Covid-19: An sallami ƙarin mutum 135 daga wurin killacewa a Borno

Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye dangane da irin wainar da ake toyawa a fadin duniya musamman batutuwan da suka shafi annobar korona na ma karin wasu daban.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya, Umar Mikail and Mustapha Musa Kaita

  1. Rufewa

      • Marubuci, Mustapha Musa Kaita
      • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multi-Media Broadcast Journalist

    Masu bibiyarmu a wannan shafin a daidai wannan lokaci muka kawo ƙarshen kawo muku labarai da rahotanni kai-tsaye, sai kuma gobe idan Allah ya kaimu za mu kawo muku wasu ƙarin labaran.

    Ga wasu daga cikin labaran da muka wallafa tun daga safiyar yau a wannan shafin:

    • COVID-19: An sake rufe makarantu a Koriya ta Kudu
    • AfDB ya wanke Adesina daga zargin nuna ɓangaranci
    • A biya diyya ga yaran da aka tsare saboda rikicin Boko Haram – Amnesty
    • Wani shahararren mayaƙin Boko Haram ya miƙa wuya ga sojojin Najeriya
    • Korona ta kashe wasu mutum 232 a Rasha
    • La Liga: Za a ci gaba da gasar kwallon Spaniya a ranar 11 ga watan Yuni
    • Gwamna Masari ya amince a buɗe masallatan Juma'a a Katsina
    • Soja ya kashe mutum saboda wayarsa ta yi ƙara
    • Gwamna Tambuwal ya gana da Buhari kan hare-haren Sokoto
    • Buhari ya ƙara wa'adin Shugabar Kotun Daukaka Ƙara

    Ku duba ƙasa domin karanta labaran da wasu muhimmai...

  2. Trump da Boris Johnson sun tattauna kan batun riga-kafin korona

    .

    Shugaban Amurka Donald Trump da kuma Firai Ministan Birtaniya Boris Johnson sun tattauna ta waya dangane da yadda ƙasashen duniya ke tunkarar annobar korona.

    Fadar Firai Ministan Birtaniya ya bayyana cewa shugabannin biyu sun tattauna ne kan batun ƙokarin da ƙasashe ke yi wajen ganin cewa an fito da riga-kafin cutar korona.

    Tuni aka fara gwajin riga-kafin cutar korona a faɗin duniya, cikin ƙasashen kuwa har da Amurka da Birtaniya.

    An bayyana cewa shugabannin biyu sun kuma tattauna kan batun taron G7, wato ƙasashe bakwai mafi tattalin arziƙi a duniya wanda ake sa ran yi a birnin Washington.

  3. Covid-19: An sallami ƙarin mutum 135 daga wurin killacewa a Borno

    Gwamnatin jihar Borno ta sallami marasa lafiya 135 da suka kamu da cutar korona a jihar bayan sun warke.

    Mai taimaka wa shugaban Najeriya kan shafukan sada zumunta Bashir Ahmad ne ya wallafa hakan a shafinsa na Twitter inda ya ce an sallame su ne bayan an yi musu gwaji har sau biyu an tabbatar ba su ɗauke da cutar.

    Mutum 258 ne suka kamu da cutar a jihar Borno kamar yadda hukumar NCDC a ƙasar ta wallafa a ranar Alhamis.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  4. Buhari ya ƙara wa'adin Shugabar Kotun Daukaka Ƙara

    .

    Asalin hoton, MONICA DONGBAN-MENSEM

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ƙara wa'adin shugabar riƙo ta Kotun Daukaka Ƙara ta ƙasar Mai Sharia'a Bolna'an Monica Dongban-Mensem.

    A wata sanarwa da Fadar Shugaban Ƙasar ta fitar a ranar Juma'a, ta bayyana cewa sabon wa'adin na rikon kwaryar zai fara aiki ne daga 3 ga watan Yunin 2020.

    Shugaba Buhari ya nada Mai Shari'a Monica a mukamin na rikon kwarya ne biyo bayan ritaya da Zainab Bulkachuwa ta yi.

    Mai Shari'a Monica ta zama mace ta biyu da ta shugabanci Kotun Daukaka kara ta Najeriya.

    Monica Dongban-Mensem 'yar asalin Jihar Filato ce, kuma ita ce Shugabar Kotun Daukaka Kara reshen Jihar Inugu kafin yanzu.

