Ɗalibai 9 'yan aji guda sun kamu da korona

Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye kuma da dumi-duminsu game da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya musamman masu alaka da annobar korona da ma karin wasu daban.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya, Umar Mikail and Mustapha Musa Kaita

  1. Ƙarin mutum 14 sun warke daga cutar korona a Kaduna

    Gwamnan Kaduna da ke Najeriya, Nasir El-Rufai, ya ce karin mutum goma sha hudu sun warke daga cutar korona a jihar.

    Ya bayyana haka ne a shafinsa na Twitter ranar Alhamis da almuru.

    Ya ce ko da yake an sallami mutanen da suka warke, amma an samu karin mutum 20 da suka kamu da cutar a ranar.

    Mutanen da suka harbu da cutar sun fito ne daga kananan hukumomin Zaria, da Sabongari, da Chikun da Kaduna South, da Igabi, da kuma Kaduna North, in ji Gwamna El-Rufai.

    Gwamnan ya kuma bukaci mazauna jIhar su ci gaba da hakurin zama a kulle, yana mai cewa taron da ya gudanar da masu rike da sarautun gargajiya na jihar ya tattauna kan yadda za a sake bude ta.

    A cewarsa, kasuwanni da wuraren ibada da makamantansu za su ci gaba da kasancewa a garƙame amma a makon gobe za a dauki karin matakai kan yadda za a bude jihar sannu a hankali.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  2. Takunkumin da aka sanya wa China kan cin zarafin Musulmi ya soma aiki

    Sabon takunkumin da Amurka ta ƙaƙaba a kan manyan kamfanonin fasahar China da wasu cibiyoyinta ya soma aiki.

    Hukumar harkokin kasuwancin Amurka ta zargin kamfononi tara na China da taka rawa a cin zarafi da azabtarwa kan Musulmi 'yan kabilar Uighur da sauran Musulmin kasar.

    Gwamnatin China ta ce bai kamata Amurka ta tsoma baki a harkokin cikin gidanta game da lamuran tsirarun kabilu a yankin Xinjaiang ba

    Amurkan ta kuma sake sanya haramci a kan wasu kamfanoni China 24 da ke samar wa dakarun kasar makamai.

    Gwamnatin Beijing ta ce yadda take tafiyar da lamuran tsirarun a yankin Xinjaiang ya shafi cikin gida ne zalla.

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, China ta ce bai kamata Amurka ta tsoma baki a harkokin cikin gidanta game da lamuran tsirarun kabilu a yankin Xinjaiang ba
  3. Buɗewa

    Nasidi AdamuYahaya ne yake yi muku barka da safiyar Juma'a.

    Muna fatan za ku kasance tare da mu tsawon wannan rana domin sanin halin da duniya take ciki.

    Za mu kawo muku labarai da rahotannin da suka shafi rayuwarku, musamman kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da makwabtansu, har ma da sassan duniya.

    Za ku iya tafka muhawara da bayyana ra'ayoyinku a shafukanmu na sada zumunta a BBC Hausa.