Buhari ya jajanta wa mutanen Sokoto

Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye dangane da irin wainar da ake toyawa a fadin duniya musamman batutuwan da suka shafi annobar korona na ma karin wasu daban.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya and Mustapha Musa Kaita

  1. Rufewa

      • Marubuci, Mustapha Musa Kaita
      • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multi-Media Broadcast Journalist

    Masu bibiyarmu a wannan shafin a daidai wannan lokacin muka kawo karshen kawo muku bayanai da rahotanni kai-tsaye, sai kuma gobe idan Allah ya kaimu za muka kawo muku wasu labaran.

    Ga wasu daga cikin labaran da muka wallafa a yau:

    • 'Masu ɗauke da cutar korona a Najeriya sun ninka sau huɗu a kan da yadda ake sanarwa'
    • Shugaban Kenya ya gargaɗi ɗansa kan karya dokar kulle
    • Ɗaruruwan mutane sun tsere daga cibiyar killace masu cutar korona a Malawi
    • Kamfanin jirgin Afirka ta Kudu 'ba zai iya biyan albashi ba'
    • An samu ƙaruwar masu ɗauke da korona a Zimbabwe
    • Faransa ta zaftare ayyuka 850,000 a watan Afrilu
    • Sama da mutum miliyan biyu sun sake rasa ayyukansu a Amurka
    • Ƙungiyoyin farar hula 16 za su sa ido kan yadda za a kashe kudin Abacha
    • Za a dawo da Gasar Premier ran 17 ga watan Yuni
    • Ana shirin bude makarantu a Kamaru

    Ku duba ƙasa domin karanta labaran da kuma wasu muhimmai...

  2. Trump ya sa hannu kan dokar shafukan sada zumunta

    .

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaban Amurka Donald Trump ya saka hannu kan doka ta musamman da za ta sauya fasalin dokokin da ke kare shafukan sada zumunta.

    Hakan na nufin za a iya yin ƙarar shafuka irin su Facebook da Twitter idan har kotu ta same su da laifin toshe sakonnin mutane ta hanyar yaudara.

    Shugaban ya bayyana cewa kafofin sada zumunta kamar Facebook da Twitter da Google na da ikon da za su iya tacewa da kuma taƙaita bayanan da ake wallafawa a shafukan.

    A ranar Laraba ne Shugaba Trump ya soki Twitter da hana shi 'yancin fadin albarkacin baki bayan a karon farko shafin ya bayyana wani sako da shugaban ya wallafa a matsayin na yaudara.

  3. Korona ta kashe fiye da mutum dubu 100 a Amurka

    Fiye da mutum 100,000 ne suka mutu sakamakon cutar korona a Amurka, ƙasar da ke kan gaba wajen yawan masu cutar.

    Shugaban ƙasar Donald Trump ya jajanta wa 'yan uwa da abokan arziƙi na waɗanda suka mutu sakamakon cutar.

    Fiye da watanni biyu kenan da ƙasar ta saka dokar kulle domin daƙile yaduwar korona.

    Sai dai a cikin makon da ya gabata ƙasar ta fara sassauta dokoki masu tsauri da ta saka.

  4. An kashe fararen hula 27 a Mali

    Rahotanni daga Mali na cewa an kashe fararen hula 27 a wasu hare-hare masu nasaba da ƙabilanci kan ƙabilar Dogon.

    Hukumomi a ƙasar sun yi amannar cewa hare-haren na Yammacin Talata da Laraba wasu mayaka ne da ke iƙirarin kare Fulani da ke yankin suka kai su.

    Hare hare a arewacin Mali sun haifar da farmakin ramuwar gayya a tsakanin makiyaya da kuma manoma a kasar.

    Sojojin kasar na shan suka daga masu rajin kare haƙƙin bil’adama saboda gazawa wurin kare fararen hula daga hare hare.

  5. Buhari ya shiga taron Majalisar Dinkin Duniya ta intanet

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari lokacin da yake wata ganawa ta bidiyo a wani taron Majalisar Dinkin Duniya kan korona a ranar Alhamis.

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    .

    Asalin hoton, Getty Images

    .