    Ta yi karatun digirinta na farko da na biyu a bangaren shari'a a Jami'ar Ahmadu Bello, Zaria.

    Tarihin Rayuwar Monica Dongban-Mensem a takaice:

    • An haifi Monica Bolna'an Dongban-Mensem ranar 13 ga watan Yunin 1957
    • A garin Dorok na Karamar Hukumar Shendam aka haife ta
    • Tsohuwar Shugabar Kotun Daukaka Kara reshen Jihar Inugu
    • Marubuciyar littafin The Defendant a shekarar 1991
    • A Jami'ar Ahmadu Bello Zaria ta yi digiri na farko da na biyu
    • Ta yi difiloma a cibiyar Advanced Legal Studies, ta Jami'ar London, Russel Square
    • Tsohuwar mai shari'a ce a kotun Abuja
    • Tsohuwar rijistira a Babbar Kotun Jihar Filato a shekarar 1979
    • Tsohuwar malama a cibiyar Catholic Media Centre da ke Kaduna
    • Tsohuwar malama a Jami'ar Jos
    • Ta kafa gidauniyar Pa William Mensem Education
    • Rundunar sojin sama ta Najeriya ta ƙera na'urar taimaka wa numfashi

      .

      Asalin hoton, Air Force Institute of Technology

      Cibiyar kimiyya da fasaha ta rundunar sojin sama ta Najeriya da ke Kaduna ta ƙaddamar da na'urar taimaka wa numfashi wadda cibiyar ta ƙera.

      Cibiyar ta bayyana cewa akwai yiwuwar wannan na'urar ta zama ta kawo ci gaba ta ɓangaren yaƙi da korona a ƙasar.

      Kyaftin Osichinaka Ubadike ya shaida wa BBC cewa waɗannan na'urorin za su taimaka wa har masu larurori da suka shafi numfashi ba wai korona kaɗai ba.

    • Gwamna Tambuwal ya gana da Buhari kan hare-haren Sokoto

      Buhari da Gwamna Tambuwal

      Asalin hoton, Nigeria Presidency

      Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na Jihar Sokoto da ke arewa maso yakmmacin Najeriya ya gana da Shugaba Muhammadu Buhari game da harin 'yan bindiga da ya yi ajalin fiye da mutum 60 a Sokoto.

      Bayanan baya-bayan nan sun nuna cewa mutanen da suka mutu din sun kai kusan 80.

      Ganau sun ce maharan sun kwashe sa'o'i suna ta'adi a ƙauyukan ba tare da kowa ya tunkare su ba.

      Kazalika shaidu sun ce wata mata da 'yan bindiga uku sun mutu a cikin wani harin daban da suka kai a Ƙaramar Hukumar Gwadabawa.

      Ba a samu ƙarin bayani kan abin da suka tattauna ba amma Fadar Shugaban Ƙasa ta ce gwamnatin ta shirya wani taro na musamman da masu ruwa da tsaki don tattaunawa kan here-hare a yankin Isa da Sabon Birni a jihar ta Sokoto.

      Za ku iya karanta wasu labaran kan matsalar tsaron a Najeriya kamar waɗannan:

      • 'Yan bindiga 'sun kashe kusan mutum 60 a Sokoto'
      • 'Yan bindiga sun kashe mutum 8,000 a arewa maso yammacin Najeriya - ICG
      • Najeriya za ta dauki mataki kan 'yan ta'adda a Sokoto
      • Rashin tsaro: Shin Buhari ya yi watsi da jihar Katsina ne?
      Kauce wa X
      Ya kamata a bar bayanan X?

      Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

      Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

      Karshen labarin da aka sa a X

    • Soja ya kashe mutum saboda wayarsa ta yi ƙara

      Abiy Ahmed

      Asalin hoton, Getty Images

      Wani soja a ƙasar Habasha ya harbe wani mutum bayan wayarsa ta yi ƙara yayin wani taron ganawa, a cewar ƙungiyar kare haƙƙi ta Amnesty International.

      An harbe Ariti Shununde mai shekara 32 yayin wani samame domin kakkaɓe 'yan bindiga na Oromo Liberation Army (OLA), a cewar shaidun da Amnesty ta ambato.

      BBC ta yi ƙoƙarin jin ta bakin mahukunta game da rahoton kisan amma ba su ce komai ba.

