Sojoji sun kashe ‘yan bindiga 200 a Katsina da Zamfara

Asalin hoton, Others
Dakarun rundunar Hadarin Daji karkashin sojojin sama na Najeriya sun hallaka kusan 'yan bindiga 200 a jihohin Katsina da Zamfara.
Sojojin sun hallaka su ne a wani hari da suka kai ta sama a sansanonin ɓarayin da ke Mai'Bai a ƙaramar hukumar Jibiya a jihar Katsina da kuma sansanin Kurmin Kura a ƙaramar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara a ranakun Juma'a da Asabar.
A wata sanarwa da Shelkwatar Tsaro ta Najeriya ta wallafa a shafinta na Twiitter, ta bayyana cewa an ƙaddamar da harin ne bayan an ɗauki lokaci ana tattara bayanan sirri inda aka gano ɓarayin na amfani da wuraren biyu a matsayin maɓuyarsu.



