in ji Magufuli, yayin da yake magana a wata coci a babban birnin ƙasar, Dodoma.
Kazalika ya yabe su saboda rashin saka takunkumi da kuma safar hannu.
Sai dai Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta soki yadda gwamnatin ke yaƙi da cutar.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya aike wa Majalisar Dattawa sunan Mai Shari'a Monica Dongban-Mensem domin amincewa da ita a matsayin Shugabar Kotun Ɗaukaka Ƙara.
Mai magana da yawun Buhari, Garba Shehu, ya bayyana cewa shugaban ya yi haka ne bisa damar da Kundin Tsarin Mulki ya ba shi.
Yanzu haka Mai Shari'a Monica Dongban-Mensem tana matsayin shugabar riko ne a kotun.
Buhari ya naɗa ta a muƙamin a watan Maris biyo bayan ritayar da Mai Shari'a Zainab Bulkachuwa ta yi.
Ma'aikatar Agaji da Ci Gaban Al'umma ta Najeriya ƙarƙashin jagorancin Minista Sadiya Umar Farouk ta dakatar da shirin bayar da tallafin kuɗi ga marasa ƙarfi da ta tsara yi a ƙarshen makon nan saboda matsalar tsaro.
Ma'aikatar ta bayyana haka ne yau Litinin a wata sanarwa a shafukanta na zumunta. Ta ce dakatarwar ta shafi shirin raba tallafin taki da kuma kayan abinci domin rage raɗaɗin annobar korona.
"Za a shaida wa waɗanda za su ci gajiyar tallafin lokacin da za a raba nan gaba," in ji sanarwar.
Tuni ma'aikatar ta raba tallafin a Abuja da kuma wasu jihohin ƙasar.
Ƙungiyar mahaddata Ƙur'ani ta ƙasa ta yi ƙorafin cewa gwamnatin Jihar Kano na kama malaman tsangayu, abin da ta bayyana cewa "saboda ba su da gata ne".
Shugaban ƙungiyar, Gwani Lawi Gwani Ɗan Zarga ya shaida wa wakilin BBC a Kano cewa gwamnati na ɗaukar matakan rufe makarantun ba tare da ta tuntuɓe su ba.
"A lokacin da aka ce an hana [bara] sai muka ga kawai ana bi ana kamawa," in ji shi.
Ya ƙara da cewa: "[Waɗanda aka kama] suna da yawa, muna nan muna dubawa domin kai wa gwamanti kuka don a yi mana adalci."
Sai dai gwamnatin Kano ta bakin kwamishinan ilimi kuma shugaban kwamitin hana bara, Muhammad Sanusi Ƙiru, ta musanta zargin, inda ta ce ta gayyaci malamai 50 taron tattaunawa.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gana da shugaban rundunar sojan ƙasa ta Najeriya, Laftanal Janar Yusuf Tukur Buratai a Fadar Shugaban Ƙasa ta Aso Rock Villa.
Sanarwar da fadar shugaban ta wallafa a yau Litinin ta ce Janar Buratai ya gana da Buhari ne domin yi masa bayani kan irin ci gaban da rundunarsa ke samu game da yaƙi da ƙungiyar Boko Haram.
Ganawar tasu na zuwa ne kwana biyu bayan 'yan ƙungiyar ISWAP sun kashe sojojin Najeriya shida a garin Auno na Jihar Borno.
Fiye da wata biyu kenan da Janar Buratai ya koma yankin arewa maso gabas domin jagorantar yaƙi da masu iƙirarin jihadi a jihohin Borno da Yobe da Adamawa - inda suka fi ƙamari.
Sanarwar ta ƙara da cewa mayaƙan ƙungiyoyin Boko Haram da ISWAP 1,400 aka kashe a yankin sannan aka kama 'yan leƙen asirinsu 166.
Kasar Poland za ta rufe wasu wuraren hakar kwal 12 na wucin gadi ranar Talata, domin takaita yaduwar cutar korona a yankunan da ake aikin.
Ministan ma’adanai Jacek Sasin ya ce za a dakatar da aikin hakar a duk inda aka gano cutar ta bulla, amma za a ci gaba da biyan ma’aikatan kudaden su.
A ranakun Asabar da Lahadi ne Poland ta tabbatar da mutum kusan 600 sun kamu da cutar korona a mahakar ma’adanai ta Zofiokwa.
Ana ci gaba da nuna kin amincewa da sabuwar dokar da gwamnatin Birtaniya ta kafa a kasar, wadda ta ce mutanen da suka shiga kasar za su killace kansu na makonni biyu.
Shugaban kamfanin jirgin sama na Ryanair, Michael O’Leary ya ce wannan makararran mataki ne, yayin da adadin mutanen da suka mutu a kasar sakamakon korona ya fi na ko ina a nahiyar Turai.
Wata jami’a a dakarun da ke aikin tsaro kan iyaka ta ce ba a yi musu bayani kan yadda dokar za ta yi aiki ba.
‘Yan majalisar jam’iyya mai mulki sun nuna damuwa kan matakin suna cewa hakan kai ya shafar tattalin arzikin kasar.