      Sojojin sun kira wani taro na jama'ar gari a Oromia sannan suka karɓe wayoyin mahalarta taron.

      Sai ɗaya daga cikin wayoyin ta yi ƙara. Sojoji suka tambayi wayar wace ce kuma nan take Ariti ya fito, kamar yadda wanda ya shaida lamarin ya bayyana.

      Kawai sai aka harbe shi har sau biyu a baya, in ji mutumin. Amnesty ta ce wasu majiyoyin ma daban sun ruwaito labarin.

      Wannan yana ɗaya daga cikin abubuwan da Amnesty ta ruwaito daga cikin irin ayyukan da sojoji ke yi na dakile 'yan tawayen yankin Oromia a ƙarshen shekarar 2018 zuwa 2019.

      Ita ce shekarar da Shugaban Ƙasar, Abiy Ahmed ya lashe kyautar Nobel ta zaman lafiya.

    • Gwamna Masari ya amince a buɗe masallatan Juma'a a Katsina

      Aminu Bello Masari

      Asalin hoton, @GovernorMasari

      Gwamna Aminu Bello Masari na Jihar Katsina ya bayar da damar ci gaba da sallar Juma'a a jihar bayan makonni da saka dokar kulle da zummar daƙile yaɗuwar cutar korona.

      Sakataren Gwamnatin Jihar ne, Alhaji Mustapha Inuwa ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a Katsina.

      Kamfanin dillancin labarai na NAN ya rawaito Mustapha Inuwa yana cewa su ma al'ummar Kirista za su iya zuwa wuraren ibadarsu duk Lahadi da kuma tafiye-tafiye a tsakanin ƙananan hukumomin jihar.

      Sai dai ya buƙaci jama'a da su su ci gaba da bin umarnin kariya kamar saka takunkumi da bayar da tazara da wanke hannaye da sabulu da kuma amfani da mai na sanitiser.

      Ya zuwa daren Alhamis, hukumar NCDC ta ce mutum 358 ne suka harbu da cutar korona a Jihar Katsina, yayin da 14 suka rasu da kuma 51 da suka warke daga cutar.

    • 'Cutuka na daban sun fi kashe 'yan Najeriya'

      Shugaban kwamitin yaki da cutar korona a Najeriya ya ce mafi yawan masu mutuwa a kasar wasu cutuka ne ke kashe su na daban maimakon cutar korona, saboda ba sa samun kulawar da ta da ce a asibiti.

      Boss Mustapha ya bayyana hakan ne ga manema labarai, yana cewa abin bakin ciki ne kuma wanda ba za a yarda da shi ba, asibitocin gwamnati da masu zaman kansu su rika kin karbar marasa lafiya saboda tsoron cutar korona.

      An rufe wasu asibitocin a Najeriya baki daya, ana cewa saboda karancin kayan kariya da ma’aikatansu suke da shi.

      Jami’an lafiya sun ce yawan masu zuwa asibiti a kasar ya ragu sosai saboda wannan annoba.

      Boss Mustafa

      Asalin hoton, NIGERIA PRESIDENCY

    • Zakuna sun kai hari kan matar da ke gadinsu

      Wasu zakuna biyu sun kai hari kan matar da ke gadinsu a Australia inda suka ji mata munanan raunuka, a cewar hukumomi.

      Matar mai shekara 35 ta ji munanan raunuka a fuska da wuyanta a harin da zakunan suka kai mata raanar Talata a gidan adana namun dajin Shoalhaven da ke nisan kilimita 150 daga birnin Sydney.

      Sun kai mata harin ne lokacin tana goge-goge, a cewar 'yan sanda.

      Jamai'an gidan adana namun dajin sun ce za su taimaka wa 'yan sanda wajen gudanar da bincike sannan za su taimaka wa sauran ma'aikatan gidan.

      Ma'aikatan lafiya sun ce an gano matar kwance magashiyan dauke da cizon zakunan.

      Ma'aikatan lafiya sun ce an gano matar kwance magashiyan dauke da cizon zakunan.

      Asalin hoton, Getty Images

    • La Liga: Za a ci gaba da gasar kwallon Spaniya a ranar 11 ga watan Yuni

      Za a koma fafatawa a gasar La Liga ta kasar Spaniya a ranar 11 ga watan Yuni, in ji shugaban gasar Javier Tebas.

      Sannan ya bayyana cewa za a soma gasar kwallo ta kaka mai zuwa a 12 ga watan Satumba.