    Asalin hoton, Getty Images

  6. Buhari ya jajanta wa mutanen Sokoto

    .

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya janjanta wa iyalan waɗanda suka rasa ransu a wani hari da 'yan bindiga suka kai a ƙaramar hukumar Sabon Birni ta jihar Sokoto.

    A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar Malam Garba Shehu ya fitar, ya ce shugaban ya yi addu'ar samun sauƙi ga waɗanda suka samu raunuka.

    Shugaban ya bayyana cewa abin takaici ne a ce 'yan bindiga suna kai hare-hare a irin wannan lokaci da duniya da Najeriya ke fama da annobar korona.

    Shugaban ya yi alkawarin cewa rundunar da aka ƙaddamar domin yaƙar masu tayar da ƙayar baya a arewa maso yammacin ƙasar za ta ci gaba da yaƙar 'yan bindigar da suka addabi yankin.

  7. Za a dawo da Gasar Premier ran 17 ga watan Yuni

    BBC ta fahimci cewa za a dawo gasar firimiya ta ingila a ranar 17 ga watan Yuni mai kamawa.

    Kungiyoyin da ke cikin gasar na ci gaba da tattaunawa, kuma rahotanni sun ce sun aminta da fara kammala kwantan wasanni biyu tsakanin Aston Villa da Sheffield United, da kuma Manchester City da Arsenal.

    Sauran wasanni tara kuwa za a ci gaba da su mako daya bayan buga kwantan, kuma duka ba a tare da 'yan kallo ba.

    A ranar Laraba ne kungiyoyin suka aminta da dawowa atisaye gadan-gadan tare da hada jiki da juna.

    Tuni Gasar Bundesliga ta Jamus aka dawo taka leda. A Sfaniya ma ana shirye-shiryen dawowa gasar La Liga wata mai zuwa.

  8. China na son hana 'yancin siyasa a yankin Asiya

    Amurka da Burtaniya da Kanada da Australiya sun fitar da sanarwar cewa sabuwar dokar tsaro da China ta kakaba a Hong Kong za ta hana 'yancin ra’ayin siyasa a yankin.

    Sun ce China za ta yi anfani da dokar wurin samun damar kama mutane da sunan fursunonin siyasa wanda hakan zai kara ta’azzara rikici a yankin.

    To amma gwamnati a Beijing ta ce dokar ta zama dole, don hakan zai ba ta damar kaucewa zanga-zangar goyon bayan dimokradiyya da ta faru bara.

    Dokar za ta tsaurara hukunci ga masu aikata wasu ayyuka da a yanzu China ke wa kallon na ta'addanci, kuma hakan zai bai wa gwamnatin Beijing damar tura masu leken asiri zuwa yankin a karon farko.

  9. Ma'ikatan kamfanin Nissan na zanga-zanga a Spaniya

    EPA

    Asalin hoton, EPA

    Bayanan hoto, Masu zanga-zangar sun ta kona tayoyi lokacin da suke nuna bacin ransu

    Ma'aikatan kamfanin kera motoci na Nissan birnin Barcelona da ke Spaniya sun gudanar da zanga zanag a a harabar kamfanin.

    Wannan na zuwa ne bayan da kamfanin Nissan ya sanar da cewa zai rufe ofishin a watan Disamba.

    Hakan na nufin za a rasa ayyuka 3,000 kenan a Spaniya.

    Masu boren sun rika kona tayu sun kuma kutsa kai cikin gine ginen kamfanin.

    Magajiyar garin Barcelona Laura Campos ta ce ''muna jin bacin ran da ma'aikatan kanfanin Nissan ke ji na batun rufe tashar sa da ke yankin Catalonia.Kuma wannan mataki ne da zai yi tasiri sosai ga tattalin arzikinmu.''

    Rahotanni sun ce duk da sun saka takunkumin, amma basu ba da tazara ba yayin zanga-zangar.

    Dama ma'aikatan Nissan na yajin aikin sama da wata daya, bayan zaftare musu kashi 20 cikin 100 na albashinsu da aka yi.

    To amma gwamnati ta ware sama da dala miliyan 500 don farfado da kamfanonin ababen hawa da ke neman durkushewa a kasar.