Ƙungiyar mahaddata Alƙur'ani ta Najeriya ta zargi gwamnatin Kano da kama wasu daga cikin malaman tsangaya da suka ki amincewa da umarnin rufe makarantun Allo da aka yi a Kano.
Ƙungiyar dai ta ce almajirai su ma ‘yan kasa ne kuma suna da ikon da za su je ko ina a fadin Najeriya don neman ilimi.
''Amma sai gashi da Kano da wasu jahohi a Arewacin Najeriya na nuna wa almajiran inda aka ringa kwashe su daga makarantun,'' in ji kungiyar.
Sannan sun ce ko kadan gwamnati ba ta nemi shawararsu ba kawai sai ji suka yi cewar an rufe makarantun.
Sheikh Dr Gwani Lawi Gwani Danzarga shi ne shugaban kungiyar a inda a ya shaida wa BBC cewar duk da cewar ba sa goyan bayan shirin za su yi biyayya kan wannan kuduri na gwamnati.
Amma suna tattaunawa a junansu da sauran kungiyoyin malaman tsangayu don tunkarar gwamnatin Kano don bayyana mata matsayarsu.
A kwanakin baya ne dai gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya sanar da dakatar da Makarantun Tsangayu a Kano, a wani mataki na shigar da almajirai tsarin ilimi kyauta kuma tilas a jihar.
A yayin wata tattaunawa da BBC shugaban kwamitin mayar da almajirai jihohinsu Murtala Sule Garo ya ce dukkan makarantun tsangayun da ba su da wurin kwana da inda za a bai wa almajirai abinci tare gwamnati ta rufe su.
Sannan Gwani Lawi yace inda gwamnatin ta Kano da gaske take da ta dabbak makarantun Tsangayu na zamani da tsohuwa gwamnatin Goodluck Jonathan ta samar a arewacin Najeriya ciki har da Kano, amma sai gashi tana neman hana almajirci ma baki a mayar almajirai tasarin ilimin boko
Kungiyar hadin kan kasashen Musulmi ta OIC za ta yi wani taro na musamman na ministocin kasashen a ranar Laraba 10 ga watan Yuni, don tattaunawa kan mamayar da Isra'ilawa ke ci gaba da yi wa yankunan Falasdinawa.
Jaridar intanet ta Saudi Gazette ta ruwaito cewa Ministan Harkokin Kasashen Wajen Saudiyya Yarima Faisal Bin Farhan ne zai jagoranci tattaunawar.
Kazalika sauran ministocin harkokin kasashen wajen sauran kasashen za su halarta da kuma Sakatare Janar na OIC, Dr. Yousef A. Al-Othaimeen.
Babban shugaban masallatai biyu masu daraja na Makkah da Maidna Sheikh Abdurrahman Sudais ya yaba wa ma'aikatan da ke aikin gyara da tsaftace Masallacin Manzon SAW.
Sudais ya yi wannan yabo ne a lokacin da ya kai ziyara don ganin yadda ake kula da masallacin bayan bude shi da aka yi bayan shafe tsawon lokaci yana rufe sakamakon cutar korona.
Ga dai wasu hotona da shafin Haramain Sharifain na Facebook ya wallafa:
Wani shirin hadin gwiwa na intanet na tattara hotunan kalubalen da al'ummar Jamhuriyar Dimokradiyar Congo ke fuskanta a lokacin da take fama da annobar Covid-19 da kyanda da kuma Ebola a 2020.
Shirin na Congo in Conversation na duba yadda rayuwa ke tafiya a kasar ta bangarori daban-daban a yayin da kasar ke fusknatar matsalolin lafiya.
Fiye da rabin kasar na cikin dokar kulle, amma miliyoyin 'yan Congo sun dogara kan kananan kasuwanci don su rayu ba tare da daukar dokokin kare kansu ba.
Masu talla a kan tituna da 'yan kasuwa da masu motocin haya sun dogara kan abin da suke samu duk rana sannan ba sa iya tara kudi.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce kusan rabin ma'aikata a nahiyar Afrika na iya rasa ayyukansu.
Jamhuriyyar Dimokradiyar Congo tana da masu dauke da cutar korona 4,000, kuma mutum 85 sun mutu.
A yayin da kasashen duniya da dama ke sassauta dokar kulle, ita kuwa kasar New Zealand kawo karshen dokar za ta yi baki daya da misalin karfe 12 na tsakar daren Litinin agogon GMT.
Firaminista Jacinda Ardern ta shaida wa manema labarai cewa ''sai da ta dan taka rawa'' a lokacin da aka shaida mata cewa babu sauran mai dauke da cutar a kasar.
Tun kwana 17 da suka gabata ba a sake samun sabbin masu dauke da cutar ba.
Da tsakar daren yau New Zealand za ta hau mataki na gaba, wanda ke nufin za a dage dukkan dokokin da aka sanya a cikin kasar. Abin da kawai ba za a sauya ba shi ne matakan killace duk dan kasar da zai koma cikinta da kuma haramta wa baki zuwa.
Ardern ta yi gargadin cewa New Zealand na iya sake samun sabbin masu kamuwa.