      "Mun kammala shiri kuma akwai mahimmanci a karkare gasar," Tebas ya shaidawa gasar jaridar Marca ta Spaniya.

      A ranar Asabar, Firayi ministan Spaniya, Pedro Sanchez ya bada dama ga masu shirya gasar kwallon kafa a kasar cewa za su iya koma wa fagen tamaula tun daga ranar 8 ga watan Yuni.

      La Liga

      Asalin hoton, Getty Images

    • Korona ta kashe wasu mutum 232 a Rasha

      Rasha ta bayar da rahoton mutum 232 da suka rasa rayukansu cikin sa'a 24 da suka gabata, adadin rana guda mafi yawa kenan wanda kuma ya sa jumillar adadin zuwa 4,374 a ƙasar.

      Hukumomi sun faɗa ranar Juma'a cewa wasu 8,572 sun harbu da cutar - yanzu jumillarsu ya zama 387,623.

      Rasha ce ƙasa ta uku a yawan waɗanda suka kamu da cutar a duniya bayan Amurka da Brazil.

    • Wani shahararren mayaƙin Boko Haram ya miƙa wuya ga sojojin Najeriya

      Makamai

      Asalin hoton, Nigerian Army

      Hedikwatar tsaro ta sojojin najeriya da ke Abuja, babban birni ƙasar, ta ce wani ƙasurgumin ɗan ƙungiyar Boko Haram mai suna Malam Adamu Yahaya, wanda aka fi sani da Saad Ƙarami ya miƙa wuya ga dakarunta.

      Rundunar ta ce Ƙarami ya miƙa wuya ne domin raɗin kansa ga dakarun Runduna ta 242 da ke Monguno a Jihar Borno ranar 24 ga watan Mayu - Ranar Sallah.

      Ta ƙara da cewa shi ne ya jagoranci hari a kan sojojinta a Baga sannan da shi aka kai hare-hare a garuruwan Metele da Mairari da Bindiram da Kangarwa da Shetimari.

      "Wannan ya biyo bayan hare-hare ba ƙaƙƙautawa kan sansanonin da suke," a cewar rundunar.

      Kauce wa X
      Ya kamata a bar bayanan X?

      Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

      Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

      Karshen labarin da aka sa a X

    • A biya diyya ga yaran da aka tsare saboda rikicin Boko Haram – Amnesty

      Mata da ƙananan yara a Borno

      Asalin hoton, Nigerian Army

      Bayanan hoto, Sojojin Najeriya sun bayyana ranar Juma'a cewa sun kuɓutar da mata da ƙananan yara 241 daga ƙungiyar Boko Haram

      Ƙungiyar kare haƙƙi ta Amnesty International ta ce "lokaci ya yi na biyan diyya" ga yara fiye da 3,600 da aka tsare bayan zarginsu da laifin shiga ayyukan ƙungiyar Boko Haram.

      Wannan kira na Amnesty yana ƙunshe ne a wani kundin bayani da ta wallafa a watan Mayun 2020 na binciken da ta shekara 10 tana gudanarwa a arewa maso gabashin Najeriya, inda ta ce sojojin Najeriya da Boko Haram duka sun aikata laifukan cin zarafi ga yara.

      Amnesty ta zargi gwamnatin Najeriya da musguna wa yara ƙanana ne ta hanyar fakewa da shirinta na gyara hali mai suna Safe Corridor. Ta ce an sha tsare su ba tare da shari'a ba kuma ba ta hanyar da ta dace ba.

      "Sojojin Najeriya sun tsare dubban yara maza da mata a lokacin wannan rikici, yawancinsu na watanni ko shekaru. Majalisar Dinkin Duniya ta rawaito cewa an tsare yara sama da 3,600, wanda ana ganin adadin ya fi haka," in ji Amnesty.

      Kazalika ƙungiyar ta zargi Boko Haram da tafka ta'asa ta hanyar ƙona makarantu da gidajen mutane, abin da ke jefa dubban yara cikin wani hali.

      Amnesty ta ce: "Tun farkon watan Mayu na shekarar 2013, yara ƙanana na daga cikin waɗanda abin ya shafa a cikin hare-haren da aka yi ta kai wa makarantu, da sace mutane da tilasta musu zama mayaƙa ko “aure” ga ‘yan mata."