    Getty

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, A kusa da ginin kamfanin suka rika kona tayoyin
  10. 'Yan majalisar China sun amince da dokar tsaro mai cike da cece-kuce

    AFP

    Asalin hoton, AFP

    'Yan majalisa a China sun rattaba hannu kan dokar tsaro mai cike da ce-ce-ku ce da ake ganin za ta ragewa Hong Kong 'yancin gashin kai.

    Daga cikin sama da yan majalisa 3,000 daya ne kawai bai aminta ba.

    Wakilin BBC ya ce shugabar gwamnatin Hong Kong Carrie Lam ta kafe cewa za a tabbatar da cewa ba a keta hakkin al'umma ba, ko kuma hana su 'yancinsu saboda fito da wannan doka, to amma da yawa na ganin an yi haka ne da nufin ragewa Hong Kong karfin iko da take da shi, da kuma sa kafar wando guda da masu rajin kare dimokradiyya''.

    Dokar za ta tsaurara hukunci ga masu aikata wasu ayyuka da a yanzu China ke wa kallon na ta'addanci, kuma hakan zai bai wa gwamnatin Beijing damar tura masu leken asiri zuwa yankin a karon farko.

    Haka ma hukumomin Chinar ba su bayyana duk abin da dokar ta kunsa ba a zahiri.

  11. Kamfanin Rupert Murdoch zai daina buga jaridu a kamfani 112 zai koma intanet

    Getty

    Asalin hoton, Getty Images

    Kamfanin jarida na News Corp Australia ya sanar da cewa zai daina buga jaridu a kanfanoninsa sama da 100 da ke yankin Australia.

    Kamfanin wanda mallakar Rupert Murdoch ne ya ta'allaka rugujewar kasuwancin jaridar a yankin saboda rashin samun tallace-tallace da annobar Korona ta haifar.

    Daga wata mai zuwa, za a rufe kamfani 35 kwata-kwata, yayin da 76 za su koma wallafa labarai a internet kawai.

    Jaridun da ake wallafawa na fuskantar babban kalubale a 'yan shekarun nan, la'akari da yadda masu bayar da tallace-tallace suka karkata kudinsu ga jaridun intanet.

  12. 'Korona ta kashe mutane da yawa kan a farga'

    Getty

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar Lafiyar ta Duniya ta ce kusan mutun 160,000 ne suka mutu a tarayyar Turai tun a watan Maris kafin ma a ankara.

    Wani jami'in hukumar ya fada wa manema labarai cewa kusan duka mace macen na da alaka da cutar Korona.

    A wata mai kama da haka sama da mutun 108,000 ne suka rasa aikin yi a Faransa daga watan Afrilu kawo yanzu saboda annobar,

    Hukumar samar da ayyuka ta kasar ta ce a yanzu mutun miliyan 4.5 ne kenan suka rasa ayyukansu a Faransa a jumlace, kuma mafi yawansu maza ne.

  13. Ƙungiyoyin farar hula 16 za su sa ido kan yadda za a kashe kudin Abacha

    Abacha

    Asalin hoton, Getty Images

    A yau ne gwamnatin Najeriya ta rufe karbar takardun ta yi daga kungiyoyin farar-hula, wadanda ke sha`awar aiki da gwamnati wajen sa-ido a kan yadda za ta kashe wani kudi, fiye da dala miliyan 300 da ake zargin an sace a zamanin gwamnatin Sani Abacha.

    A watan Afirilun da ya wuce ne gwamnatin Najeriya ta samu damar karbo kudin daga Amurka, bayan sun kulla wata yarjejeniya, ciki har da sanya kungiyoyin farar-hula da za su bi diddigin yadda za a kashe kudin.

    Kungiyoyin farar-hula 16 ne suka nuna sha'awar aiki kafada-da-kafada da gwamnatin Najeriyar wajen sa-ido a kan yadda za ta kashe kudin daga ta karbo daga Amurka, dala miliyon 311.

