Mutum hamsin 'sun mutu sakamakon korona a asibiti daya'

Asalin hoton, Reuters
Ya zuwa yanzu 'yan tawayen Houthi da ke da iko da babban birnin Yemen Sanaa basu bayyana mutane da yawa da suka kamu da cutar korona ba.
Sai dai kaso daya cikin hudu na mutum 200 da kungiyar likitoci ta MSF take jinyarsu a Sanaa sun mutu.
'Yan tawayen na Houthi suna boye girman barkewar cutar korona, sai dai cibiyoyi marasa yawa da ke jinyar masu cutar sun cika makil da masu fama da cutar.
'Yan tawayen sun nemi asibitoci masu zaman kansu su taimaka musu da gadaje domin jinyar masu cutar ta korona.
Wani likita a Sanaa - wanda ya warke daga cutar - ya ce abokan aikinsa da dama sun mutu sanadin cutar.
Wasu rahotanni da ba a tabbatar da su ba sun ce cutar tana kama likitoci sosai, saboda rashin isassun kayayyakin kariya.