      A ƙarshe, Amnesty International ta yi kira ga Kotun Duniya da ta gaggauta fara shari'a kan binciken da ta fara yi game da laifukan yaƙi a kan ɓangarorin biyu.

      Har wa yau ta ce ɗaya daga cikin maganin matsalar shi ne "ɓangarorin biyu su biya diyya a ƙarƙashin dokokin ƙasa da ƙasa".

      "Dole ne gwamnatin Nijeriya ta saki dukkan yaran da ke tsare cikin gaggawa ko kuma ta gurfanar da su a gaban kotu kuma a yi shari’ar a fili ta hanyar bin kundin tsarin mulkin Nijeriya da kuma yarjejeniyoyin da ƙasar ta sanya wa hannu," in ji Amnesty International.

    • Coronavirus: Bayanai na baya-bayan nan daga Turai

      Karin mutum 232 sun mutu a Rasha sakamakon cutar korona, kuma wannan shi ne adadi mafi girma na mutanen da suka rasu cikin kwana guda a kasar, inda yanzu a jimulla mutum 4,374 suka rasa rayukansu sanadin cutar a kasar.

      Kazalika karin mutum 8,572 sun kamu da cutar, kasa da yadda aka saba.

      A kasar Austria, za a kyale mutane su rika zuwa ninƙaya a waje sannan mutanen da basu wucve 100 ba su halarci bukukuwan aure. Bayan an samu bullar cutar a kasar inda mutum 645, yanzu an sassauta dokar kulle.

      Wata mahauta a Netherlands ta bayar da rahoton cewa ma'aikatanta 21 cikin 130 sun harbu da cutar a birnin Helmond da ke kudancin kasar.

      Spain ta yanke shawarar sassauta dokar kulle zagaye na biyu ga kashi 70 cikin 100 na 'yan kasar ranar Litinin - za a sake bude gidajen sinima da wuraren rawa da shaguna na takaitaccen lokaci.

      Croatia ta sake bude iyakokinta da Kasashen Turai 10, cikinsu har da Austria.

      Rasha ce kasa ta uku da aka fi fama da cutar korona a  duniya

      Asalin hoton, AFP

    • Minneapolis: An cinna wuta kan ofishin 'yan sanda saboda kashe baƙar-fata

      An cinna wuta kan babban ofishin 'yan sanda na birnin Minneapolis a Amurka cikin dare uku na zanga-zanga kan mutuwar wani Ba'amurke ɗan asalin Afirka a hannun 'yan sanda.

      Shugaba Trump ya ɗora alhakin abin da ke faruwa kan 'yan banga waɗanda ya ce suna nuna rashin mutunci ga makokin mamacin, George Floyd.

      Masu zanga-zanga, haka zalika, sun fantsama tituna a sauran biranen Amurka da dama.

      Masu gabatar da ƙara sun ce ba su shirya tuhumar 'yan sanda huɗu da aka ɗora wa alhakin kisan George Floyd a farkon wannan mako ba.

      Babban baturen 'yan sanda na birnin a yanzu ya fito ya nemi afuwa. Sai dai ana ƙara samun kiraye-kirayen a tuhumi 'yan sandan da aikata babban laifi.

      Mutuwar Mista Floyd ta janyo nuna gagarumin ɓacin ran jama'a da kuma sake bijiro da sukar da ake yi kan yadda 'yan sanda ke tunkarar Amurkawa baƙaƙen fata.

      A farkon mako 'yan sanda suka kashe wani bakar-fata a Minneapolis

      Asalin hoton, Getty Images

    • Kasuwar musayar saye da 'yan kwallon kafa

      Leicester ta yi tayin bayar da kwangilar lokaci mai tsawo ga dan wasan Liverpool Adam Lallana. Kwangilar dan wasan mai shekara 32 dan kasar Ingila za ta kare a Anfield a karshen watan Yuni.(Football Insider)

      Kungiyoyin Gasar Premier biyar -Chelsea, Newcastle, Manchester United, Arsenal da kuma Leicester- suna son dauko dan wasan Barcelona da Brazil Philippe Coutinho. Za a sayar da dan wasan mai shekara 27, wanda yake zaman aro a Bayern Munich, a kan £90m.(Mundo Deportivo - in Spanish)

      Babu wata kungiya da ta yi tayin daukar dan wasan Real Madrid da Wales Gareth Bale don haka dan kwallon mai shekara 30 zai ci gaba da zama a kungiyar zuwa karin shekara daya.(Marca)