    HAkan na zuwa ne bayan da suka cimma yarjejeniya da gwamnatin Amurkan da ta Island of Jersey, cewa za a yi amfani da kudin ne wajen ci gaba da gina wasu hanyoyin mota tagwaye, da suka tashi daga Legas suka dangane da Ibadan, da wadanda suka tashi daga Abuja suka dangana da Kano da kuma gadar motar nan da aka fi sani da second Niger Bridge da ke kudancin Najeriya... sannan wajibi ne a sanya kungiyoyin a cikin masu sa ido.

  14. An bukaci a ƙara ƙokari a yaƙin da ake yi da korona a Afrika

    Getty

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban cibiyar yaki da cutuka masu yaduwa ta Afrika ya yi kira da a ƙara ƙoƙari a yakin da ake yi da korona a nahiyar, bayan alamu na nuna cutar na ƙara yaduwa cikin ƙasashen da ke nahiyar a hankali.

    John Nkengasong ya ce lokaci ya yi da ya kamata a rika yi wa mutanen da suka nuna alamar cutar gwaji da kuma kara mai da hankali wajen ba da tazara tsakanin mutane, da wanke hannu da kuma sanya takunkumi.

    Ya zuwa yanzu cutar bata yaduwa a nahiyar Afrika kamar yadda take Asiya ko kuma Turai.

    Masana na ganin hakan na da nasaba da adadin matasan da ke akwai a nahiyar.

    Duk da haka abu ne mai wuya a yi hasashe kan nahiyar, wadda a yanzu take da masu cutar 120,000, daga cikin sama da mutane biliyan daya da take da su.

  15. Labarai da dumi-dumi, Sama da mutum miliyan biyu sun sake rasa ayyukansu a Amurka

    Getty

    Asalin hoton, Getty Images

    Ma'aikatar tsaro ta Amurka ta sanar da cewa karin mutum miliyan 2.1 a kasar sun sake mika bukatar samun taimakon da ake bai wa marasa aikin yi a makon da ya gabata.

    Tun a tsakiyar watan Maris, sama da mutum miliyan 40 ne suka rasa ayyukansu a kasar - wanda shi ne kashi hudu na duka maaikatan kasar ta Amurka.

    A watan da ya wuce, adadin marasa aikin yi yakai kashi 15 cikin 100, wanda shi ne adadi mafi girma da aka samu tun lokacin Great Depression.

    Wannan adadin na zuwa ne daidai lokacin da duka jihohin kasar 50 suka fara sassauta dokar kullen da aka sanya.

    A gefe guda kuma, adadin wadanda suka mutu a kasar ya aki mutum 100,000 wanda shi ne adadi mafi girma da aka samu a duniya.

  16. Halin da ake ciki a Latin Amurka: wuraren shaƙatawa da filayen ƙwallo

    Getty

    Asalin hoton, Getty Images

    Halin da ake ciki a Latin Amurka, inda ake ci gaba da sassauta dokar kullen da aka ƙaƙaba, duk kuwa da bayanin da Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta fitar cewa yankin zai iya zama cibiyar annobar nan gaba:

    • Za a sake bude wuraren shaƙatawa a biranen ƙasar Mexico amma kashi daya cikin uku na mutane za a bari su fito, a cewar hukumomi. Matakan dai na kokarin saukaka halin zaman gidan da ake fama da shi a babban birnin kasar mai yawan jama'a. Jami'ai na kokarin kirkiro hanyoyin keke domin karfafa gwiwar mutane su rika hawa kekuna maimakon motocin haya.
    • Wasu filayen kwallo a Brazil sun koma atisaye ana sanya 'yan kwallon guje-guje domin dawo da hazaƙarsu biyo bayan kullen da aka yi fama da shi saboda korona. Kungiyar Flamengo da ke Rio de Janeiro na cikin club din da suka fara atisyen.
    • Sai dai wanu masu ruwa da tsaki sun yi gargadin cewa bai kamata Brazil ta dawo atisaye ba a yanzu kamar yadda Jamus ta yi, inda aka dawo wasanni a Bundisliga amma ba tare da 'yan kallo ba. Brazil ce ƙasa ta biyu da cutar ta fi ƙamari a cikinta a duniya. Ya zuwa ranar Laraba, adadin wadanda suka mutu a kasar ya kai 25,000.
  17. Adadin wadanda suka mutu a Sakkwato ya karu zuwa 74

    Rahotanni daga jihar Sokoto a Najeriya na cewa adadin mutane da suka rasa rayukansu a wani jerin hare-hare da 'yan bindiga suka kai a karamar hukumar Sabon Birni ya karu zuwa 74.

