Covid-19: An sallami ƙarin mutum 135 daga wurin killacewa a Borno

Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye dangane da irin wainar da ake toyawa a fadin duniya musamman batutuwan da suka shafi annobar korona na ma karin wasu daban.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya, Umar Mikail and Mustapha Musa Kaita

  1. 'Trump bai aika wa Najeriya na'urorin taimakawa mutum yin numfashi ba'

    Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Ministan watsa labaran Najeriya ya ce har yanzu kasar ba ta karbi na'urorin taimakawa masu dauke da cutar korona yin numfashi ba, wadanda shugaban Amurka Donald Trump ya yi alkawarin bai wa kasar a watan Afrilu.

    Lai Mohammed ya musanta kalaman da Mr Trump ya yi makon jiya cewa ya aike da na'urorin 1,000 ga Najeriya.

    Ya kara da cewa gwamnatin Najeriya za ta sanar da zarar na'urorin sun isa kasar.

    Shugaba Trump ya yi alkawarin aikawa da na'urorin taimakawa mutane yin numfasin ne lokacin da suka yi wayar tarho da Shugaba Muhammadu Buhari ranar 28 ga watan Afrilu. Ya ce gwamnatin Amurka tana son taimakwa Najeriya wajen yaki da cutar korona.

    Makon jiya, lokacin da ya ziyarci kamfanin motoci na Ford da ke birnin Michigan, Mr Trump ya ce kasarsa ta aike wa Najeriya na'urori 1,000.

    Ya zuwa yanzu, an tabbatar mutum 8,915 sun kamu da cutar korona a Najeriya, inda mutum 259 suka mutu.

  2. Barkanmu da Juma'a

    Nasidi AdamuYahaya ne yake yi muku barka da Juma'a.

    Muna fatan za ku kasance tare da mu tsawon wannan rana domin sanin halin da duniya take ciki.

    Za mu kawo muku labarai da rahotannin da suka shafi rayuwarku, musamman kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da makwabtansu, har ma da sassan duniya.