      Manchester United da Newcastle suna son dauko dan wasan Uruguay Facundo Pellistri. A halin da ake ciki dan wasan dan shekara 18 yana buga tamaula a Penarol.(Mail)

      Adam Lallana

      Asalin hoton, Getty Images

      Bayanan hoto, Kwangilar Adam Lallana za ta kare a Anfield a karshen watan Yuni.
    • AfDB ya wanke Adesina daga zargin nuna ɓangaranci

      Mr Adesina

      Asalin hoton, Getty Images

      Bayanan hoto, Mista Adesina ya musanta zargin nuna ɓangaranci

      Hukumar gudanarwar bankin ci gaban Afirka, African Development Bank (AfDB), ta ce bata nemi shugaban bankin, Akinwumi Adesina, ya sauka daga mukaminsa ba.

      Hukumar ta ce tana yin nazari da gaske kan zarge-zargen da aka yi wa Mr Adesina.

      Amurka ta yi watsi da wani bincike da aka yi a kansa game da zarge-zargen nuna ɓangaranci - sai dai bankin ya wanke Mr Adesina daga zarge-zargen.

      Niale Kaba, mai magana da yawun bankin, ta ce babu wata matsalar shugabanci ko ta tsarin mulki a AfDB.

      Wasu masu kwarmata bayanai ne suka zaergi Mr Adesina da nada 'yan uwansa a kan wasu manyan mukamai da kuma bayar da kwangiloli ga 'yan uwa da abokansa. Sai dai ya musanta zarge-zargen.

      Amurka tana da kashi 6.5 na hannun jari a bankin, kuma ita ce ta biyu mafi yawan hannun jari bayan Najeriya.

      Denmark, Norway, Sweden da kuma Finland - wadanda su ma suna da hannun jari a bankin - sun aike da sakon da ke goyon bayan gudanar da bincike mai zaman kansa a kan Mr Adesina.

    • Coronavirus: Idan kuka je coci, za ku mutu - Malema

      Malema

      Asalin hoton, AFP

      Bayanan hoto, Malema ya ce tarko daka ɗanawa masu ibada

      Fitaccen dan hamayyar nan na Afirka ta Kudu Julius Malema ya gargadi mutane da kada su fada "tarko" na zuwa coci, yana mai cewa za su mutu idan suka kamu da cutar korona.

      Za a sake bude wuraren ibada daga ranar 1 ga watan Yuni bayan Shugaba Cyril Ramaphosa ya sanar da sassauta dokar kulle - ko da yake mutum 50 zuwa kasa kawai za a bari su rika shiga coci a kowanne lokaci.

      Ranar Alhamis, Mr Malema ya ce sake bude coci-coci zai jefa masu ibada cikin kasadar kamuwa da cutar korona sannan ya yi kira ga malaman coci da kada su sake bude su idan har sun damu da rayuwar jama'a.

      Ya bayar da shawara ga 'yan jam'iyyarsa ta Economic Freedom Fighters kada su halarci coci, yana mai cewa "tarko aka ɗana".

      Ya ce gidajen abinci sun fi tsarin kiwon lafiya amma suna ci gaba da kasancewa a rufe don haka bai ga dalilin sake bude coci-coci ba.

    • COVID-19: An sake rufe makarantu a Koriya ta Kudu

      Daruruwan makarantu a Koriya ta Kudu sun rufe kwanaki ƙalilan da sake buɗewa saboda ƙaruwar mutanen da suka kamu da korona.

      Ana alaƙanta mafi yawan mutanen da annobar ta sake harba da wasu maka-maka gidajen ajiyar kaya da ke yammacin Seoul babban birnin ƙasar.

      Jami'ai sun ce masu wurin ba sa aiki yadda ya kamata da matakan taƙaita yaɗuwar cutar. Kuma an gano alamun cutar har a takalman ma'aikata."

      Makarantu sama da 800 ne a yankin suka koma karatu ta intanet yayin da hukumomi ke kira ga kamfanoni su ba da damar aiki daga gida.

      An faɗa wa mutane su guji shiga manyan taruka kuma an rufe gidajen tarihi da dandulan shaƙatawa.

      Mutum 56 aka ba da rahoton sun sake kamuwa da korona a jiya, bayan samun 79 a shekaran jiya Laraba.