    Jiya ne dai 'yan bindigar suka afka wa kauyuka a kalla biyar a yankin inda alkaluma na farko suka nuna cewa mutane 60 ne suka mutu.

    To amma bayanai daga jama'ar yankin na nuna cewa yau da safe an samu karin gawawaki, yayin da aka kai wadanda suka jikkata asibiti.

  18. Ana shirin bude makarantu a Kamaru

    A lokacin da ake shirin bude makarantu, a duk fadin Kamaru daga mako mai zuwa, shugabannin makarantun mabiya darikar katolika sun yanke shawarar dage komawa ajujuwan makarantunsu zuwa wani lokacin da ba su ambata ba.

    Sun ce sun yi hakan ne a dalilin fargabar da suke da ita game da annobar cutar corona da take yaduwa da gaggawa a cikin kasar.

    Ita kuma gwamnati ta ce daliban Firamare da Sakandare da za su rubuta jarrabawa a karshen shekarar karatu, za su koma ajujuwa ne a ranar 1 ga watan Yuni.

    Sai dai ita Gwamnati tuni ta fitar da jadawalin kowace jarrabawa.

  19. An tisa ƙeyar wasu mata masu zaman kansu gida a Mozambique

    Getty

    Asalin hoton, Getty Images

    'Yan sanda a Mozambique sun tisa kyeyar wasu mata 43 masu zaman kansu gida, wadanda aka kama saboda karya dokar kulle da aka sanya a wani mataki na yaki da cutar korona.

    Matan sun hadar da wadanda suka fito daga Zimbabwe da Zambia, wadanda aka kama yayin wani samame a makon jiya, in ji hukumomin kasar ta Mozambique.

    Kimanin mutane 109 ne aka kama sakamakon karya dokar kulle da aka sa a birnin Beira.

    Wadanda aka kaman sun hada da mata masu zaman kansu da 'yan kasuwa da wasu mutane da aka kama a kan titi bayan sun sha barasa.

    Ciki akwai 77 da aka kaman wadanda mata ne masu zaman kansu amma 'yan kasar, 43 kuma 'yan kasashen kyetare ne kuma an tisa keyarsu gida. In ji daraktan yan sanda na gundumar Fernando Riberito.

    Ya kara da cewa akwai knanan yaran da aka kama cikin masu sayer da barasa.

    Mozambique ta tabbatar da mutum 227 da ke dauke da korona a kasar, 12 daga cikinsu kuma a lardin Sofala suke.

    Shugaban kasar Filipe Nyusi ya sanar da tsawaita dokar kullen da aka kakaba a ranar 1 ga watan Afrilu har na tsawon wata guda saboda karuwar masu cutar da ake samu, in ji shugaban.

    Yayin dokar an haramta zirga-zirga, an rufe makarantu kuma an hana 'yan kasashen waje shiga kasar.

  20. Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi kan aikata laifukan yaƙi a Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo

    BBC

    Majalisar Dinkin Duniya ta ce yawan kashe-kashen da fyade da mayaƙa ke yi a arewa maso gabashin Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo zai iya zama tamkar laifukan take hakkin bil-adama da laifukan yaƙi.

    Wannan gargadin na zuwa ne bayan karuwar rikicin kabilanci da ake samu a 'yan watannin bayan nan a lardin Ituri.

    Majalisar Dinkin Dukiya ta ce kimanin mutum 300 aka kashe, aka yi wa wasu 40 fyade tsakanin watan Nuwamba da Afrilu - wanda kuma mayakan da ke da alaka da kungiyar 'yan tawayen Codeco wadanda aka kora daga al'ummar Lendu ne ke aikatawa.

    Tun da farko MDD ta ce kimanin mutum 38 ne aka kashe a Ituri da kuma garin Kivu da ke makwabtaka daga arewaci.