Majalisa ta amince wa Buhari karɓo rancen dala biliyan 5

Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye kuma da dumi-duminsu game da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya musamman masu alaka da annobar korona da ma karin wasu daban.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya, Umar Mikail and Awwal Ahmad Janyau

  1. Fitaccen mawaƙin Najeriya Majek Fashek ya mutu

    Majek ya shahara musamman a wakokin da ya rera a shekarun 1980 zuwa 1980

    Asalin hoton, OFFICIAL_MAJEKFASHEK/INSTAGRAM

    Bayanan hoto, Majek ya shahara musamman a wakokin da ya rera a shekarun 1980 zuwa 1990

    Fitaccen mawakin nan na Najeriya Majek Fashek ya rasu.

    Manajan mawakin ne ya tabbata da rasuwarsa ranar Talata a shafin marigayin na Instagam.

    Majek ya shahara musamman a wakokin da ya rera a shekarun 1980 zuwa 1990, kamar fitattun wakokinsaSend Down the RaindaSo Long for Too Long.

    Majek, wanda sunansa na yanka shi ne Majekodunmi Fasheke, ya kuma rera wakoki tare da shahararrun mawaka irin su Jimmy Cliff, Tracy Chapman da Snoop Dogg.

    Manajansa Omenka Uzoma ya wallafa sanarwar rasuwar mawakin a shafin maragayin na Instagram ko da yake bai bayyana musabbabin rasuwarsa ba.

    Kauce wa Instagram
    Ya kamata a bar bayanan Instagram?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da Instagram suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Instagram da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a Instagram

  2. Barkanmu da safiya

    Nasidi Adamu Yahaya ne yake yi muku barka da wannan safiya ta Talata.

    Da fatan za ku kasance da mu domin sanin halin da duniya take ciki.

    Za mu kawo muku labarai da rahotannin da suka shafi rayuwarku, musamman daga kasashen Najeriya da Nijar da ma wasu sassan duniya.

    Kuna iya tafka muhawara da bayyana ra’ayoyinku a shafukanmu na sada zumunta a BBC Hausa.